Matthew 25 (BOHCB)

1 “A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango. 2 Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima. 3 Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba. 4 Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu. 5 Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su. 6 “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’ 7 “Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu. 8 Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’ 9 “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’ 10 “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa. 11 “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’ 12 “Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’ 13 “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba. 14 “Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa. 15 Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa. 16 Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar. 17 Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu. 18 Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa. 19 “Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su. 20 Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’ 21 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ 22 “Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’ 23 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ 24 “Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba. 25 Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.’ 26 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba? 27 To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba. 28 “ ‘Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma. 29 Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa. 30 Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’ 31 “Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama. 32 Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki. 33 Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa. 34 “Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya. 35 Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni, 36 da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’ 37 “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? 38 Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura? 39 Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’ 40 “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’ 41 “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa. 42 Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba, 43 da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’ 44 “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’ 45 “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’ 46 “Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”

In Other Versions

Matthew 25 in the ANGEFD

Matthew 25 in the ANTPNG2D

Matthew 25 in the AS21

Matthew 25 in the BAGH

Matthew 25 in the BBPNG

Matthew 25 in the BBT1E

Matthew 25 in the BDS

Matthew 25 in the BEV

Matthew 25 in the BHAD

Matthew 25 in the BIB

Matthew 25 in the BLPT

Matthew 25 in the BNT

Matthew 25 in the BNTABOOT

Matthew 25 in the BNTLV

Matthew 25 in the BOATCB

Matthew 25 in the BOATCB2

Matthew 25 in the BOBCV

Matthew 25 in the BOCNT

Matthew 25 in the BOECS

Matthew 25 in the BOGWICC

Matthew 25 in the BOHCV

Matthew 25 in the BOHLNT

Matthew 25 in the BOHNTLTAL

Matthew 25 in the BOICB

Matthew 25 in the BOILNTAP

Matthew 25 in the BOITCV

Matthew 25 in the BOKCV

Matthew 25 in the BOKCV2

Matthew 25 in the BOKHWOG

Matthew 25 in the BOKSSV

Matthew 25 in the BOLCB

Matthew 25 in the BOLCB2

Matthew 25 in the BOMCV

Matthew 25 in the BONAV

Matthew 25 in the BONCB

Matthew 25 in the BONLT

Matthew 25 in the BONUT2

Matthew 25 in the BOPLNT

Matthew 25 in the BOSCB

Matthew 25 in the BOSNC

Matthew 25 in the BOTLNT

Matthew 25 in the BOVCB

Matthew 25 in the BOYCB

Matthew 25 in the BPBB

Matthew 25 in the BPH

Matthew 25 in the BSB

Matthew 25 in the CCB

Matthew 25 in the CUV

Matthew 25 in the CUVS

Matthew 25 in the DBT

Matthew 25 in the DGDNT

Matthew 25 in the DHNT

Matthew 25 in the DNT

Matthew 25 in the ELBE

Matthew 25 in the EMTV

Matthew 25 in the ESV

Matthew 25 in the FBV

Matthew 25 in the FEB

Matthew 25 in the GGMNT

Matthew 25 in the GNT

Matthew 25 in the HARY

Matthew 25 in the HNT

Matthew 25 in the IRVA

Matthew 25 in the IRVB

Matthew 25 in the IRVG

Matthew 25 in the IRVH

Matthew 25 in the IRVK

Matthew 25 in the IRVM

Matthew 25 in the IRVM2

Matthew 25 in the IRVO

Matthew 25 in the IRVP

Matthew 25 in the IRVT

Matthew 25 in the IRVT2

Matthew 25 in the IRVU

Matthew 25 in the ISVN

Matthew 25 in the JSNT

Matthew 25 in the KAPI

Matthew 25 in the KBT1ETNIK

Matthew 25 in the KBV

Matthew 25 in the KJV

Matthew 25 in the KNFD

Matthew 25 in the LBA

Matthew 25 in the LBLA

Matthew 25 in the LNT

Matthew 25 in the LSV

Matthew 25 in the MAAL

Matthew 25 in the MBV

Matthew 25 in the MBV2

Matthew 25 in the MHNT

Matthew 25 in the MKNFD

Matthew 25 in the MNG

Matthew 25 in the MNT

Matthew 25 in the MNT2

Matthew 25 in the MRS1T

Matthew 25 in the NAA

Matthew 25 in the NASB

Matthew 25 in the NBLA

Matthew 25 in the NBS

Matthew 25 in the NBVTP

Matthew 25 in the NET2

Matthew 25 in the NIV11

Matthew 25 in the NNT

Matthew 25 in the NNT2

Matthew 25 in the NNT3

Matthew 25 in the PDDPT

Matthew 25 in the PFNT

Matthew 25 in the RMNT

Matthew 25 in the SBIAS

Matthew 25 in the SBIBS

Matthew 25 in the SBIBS2

Matthew 25 in the SBICS

Matthew 25 in the SBIDS

Matthew 25 in the SBIGS

Matthew 25 in the SBIHS

Matthew 25 in the SBIIS

Matthew 25 in the SBIIS2

Matthew 25 in the SBIIS3

Matthew 25 in the SBIKS

Matthew 25 in the SBIKS2

Matthew 25 in the SBIMS

Matthew 25 in the SBIOS

Matthew 25 in the SBIPS

Matthew 25 in the SBISS

Matthew 25 in the SBITS

Matthew 25 in the SBITS2

Matthew 25 in the SBITS3

Matthew 25 in the SBITS4

Matthew 25 in the SBIUS

Matthew 25 in the SBIVS

Matthew 25 in the SBT

Matthew 25 in the SBT1E

Matthew 25 in the SCHL

Matthew 25 in the SNT

Matthew 25 in the SUSU

Matthew 25 in the SUSU2

Matthew 25 in the SYNO

Matthew 25 in the TBIAOTANT

Matthew 25 in the TBT1E

Matthew 25 in the TBT1E2

Matthew 25 in the TFTIP

Matthew 25 in the TFTU

Matthew 25 in the TGNTATF3T

Matthew 25 in the THAI

Matthew 25 in the TNFD

Matthew 25 in the TNT

Matthew 25 in the TNTIK

Matthew 25 in the TNTIL

Matthew 25 in the TNTIN

Matthew 25 in the TNTIP

Matthew 25 in the TNTIZ

Matthew 25 in the TOMA

Matthew 25 in the TTENT

Matthew 25 in the UBG

Matthew 25 in the UGV

Matthew 25 in the UGV2

Matthew 25 in the UGV3

Matthew 25 in the VBL

Matthew 25 in the VDCC

Matthew 25 in the YALU

Matthew 25 in the YAPE

Matthew 25 in the YBVTP

Matthew 25 in the ZBP