1 Timothy 1 (BOHCB)

1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu, 2 Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai. 3 Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba 4 ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya. 5 Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya. 6 Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana. 7 So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai. 8 Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata. 9 Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, 10 da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa, 11 da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini. 12 Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa. 13 Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya. 14 An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu. 15 Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu. 16 Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. 17 Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin. 18 Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau, 19 kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu. 20 Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.

In Other Versions

1 Timothy 1 in the ANGEFD

1 Timothy 1 in the ANTPNG2D

1 Timothy 1 in the AS21

1 Timothy 1 in the BAGH

1 Timothy 1 in the BBPNG

1 Timothy 1 in the BBT1E

1 Timothy 1 in the BDS

1 Timothy 1 in the BEV

1 Timothy 1 in the BHAD

1 Timothy 1 in the BIB

1 Timothy 1 in the BLPT

1 Timothy 1 in the BNT

1 Timothy 1 in the BNTABOOT

1 Timothy 1 in the BNTLV

1 Timothy 1 in the BOATCB

1 Timothy 1 in the BOATCB2

1 Timothy 1 in the BOBCV

1 Timothy 1 in the BOCNT

1 Timothy 1 in the BOECS

1 Timothy 1 in the BOGWICC

1 Timothy 1 in the BOHCV

1 Timothy 1 in the BOHLNT

1 Timothy 1 in the BOHNTLTAL

1 Timothy 1 in the BOICB

1 Timothy 1 in the BOILNTAP

1 Timothy 1 in the BOITCV

1 Timothy 1 in the BOKCV

1 Timothy 1 in the BOKCV2

1 Timothy 1 in the BOKHWOG

1 Timothy 1 in the BOKSSV

1 Timothy 1 in the BOLCB

1 Timothy 1 in the BOLCB2

1 Timothy 1 in the BOMCV

1 Timothy 1 in the BONAV

1 Timothy 1 in the BONCB

1 Timothy 1 in the BONLT

1 Timothy 1 in the BONUT2

1 Timothy 1 in the BOPLNT

1 Timothy 1 in the BOSCB

1 Timothy 1 in the BOSNC

1 Timothy 1 in the BOTLNT

1 Timothy 1 in the BOVCB

1 Timothy 1 in the BOYCB

1 Timothy 1 in the BPBB

1 Timothy 1 in the BPH

1 Timothy 1 in the BSB

1 Timothy 1 in the CCB

1 Timothy 1 in the CUV

1 Timothy 1 in the CUVS

1 Timothy 1 in the DBT

1 Timothy 1 in the DGDNT

1 Timothy 1 in the DHNT

1 Timothy 1 in the DNT

1 Timothy 1 in the ELBE

1 Timothy 1 in the EMTV

1 Timothy 1 in the ESV

1 Timothy 1 in the FBV

1 Timothy 1 in the FEB

1 Timothy 1 in the GGMNT

1 Timothy 1 in the GNT

1 Timothy 1 in the HARY

1 Timothy 1 in the HNT

1 Timothy 1 in the IRVA

1 Timothy 1 in the IRVB

1 Timothy 1 in the IRVG

1 Timothy 1 in the IRVH

1 Timothy 1 in the IRVK

1 Timothy 1 in the IRVM

1 Timothy 1 in the IRVM2

1 Timothy 1 in the IRVO

1 Timothy 1 in the IRVP

1 Timothy 1 in the IRVT

1 Timothy 1 in the IRVT2

1 Timothy 1 in the IRVU

1 Timothy 1 in the ISVN

1 Timothy 1 in the JSNT

1 Timothy 1 in the KAPI

1 Timothy 1 in the KBT1ETNIK

1 Timothy 1 in the KBV

1 Timothy 1 in the KJV

1 Timothy 1 in the KNFD

1 Timothy 1 in the LBA

1 Timothy 1 in the LBLA

1 Timothy 1 in the LNT

1 Timothy 1 in the LSV

1 Timothy 1 in the MAAL

1 Timothy 1 in the MBV

1 Timothy 1 in the MBV2

1 Timothy 1 in the MHNT

1 Timothy 1 in the MKNFD

1 Timothy 1 in the MNG

1 Timothy 1 in the MNT

1 Timothy 1 in the MNT2

1 Timothy 1 in the MRS1T

1 Timothy 1 in the NAA

1 Timothy 1 in the NASB

1 Timothy 1 in the NBLA

1 Timothy 1 in the NBS

1 Timothy 1 in the NBVTP

1 Timothy 1 in the NET2

1 Timothy 1 in the NIV11

1 Timothy 1 in the NNT

1 Timothy 1 in the NNT2

1 Timothy 1 in the NNT3

1 Timothy 1 in the PDDPT

1 Timothy 1 in the PFNT

1 Timothy 1 in the RMNT

1 Timothy 1 in the SBIAS

1 Timothy 1 in the SBIBS

1 Timothy 1 in the SBIBS2

1 Timothy 1 in the SBICS

1 Timothy 1 in the SBIDS

1 Timothy 1 in the SBIGS

1 Timothy 1 in the SBIHS

1 Timothy 1 in the SBIIS

1 Timothy 1 in the SBIIS2

1 Timothy 1 in the SBIIS3

1 Timothy 1 in the SBIKS

1 Timothy 1 in the SBIKS2

1 Timothy 1 in the SBIMS

1 Timothy 1 in the SBIOS

1 Timothy 1 in the SBIPS

1 Timothy 1 in the SBISS

1 Timothy 1 in the SBITS

1 Timothy 1 in the SBITS2

1 Timothy 1 in the SBITS3

1 Timothy 1 in the SBITS4

1 Timothy 1 in the SBIUS

1 Timothy 1 in the SBIVS

1 Timothy 1 in the SBT

1 Timothy 1 in the SBT1E

1 Timothy 1 in the SCHL

1 Timothy 1 in the SNT

1 Timothy 1 in the SUSU

1 Timothy 1 in the SUSU2

1 Timothy 1 in the SYNO

1 Timothy 1 in the TBIAOTANT

1 Timothy 1 in the TBT1E

1 Timothy 1 in the TBT1E2

1 Timothy 1 in the TFTIP

1 Timothy 1 in the TFTU

1 Timothy 1 in the TGNTATF3T

1 Timothy 1 in the THAI

1 Timothy 1 in the TNFD

1 Timothy 1 in the TNT

1 Timothy 1 in the TNTIK

1 Timothy 1 in the TNTIL

1 Timothy 1 in the TNTIN

1 Timothy 1 in the TNTIP

1 Timothy 1 in the TNTIZ

1 Timothy 1 in the TOMA

1 Timothy 1 in the TTENT

1 Timothy 1 in the UBG

1 Timothy 1 in the UGV

1 Timothy 1 in the UGV2

1 Timothy 1 in the UGV3

1 Timothy 1 in the VBL

1 Timothy 1 in the VDCC

1 Timothy 1 in the YALU

1 Timothy 1 in the YAPE

1 Timothy 1 in the YBVTP

1 Timothy 1 in the ZBP