Mark 10 (BOHCB)

1 Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba. 2 Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?” 3 Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?” 4 Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.” 5 Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka. 6 Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’ 7 ‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, 8 su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’ Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya. 9 Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.” 10 Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan. 11 Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki. 12 In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.” 13 Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su. 14 Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 15 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.” 16 Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su. 17 Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?” 18 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 19 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’” 20 Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.” 21 Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.” 22 Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai. 23 Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!” 24 Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “’Ya’yana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah! 25 Ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.” 26 Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?” 27 Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.” 28 Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!” 29 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, 30 sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami. 31 Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma, za su zama na farko.” 32 Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna bin sa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi. 33 Ya ce, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Al’ummai, 34 waɗanda za su yi masa ba’a, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yă tashi.” 35 Sai Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zebedi maza suka zo wurinsa suka ce, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙa.” 36 Ya tambaye su ya ce, “Me kuke so in yi muku?” 37 Suka amsa suka ce, “Ka bar ɗayanmu yă zauna a damarka, ɗayan kuma a hagunka, a cikin ɗaukakarka.” 38 Yesu ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya shan kwaf da zan sha, ko a yi muku baftisma da baftismar da aka yi mini?” 39 Suka ce, “Za mu iya.”Yesu ya ce musu, “Za ku sha kwaf da zan sha, a kuma yi muku baftisma da aka yi mini, 40 amma zama a damana ko haguna, ba ni nake ba da izinin ba. Waɗannan wurare na waɗanda aka riga aka shirya musu ne.” 41 Da sauran goman suka ji wannan, sai suka yi fushi da Yaƙub da Yohanna. 42 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko. 43 Ba haka ya kamata yă zama da ku ba. A maimakon, duk wanda yake so yă zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku. 44 Duk wanda kuma yake so yă zama na farko, dole yă zama bawan kowa. 45 Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.” 46 Sai suka iso Yeriko. Sa’ad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa (wato, “ɗan Timawus”), yana zaune a gefen hanya yana bara. 47 Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” 48 Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yă yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” 49 Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kira shi.”Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.” 50 Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu. 51 Yesu ya tambaye shi ya ce, “Me kake so in yi maka?”Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.” 52 Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.

In Other Versions

Mark 10 in the ANGEFD

Mark 10 in the ANTPNG2D

Mark 10 in the AS21

Mark 10 in the BAGH

Mark 10 in the BBPNG

Mark 10 in the BBT1E

Mark 10 in the BDS

Mark 10 in the BEV

Mark 10 in the BHAD

Mark 10 in the BIB

Mark 10 in the BLPT

Mark 10 in the BNT

Mark 10 in the BNTABOOT

Mark 10 in the BNTLV

Mark 10 in the BOATCB

Mark 10 in the BOATCB2

Mark 10 in the BOBCV

Mark 10 in the BOCNT

Mark 10 in the BOECS

Mark 10 in the BOGWICC

Mark 10 in the BOHCV

Mark 10 in the BOHLNT

Mark 10 in the BOHNTLTAL

Mark 10 in the BOICB

Mark 10 in the BOILNTAP

Mark 10 in the BOITCV

Mark 10 in the BOKCV

Mark 10 in the BOKCV2

Mark 10 in the BOKHWOG

Mark 10 in the BOKSSV

Mark 10 in the BOLCB

Mark 10 in the BOLCB2

Mark 10 in the BOMCV

Mark 10 in the BONAV

Mark 10 in the BONCB

Mark 10 in the BONLT

Mark 10 in the BONUT2

Mark 10 in the BOPLNT

Mark 10 in the BOSCB

Mark 10 in the BOSNC

Mark 10 in the BOTLNT

Mark 10 in the BOVCB

Mark 10 in the BOYCB

Mark 10 in the BPBB

Mark 10 in the BPH

Mark 10 in the BSB

Mark 10 in the CCB

Mark 10 in the CUV

Mark 10 in the CUVS

Mark 10 in the DBT

Mark 10 in the DGDNT

Mark 10 in the DHNT

Mark 10 in the DNT

Mark 10 in the ELBE

Mark 10 in the EMTV

Mark 10 in the ESV

Mark 10 in the FBV

Mark 10 in the FEB

Mark 10 in the GGMNT

Mark 10 in the GNT

Mark 10 in the HARY

Mark 10 in the HNT

Mark 10 in the IRVA

Mark 10 in the IRVB

Mark 10 in the IRVG

Mark 10 in the IRVH

Mark 10 in the IRVK

Mark 10 in the IRVM

Mark 10 in the IRVM2

Mark 10 in the IRVO

Mark 10 in the IRVP

Mark 10 in the IRVT

Mark 10 in the IRVT2

Mark 10 in the IRVU

Mark 10 in the ISVN

Mark 10 in the JSNT

Mark 10 in the KAPI

Mark 10 in the KBT1ETNIK

Mark 10 in the KBV

Mark 10 in the KJV

Mark 10 in the KNFD

Mark 10 in the LBA

Mark 10 in the LBLA

Mark 10 in the LNT

Mark 10 in the LSV

Mark 10 in the MAAL

Mark 10 in the MBV

Mark 10 in the MBV2

Mark 10 in the MHNT

Mark 10 in the MKNFD

Mark 10 in the MNG

Mark 10 in the MNT

Mark 10 in the MNT2

Mark 10 in the MRS1T

Mark 10 in the NAA

Mark 10 in the NASB

Mark 10 in the NBLA

Mark 10 in the NBS

Mark 10 in the NBVTP

Mark 10 in the NET2

Mark 10 in the NIV11

Mark 10 in the NNT

Mark 10 in the NNT2

Mark 10 in the NNT3

Mark 10 in the PDDPT

Mark 10 in the PFNT

Mark 10 in the RMNT

Mark 10 in the SBIAS

Mark 10 in the SBIBS

Mark 10 in the SBIBS2

Mark 10 in the SBICS

Mark 10 in the SBIDS

Mark 10 in the SBIGS

Mark 10 in the SBIHS

Mark 10 in the SBIIS

Mark 10 in the SBIIS2

Mark 10 in the SBIIS3

Mark 10 in the SBIKS

Mark 10 in the SBIKS2

Mark 10 in the SBIMS

Mark 10 in the SBIOS

Mark 10 in the SBIPS

Mark 10 in the SBISS

Mark 10 in the SBITS

Mark 10 in the SBITS2

Mark 10 in the SBITS3

Mark 10 in the SBITS4

Mark 10 in the SBIUS

Mark 10 in the SBIVS

Mark 10 in the SBT

Mark 10 in the SBT1E

Mark 10 in the SCHL

Mark 10 in the SNT

Mark 10 in the SUSU

Mark 10 in the SUSU2

Mark 10 in the SYNO

Mark 10 in the TBIAOTANT

Mark 10 in the TBT1E

Mark 10 in the TBT1E2

Mark 10 in the TFTIP

Mark 10 in the TFTU

Mark 10 in the TGNTATF3T

Mark 10 in the THAI

Mark 10 in the TNFD

Mark 10 in the TNT

Mark 10 in the TNTIK

Mark 10 in the TNTIL

Mark 10 in the TNTIN

Mark 10 in the TNTIP

Mark 10 in the TNTIZ

Mark 10 in the TOMA

Mark 10 in the TTENT

Mark 10 in the UBG

Mark 10 in the UGV

Mark 10 in the UGV2

Mark 10 in the UGV3

Mark 10 in the VBL

Mark 10 in the VDCC

Mark 10 in the YALU

Mark 10 in the YAPE

Mark 10 in the YBVTP

Mark 10 in the ZBP