Acts 26 (BOHCB)

1 Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “An ba ka izini ka yi magana.”Saboda haka Bulus ya yi alama da hannunsa ya fara kāriyarsa. 2 Ya ce, “Sarki Agiriffa, na yi sa’a da na tsaya a gabanka yau yayinda nake kāriyata game da dukan zargin Yahudawa, 3 musamman ma domin ka saba sosai da dukan al’adun Yahudawa da kuma maganganunsu. Saboda haka ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri. 4 “Yahudawa duk sun san yadda na yi rayuwa tun ina yaro, daga farkon rayuwata a ƙasarmu da kuma a Urushalima. 5 Sun san ni tun da daɗewa za su kuwa shaida, in suna so, cewa bisa ga ɗarikar addininmu mafi tsanani, na yi rayuwar Bafarisiye ne. 6 Yanzu kuwa saboda begena cikin abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari ne, ake mini shari’a yau. 7 Wannan shi ne alkawarin da kabilanmu goma sha biyu suke bege su ga cikawarsa, yayinda suke bauta wa Allah da himma dare da rana. Ya Sarki, saboda wannan bege ne fa Yahudawa suke zargena. 8 Don me wani a cikinku zai yi shakka cewa Allah yana tā da matattu? 9 “Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare. 10 Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, sa’ad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuri’ata gāba da su. 11 Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu. 12 “A cikin irin tafiye-tafiyen nan ne ina kan hanya zuwa Damaskus tare da izini daga manyan firistoci. 13 Da tsakar rana, ya sarki, sa’ad da nake kan hanya, sai na ga wani haske daga sama, fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata. 14 Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’ 15 “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’“Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. 16 Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka. 17 Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin 18 ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’ 19 “Saboda haka fa, Sarki Agiriffa, ban yi rashin biyayya ga wahayin nan daga sama ba. 20 Da farko ga waɗanda suke a Damaskus, sa’an nan ga waɗanda suke a Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya, da kuma ga Al’ummai su ma, na yi wa’azi don su tuba su juyo ga Allah su kuma tabbatar da tubansu ta wurin ayyukansu. 21 Shi ya sa Yahudawa suka kama ni a filin haikali suka kuma yi ƙoƙarin kashe ni. 22 Amma na sami taimakon Allah har yă zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru, 23 cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Al’ummai.” 24 A nan ne fa Festus ya tsai da kāriyar Bulus. Ya yi ihu ya ce, “Bulus! Kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.” 25 Bulus ya amsa ya ce, “Ba na hauka, ya mafifici Festus. Abin da nake faɗi gaskiya ne da kuma mai kyau. 26 Sarki ya san waɗannan abubuwa, ina kuma iya yin magana da shi a sake. Na tabbata cewa ba ɗaya daga cikin waɗannan da ya kuɓuce saninsa, domin ba a ɓoye aka yi shi ba. 27 Sarki Agiriffa ka gaskata da annabawa? Na san ka gaskata.” 28 Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Kana tsammani cewa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kana so ka mai da ni Kirista?” 29 Bulus ya amsa ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa, ina addu’a ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.” 30 Sai sarki ya tashi, haka kuma gwamna da Bernis da kuma waɗanda suke zaune tare da su. 31 Suka bar ɗakin, kuma yayinda suke magana da juna, sai suka ce, “Wannan mutum ba ya yin kome da ya isa kisa ko dauri.” 32 Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Da ba don wannan mutum ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba da an sake shi.”

In Other Versions

Acts 26 in the ANGEFD

Acts 26 in the ANTPNG2D

Acts 26 in the AS21

Acts 26 in the BAGH

Acts 26 in the BBPNG

Acts 26 in the BBT1E

Acts 26 in the BDS

Acts 26 in the BEV

Acts 26 in the BHAD

Acts 26 in the BIB

Acts 26 in the BLPT

Acts 26 in the BNT

Acts 26 in the BNTABOOT

Acts 26 in the BNTLV

Acts 26 in the BOATCB

Acts 26 in the BOATCB2

Acts 26 in the BOBCV

Acts 26 in the BOCNT

Acts 26 in the BOECS

Acts 26 in the BOGWICC

Acts 26 in the BOHCV

Acts 26 in the BOHLNT

Acts 26 in the BOHNTLTAL

Acts 26 in the BOICB

Acts 26 in the BOILNTAP

Acts 26 in the BOITCV

Acts 26 in the BOKCV

Acts 26 in the BOKCV2

Acts 26 in the BOKHWOG

Acts 26 in the BOKSSV

Acts 26 in the BOLCB

Acts 26 in the BOLCB2

Acts 26 in the BOMCV

Acts 26 in the BONAV

Acts 26 in the BONCB

Acts 26 in the BONLT

Acts 26 in the BONUT2

Acts 26 in the BOPLNT

Acts 26 in the BOSCB

Acts 26 in the BOSNC

Acts 26 in the BOTLNT

Acts 26 in the BOVCB

Acts 26 in the BOYCB

Acts 26 in the BPBB

Acts 26 in the BPH

Acts 26 in the BSB

Acts 26 in the CCB

Acts 26 in the CUV

Acts 26 in the CUVS

Acts 26 in the DBT

Acts 26 in the DGDNT

Acts 26 in the DHNT

Acts 26 in the DNT

Acts 26 in the ELBE

Acts 26 in the EMTV

Acts 26 in the ESV

Acts 26 in the FBV

Acts 26 in the FEB

Acts 26 in the GGMNT

Acts 26 in the GNT

Acts 26 in the HARY

Acts 26 in the HNT

Acts 26 in the IRVA

Acts 26 in the IRVB

Acts 26 in the IRVG

Acts 26 in the IRVH

Acts 26 in the IRVK

Acts 26 in the IRVM

Acts 26 in the IRVM2

Acts 26 in the IRVO

Acts 26 in the IRVP

Acts 26 in the IRVT

Acts 26 in the IRVT2

Acts 26 in the IRVU

Acts 26 in the ISVN

Acts 26 in the JSNT

Acts 26 in the KAPI

Acts 26 in the KBT1ETNIK

Acts 26 in the KBV

Acts 26 in the KJV

Acts 26 in the KNFD

Acts 26 in the LBA

Acts 26 in the LBLA

Acts 26 in the LNT

Acts 26 in the LSV

Acts 26 in the MAAL

Acts 26 in the MBV

Acts 26 in the MBV2

Acts 26 in the MHNT

Acts 26 in the MKNFD

Acts 26 in the MNG

Acts 26 in the MNT

Acts 26 in the MNT2

Acts 26 in the MRS1T

Acts 26 in the NAA

Acts 26 in the NASB

Acts 26 in the NBLA

Acts 26 in the NBS

Acts 26 in the NBVTP

Acts 26 in the NET2

Acts 26 in the NIV11

Acts 26 in the NNT

Acts 26 in the NNT2

Acts 26 in the NNT3

Acts 26 in the PDDPT

Acts 26 in the PFNT

Acts 26 in the RMNT

Acts 26 in the SBIAS

Acts 26 in the SBIBS

Acts 26 in the SBIBS2

Acts 26 in the SBICS

Acts 26 in the SBIDS

Acts 26 in the SBIGS

Acts 26 in the SBIHS

Acts 26 in the SBIIS

Acts 26 in the SBIIS2

Acts 26 in the SBIIS3

Acts 26 in the SBIKS

Acts 26 in the SBIKS2

Acts 26 in the SBIMS

Acts 26 in the SBIOS

Acts 26 in the SBIPS

Acts 26 in the SBISS

Acts 26 in the SBITS

Acts 26 in the SBITS2

Acts 26 in the SBITS3

Acts 26 in the SBITS4

Acts 26 in the SBIUS

Acts 26 in the SBIVS

Acts 26 in the SBT

Acts 26 in the SBT1E

Acts 26 in the SCHL

Acts 26 in the SNT

Acts 26 in the SUSU

Acts 26 in the SUSU2

Acts 26 in the SYNO

Acts 26 in the TBIAOTANT

Acts 26 in the TBT1E

Acts 26 in the TBT1E2

Acts 26 in the TFTIP

Acts 26 in the TFTU

Acts 26 in the TGNTATF3T

Acts 26 in the THAI

Acts 26 in the TNFD

Acts 26 in the TNT

Acts 26 in the TNTIK

Acts 26 in the TNTIL

Acts 26 in the TNTIN

Acts 26 in the TNTIP

Acts 26 in the TNTIZ

Acts 26 in the TOMA

Acts 26 in the TTENT

Acts 26 in the UBG

Acts 26 in the UGV

Acts 26 in the UGV2

Acts 26 in the UGV3

Acts 26 in the VBL

Acts 26 in the VDCC

Acts 26 in the YALU

Acts 26 in the YAPE

Acts 26 in the YBVTP

Acts 26 in the ZBP