John 21 (BOHCB)

1 Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru. 2 Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare. 3 Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba. 4 Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba. 5 Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?”Suka amsa suka ce, “A’a.” 6 Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi. 7 Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. 8 Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. 9 Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi. 10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.” 11 Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba. 12 Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne. 13 Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin. 14 Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu. 15 Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?”Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.” 16 Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?”Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”Yesu ya ce, “Lura da tumakina.” 17 Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?”Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.”Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina. 18 Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.” 19 Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!” 20 Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”) 21 Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?” 22 Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.” 23 Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?” 24 Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce. 25 Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.

In Other Versions

John 21 in the ANGEFD

John 21 in the ANTPNG2D

John 21 in the AS21

John 21 in the BAGH

John 21 in the BBPNG

John 21 in the BBT1E

John 21 in the BDS

John 21 in the BEV

John 21 in the BHAD

John 21 in the BIB

John 21 in the BLPT

John 21 in the BNT

John 21 in the BNTABOOT

John 21 in the BNTLV

John 21 in the BOATCB

John 21 in the BOATCB2

John 21 in the BOBCV

John 21 in the BOCNT

John 21 in the BOECS

John 21 in the BOGWICC

John 21 in the BOHCV

John 21 in the BOHLNT

John 21 in the BOHNTLTAL

John 21 in the BOICB

John 21 in the BOILNTAP

John 21 in the BOITCV

John 21 in the BOKCV

John 21 in the BOKCV2

John 21 in the BOKHWOG

John 21 in the BOKSSV

John 21 in the BOLCB

John 21 in the BOLCB2

John 21 in the BOMCV

John 21 in the BONAV

John 21 in the BONCB

John 21 in the BONLT

John 21 in the BONUT2

John 21 in the BOPLNT

John 21 in the BOSCB

John 21 in the BOSNC

John 21 in the BOTLNT

John 21 in the BOVCB

John 21 in the BOYCB

John 21 in the BPBB

John 21 in the BPH

John 21 in the BSB

John 21 in the CCB

John 21 in the CUV

John 21 in the CUVS

John 21 in the DBT

John 21 in the DGDNT

John 21 in the DHNT

John 21 in the DNT

John 21 in the ELBE

John 21 in the EMTV

John 21 in the ESV

John 21 in the FBV

John 21 in the FEB

John 21 in the GGMNT

John 21 in the GNT

John 21 in the HARY

John 21 in the HNT

John 21 in the IRVA

John 21 in the IRVB

John 21 in the IRVG

John 21 in the IRVH

John 21 in the IRVK

John 21 in the IRVM

John 21 in the IRVM2

John 21 in the IRVO

John 21 in the IRVP

John 21 in the IRVT

John 21 in the IRVT2

John 21 in the IRVU

John 21 in the ISVN

John 21 in the JSNT

John 21 in the KAPI

John 21 in the KBT1ETNIK

John 21 in the KBV

John 21 in the KJV

John 21 in the KNFD

John 21 in the LBA

John 21 in the LBLA

John 21 in the LNT

John 21 in the LSV

John 21 in the MAAL

John 21 in the MBV

John 21 in the MBV2

John 21 in the MHNT

John 21 in the MKNFD

John 21 in the MNG

John 21 in the MNT

John 21 in the MNT2

John 21 in the MRS1T

John 21 in the NAA

John 21 in the NASB

John 21 in the NBLA

John 21 in the NBS

John 21 in the NBVTP

John 21 in the NET2

John 21 in the NIV11

John 21 in the NNT

John 21 in the NNT2

John 21 in the NNT3

John 21 in the PDDPT

John 21 in the PFNT

John 21 in the RMNT

John 21 in the SBIAS

John 21 in the SBIBS

John 21 in the SBIBS2

John 21 in the SBICS

John 21 in the SBIDS

John 21 in the SBIGS

John 21 in the SBIHS

John 21 in the SBIIS

John 21 in the SBIIS2

John 21 in the SBIIS3

John 21 in the SBIKS

John 21 in the SBIKS2

John 21 in the SBIMS

John 21 in the SBIOS

John 21 in the SBIPS

John 21 in the SBISS

John 21 in the SBITS

John 21 in the SBITS2

John 21 in the SBITS3

John 21 in the SBITS4

John 21 in the SBIUS

John 21 in the SBIVS

John 21 in the SBT

John 21 in the SBT1E

John 21 in the SCHL

John 21 in the SNT

John 21 in the SUSU

John 21 in the SUSU2

John 21 in the SYNO

John 21 in the TBIAOTANT

John 21 in the TBT1E

John 21 in the TBT1E2

John 21 in the TFTIP

John 21 in the TFTU

John 21 in the TGNTATF3T

John 21 in the THAI

John 21 in the TNFD

John 21 in the TNT

John 21 in the TNTIK

John 21 in the TNTIL

John 21 in the TNTIN

John 21 in the TNTIP

John 21 in the TNTIZ

John 21 in the TOMA

John 21 in the TTENT

John 21 in the UBG

John 21 in the UGV

John 21 in the UGV2

John 21 in the UGV3

John 21 in the VBL

John 21 in the VDCC

John 21 in the YALU

John 21 in the YAPE

John 21 in the YBVTP

John 21 in the ZBP