2 Corinthians 10 (BOHCB)

1 Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali’u da sanyin hali na Kiristi, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” a cikinku, amma “mai matsawa” sa’ad da nake rabe da ku! 2 Ina roƙonku cewa sa’ad da na zo kada ku tilasta ni in matsa muku, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha’anin duniya ne. 3 Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi. 4 Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. 5 Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. 6 A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika. 7 Kuna duban abubuwa bisa-bisa ne kawai. In wani ya ganin cewa shi na Kiristi ne, ya kamata yă sāke lura cewa kamar yadda yake na Kiristi, haka mu ma muke. 8 Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba ni da abin jin kunya a ciki. 9 Ba na so yă zama kamar ina ƙoƙari in tsorata ku ne da wasiƙuna. 10 Gama waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa suna da nauyi da kuma ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi, ba shi da wani kwarjini, maganarsa kuma ba kome ba ce.” 11 Ya kamata irin waɗannan mutane su gane cewa abin da muke faɗa a cikin wasiƙunmu sa’ad da ba ma nan tare da ku, shi muke aikatawa sa’ad da muke nan. 12 Ba za mu yi ƙarfin halin lissafta kanmu, ko mu kwatanta kanmu da waɗansu masu yabon kansu ba. Sa’ad da suke gwada kansu da kansu, da kuma kwatanta kansu da kansu, ba su da hikima. 13 Amma mu kam, ba za mu yi taƙama mu zarce iyakarmu ba, sai dai za mu yi taƙama cikin filin da Allah ya ƙayyade mana, filin kuwa ya kai har zuwa wurinku. 14 Ba mu wuce gona da iri a taƙamarmu ba, kamar yadda zai zama, da a ce ba mu zo wurinku ba, gama mun kai har wurinku da bisharar Kiristi. 15 Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba tă kuma shafi aikin waɗansu ba. Sai dai muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku yă riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske. 16 Saboda mu iya yin wa’azin bishara a yankunan da suke gaba da ku. Gama ba ma so mu yi taƙama game da aikin da aka riga aka yi a sashen wani. 17 Amma, “Duk mai yin taƙama, sai ya yi taƙama da Ubangiji.” 18 Ai, ba mai yabon kansa ake amincewa da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.

In Other Versions

2 Corinthians 10 in the ANGEFD

2 Corinthians 10 in the ANTPNG2D

2 Corinthians 10 in the AS21

2 Corinthians 10 in the BAGH

2 Corinthians 10 in the BBPNG

2 Corinthians 10 in the BBT1E

2 Corinthians 10 in the BDS

2 Corinthians 10 in the BEV

2 Corinthians 10 in the BHAD

2 Corinthians 10 in the BIB

2 Corinthians 10 in the BLPT

2 Corinthians 10 in the BNT

2 Corinthians 10 in the BNTABOOT

2 Corinthians 10 in the BNTLV

2 Corinthians 10 in the BOATCB

2 Corinthians 10 in the BOATCB2

2 Corinthians 10 in the BOBCV

2 Corinthians 10 in the BOCNT

2 Corinthians 10 in the BOECS

2 Corinthians 10 in the BOGWICC

2 Corinthians 10 in the BOHCV

2 Corinthians 10 in the BOHLNT

2 Corinthians 10 in the BOHNTLTAL

2 Corinthians 10 in the BOICB

2 Corinthians 10 in the BOILNTAP

2 Corinthians 10 in the BOITCV

2 Corinthians 10 in the BOKCV

2 Corinthians 10 in the BOKCV2

2 Corinthians 10 in the BOKHWOG

2 Corinthians 10 in the BOKSSV

2 Corinthians 10 in the BOLCB

2 Corinthians 10 in the BOLCB2

2 Corinthians 10 in the BOMCV

2 Corinthians 10 in the BONAV

2 Corinthians 10 in the BONCB

2 Corinthians 10 in the BONLT

2 Corinthians 10 in the BONUT2

2 Corinthians 10 in the BOPLNT

2 Corinthians 10 in the BOSCB

2 Corinthians 10 in the BOSNC

2 Corinthians 10 in the BOTLNT

2 Corinthians 10 in the BOVCB

2 Corinthians 10 in the BOYCB

2 Corinthians 10 in the BPBB

2 Corinthians 10 in the BPH

2 Corinthians 10 in the BSB

2 Corinthians 10 in the CCB

2 Corinthians 10 in the CUV

2 Corinthians 10 in the CUVS

2 Corinthians 10 in the DBT

2 Corinthians 10 in the DGDNT

2 Corinthians 10 in the DHNT

2 Corinthians 10 in the DNT

2 Corinthians 10 in the ELBE

2 Corinthians 10 in the EMTV

2 Corinthians 10 in the ESV

2 Corinthians 10 in the FBV

2 Corinthians 10 in the FEB

2 Corinthians 10 in the GGMNT

2 Corinthians 10 in the GNT

2 Corinthians 10 in the HARY

2 Corinthians 10 in the HNT

2 Corinthians 10 in the IRVA

2 Corinthians 10 in the IRVB

2 Corinthians 10 in the IRVG

2 Corinthians 10 in the IRVH

2 Corinthians 10 in the IRVK

2 Corinthians 10 in the IRVM

2 Corinthians 10 in the IRVM2

2 Corinthians 10 in the IRVO

2 Corinthians 10 in the IRVP

2 Corinthians 10 in the IRVT

2 Corinthians 10 in the IRVT2

2 Corinthians 10 in the IRVU

2 Corinthians 10 in the ISVN

2 Corinthians 10 in the JSNT

2 Corinthians 10 in the KAPI

2 Corinthians 10 in the KBT1ETNIK

2 Corinthians 10 in the KBV

2 Corinthians 10 in the KJV

2 Corinthians 10 in the KNFD

2 Corinthians 10 in the LBA

2 Corinthians 10 in the LBLA

2 Corinthians 10 in the LNT

2 Corinthians 10 in the LSV

2 Corinthians 10 in the MAAL

2 Corinthians 10 in the MBV

2 Corinthians 10 in the MBV2

2 Corinthians 10 in the MHNT

2 Corinthians 10 in the MKNFD

2 Corinthians 10 in the MNG

2 Corinthians 10 in the MNT

2 Corinthians 10 in the MNT2

2 Corinthians 10 in the MRS1T

2 Corinthians 10 in the NAA

2 Corinthians 10 in the NASB

2 Corinthians 10 in the NBLA

2 Corinthians 10 in the NBS

2 Corinthians 10 in the NBVTP

2 Corinthians 10 in the NET2

2 Corinthians 10 in the NIV11

2 Corinthians 10 in the NNT

2 Corinthians 10 in the NNT2

2 Corinthians 10 in the NNT3

2 Corinthians 10 in the PDDPT

2 Corinthians 10 in the PFNT

2 Corinthians 10 in the RMNT

2 Corinthians 10 in the SBIAS

2 Corinthians 10 in the SBIBS

2 Corinthians 10 in the SBIBS2

2 Corinthians 10 in the SBICS

2 Corinthians 10 in the SBIDS

2 Corinthians 10 in the SBIGS

2 Corinthians 10 in the SBIHS

2 Corinthians 10 in the SBIIS

2 Corinthians 10 in the SBIIS2

2 Corinthians 10 in the SBIIS3

2 Corinthians 10 in the SBIKS

2 Corinthians 10 in the SBIKS2

2 Corinthians 10 in the SBIMS

2 Corinthians 10 in the SBIOS

2 Corinthians 10 in the SBIPS

2 Corinthians 10 in the SBISS

2 Corinthians 10 in the SBITS

2 Corinthians 10 in the SBITS2

2 Corinthians 10 in the SBITS3

2 Corinthians 10 in the SBITS4

2 Corinthians 10 in the SBIUS

2 Corinthians 10 in the SBIVS

2 Corinthians 10 in the SBT

2 Corinthians 10 in the SBT1E

2 Corinthians 10 in the SCHL

2 Corinthians 10 in the SNT

2 Corinthians 10 in the SUSU

2 Corinthians 10 in the SUSU2

2 Corinthians 10 in the SYNO

2 Corinthians 10 in the TBIAOTANT

2 Corinthians 10 in the TBT1E

2 Corinthians 10 in the TBT1E2

2 Corinthians 10 in the TFTIP

2 Corinthians 10 in the TFTU

2 Corinthians 10 in the TGNTATF3T

2 Corinthians 10 in the THAI

2 Corinthians 10 in the TNFD

2 Corinthians 10 in the TNT

2 Corinthians 10 in the TNTIK

2 Corinthians 10 in the TNTIL

2 Corinthians 10 in the TNTIN

2 Corinthians 10 in the TNTIP

2 Corinthians 10 in the TNTIZ

2 Corinthians 10 in the TOMA

2 Corinthians 10 in the TTENT

2 Corinthians 10 in the UBG

2 Corinthians 10 in the UGV

2 Corinthians 10 in the UGV2

2 Corinthians 10 in the UGV3

2 Corinthians 10 in the VBL

2 Corinthians 10 in the VDCC

2 Corinthians 10 in the YALU

2 Corinthians 10 in the YAPE

2 Corinthians 10 in the YBVTP

2 Corinthians 10 in the ZBP