Luke 16 (BOHCB)

1 Yesu ya ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa. 2 Sai ya kira manajan, ya tambaye shi, ‘Me nake ji haka a kanka? Ka kawo lissafin aikinka, domin ba za ka iya cin gaba da aikinka ba.’ 3 “Sai manajan ya ce cikin tunaninsa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunyan yin bara. 4 Na san abin da zan yi, don mutane su karɓe ni a gidajensu, bayan an kore ni daga aiki a nan.’ 5 “Sai ya kira kowane ɗaya da maigidansa yake bin bashi. Ya tambayi na farkon ya ce, ‘Nawa ne maigidana yake bin ka?’ 6 “Ya amsa ya ce, ‘Garwar mai na zaitun guda ɗari tara.’ “Manajan ya ce, ‘Ga takardarka, ka zauna maza ka mai da shi ɗari huɗu.’ 7 “Ya kuma tambayi na biyun, ‘Kai fa, nawa ne ake bin ka?’ “Sai ya amsa ya ce, ‘Buhunan alkama dubu.’ “Ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi ɗari takwas.’ 8 “Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske. 9 Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama. 10 “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba. 11 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku? 13 “Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.” 14 Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki. 15 Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah. 16 “An yi shelar Doka da Annabawa har zuwa lokacin Yohanna. Tun daga lokacin nan, bisharar mulkin Allah ne ake wa’azinta, kowa kuma yana ƙoƙarin kutsa kai ya shiga. 17 Gama ta fi sauƙi sama da ƙasa su shuɗe, da a ce ɗigo guda ɗaya na rubutun, ya fita ya fāɗi daga cikin Doka. 18 “Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata mace, zina ne yake yi. Kuma mutumin da ya auri macen da aka sake, zina ne yake yi. 19 “An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum. 20 A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne. 21 Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa. 22 “Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. 23 A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa. 24 Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’ 25 “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba. 26 Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’ 27 “Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina, 28 gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’ 29 “Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’ 30 “Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’ 31 “Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”

In Other Versions

Luke 16 in the ANGEFD

Luke 16 in the ANTPNG2D

Luke 16 in the AS21

Luke 16 in the BAGH

Luke 16 in the BBPNG

Luke 16 in the BBT1E

Luke 16 in the BDS

Luke 16 in the BEV

Luke 16 in the BHAD

Luke 16 in the BIB

Luke 16 in the BLPT

Luke 16 in the BNT

Luke 16 in the BNTABOOT

Luke 16 in the BNTLV

Luke 16 in the BOATCB

Luke 16 in the BOATCB2

Luke 16 in the BOBCV

Luke 16 in the BOCNT

Luke 16 in the BOECS

Luke 16 in the BOGWICC

Luke 16 in the BOHCV

Luke 16 in the BOHLNT

Luke 16 in the BOHNTLTAL

Luke 16 in the BOICB

Luke 16 in the BOILNTAP

Luke 16 in the BOITCV

Luke 16 in the BOKCV

Luke 16 in the BOKCV2

Luke 16 in the BOKHWOG

Luke 16 in the BOKSSV

Luke 16 in the BOLCB

Luke 16 in the BOLCB2

Luke 16 in the BOMCV

Luke 16 in the BONAV

Luke 16 in the BONCB

Luke 16 in the BONLT

Luke 16 in the BONUT2

Luke 16 in the BOPLNT

Luke 16 in the BOSCB

Luke 16 in the BOSNC

Luke 16 in the BOTLNT

Luke 16 in the BOVCB

Luke 16 in the BOYCB

Luke 16 in the BPBB

Luke 16 in the BPH

Luke 16 in the BSB

Luke 16 in the CCB

Luke 16 in the CUV

Luke 16 in the CUVS

Luke 16 in the DBT

Luke 16 in the DGDNT

Luke 16 in the DHNT

Luke 16 in the DNT

Luke 16 in the ELBE

Luke 16 in the EMTV

Luke 16 in the ESV

Luke 16 in the FBV

Luke 16 in the FEB

Luke 16 in the GGMNT

Luke 16 in the GNT

Luke 16 in the HARY

Luke 16 in the HNT

Luke 16 in the IRVA

Luke 16 in the IRVB

Luke 16 in the IRVG

Luke 16 in the IRVH

Luke 16 in the IRVK

Luke 16 in the IRVM

Luke 16 in the IRVM2

Luke 16 in the IRVO

Luke 16 in the IRVP

Luke 16 in the IRVT

Luke 16 in the IRVT2

Luke 16 in the IRVU

Luke 16 in the ISVN

Luke 16 in the JSNT

Luke 16 in the KAPI

Luke 16 in the KBT1ETNIK

Luke 16 in the KBV

Luke 16 in the KJV

Luke 16 in the KNFD

Luke 16 in the LBA

Luke 16 in the LBLA

Luke 16 in the LNT

Luke 16 in the LSV

Luke 16 in the MAAL

Luke 16 in the MBV

Luke 16 in the MBV2

Luke 16 in the MHNT

Luke 16 in the MKNFD

Luke 16 in the MNG

Luke 16 in the MNT

Luke 16 in the MNT2

Luke 16 in the MRS1T

Luke 16 in the NAA

Luke 16 in the NASB

Luke 16 in the NBLA

Luke 16 in the NBS

Luke 16 in the NBVTP

Luke 16 in the NET2

Luke 16 in the NIV11

Luke 16 in the NNT

Luke 16 in the NNT2

Luke 16 in the NNT3

Luke 16 in the PDDPT

Luke 16 in the PFNT

Luke 16 in the RMNT

Luke 16 in the SBIAS

Luke 16 in the SBIBS

Luke 16 in the SBIBS2

Luke 16 in the SBICS

Luke 16 in the SBIDS

Luke 16 in the SBIGS

Luke 16 in the SBIHS

Luke 16 in the SBIIS

Luke 16 in the SBIIS2

Luke 16 in the SBIIS3

Luke 16 in the SBIKS

Luke 16 in the SBIKS2

Luke 16 in the SBIMS

Luke 16 in the SBIOS

Luke 16 in the SBIPS

Luke 16 in the SBISS

Luke 16 in the SBITS

Luke 16 in the SBITS2

Luke 16 in the SBITS3

Luke 16 in the SBITS4

Luke 16 in the SBIUS

Luke 16 in the SBIVS

Luke 16 in the SBT

Luke 16 in the SBT1E

Luke 16 in the SCHL

Luke 16 in the SNT

Luke 16 in the SUSU

Luke 16 in the SUSU2

Luke 16 in the SYNO

Luke 16 in the TBIAOTANT

Luke 16 in the TBT1E

Luke 16 in the TBT1E2

Luke 16 in the TFTIP

Luke 16 in the TFTU

Luke 16 in the TGNTATF3T

Luke 16 in the THAI

Luke 16 in the TNFD

Luke 16 in the TNT

Luke 16 in the TNTIK

Luke 16 in the TNTIL

Luke 16 in the TNTIN

Luke 16 in the TNTIP

Luke 16 in the TNTIZ

Luke 16 in the TOMA

Luke 16 in the TTENT

Luke 16 in the UBG

Luke 16 in the UGV

Luke 16 in the UGV2

Luke 16 in the UGV3

Luke 16 in the VBL

Luke 16 in the VDCC

Luke 16 in the YALU

Luke 16 in the YAPE

Luke 16 in the YBVTP

Luke 16 in the ZBP