Mark 16 (BOHCB)
1 Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu. 2 A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan, 3 sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?” 4 Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne. 5 Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita. 6 Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi. 7 Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ” 8 Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro. 9 Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta. 10 Ta je ta gaya wa waɗanda dā suke tare da shi, waɗanda kuma suke makoki da kuka. 11 Da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su gaskata ba. 12 Daga baya Yesu ya bayyana a wani kamanni dabam ga biyunsu, yayinda suke tafiya ƙauye. 13 Waɗannan kuwa suka koma suka shaida wa sauran, amma su ma ba su gaskata ba. 14 Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi. 15 Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta. 16 Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka. 17 Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna. 18 Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.” 19 Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah. 20 Sai almajiran suka fita, suka yi wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar.
In Other Versions
Mark 16 in the ANGEFD
Mark 16 in the ANTPNG2D
Mark 16 in the AS21
Mark 16 in the BAGH
Mark 16 in the BBPNG
Mark 16 in the BBT1E
Mark 16 in the BDS
Mark 16 in the BEV
Mark 16 in the BHAD
Mark 16 in the BIB
Mark 16 in the BLPT
Mark 16 in the BNT
Mark 16 in the BNTABOOT
Mark 16 in the BNTLV
Mark 16 in the BOATCB
Mark 16 in the BOATCB2
Mark 16 in the BOBCV
Mark 16 in the BOCNT
Mark 16 in the BOECS
Mark 16 in the BOGWICC
Mark 16 in the BOHCV
Mark 16 in the BOHLNT
Mark 16 in the BOHNTLTAL
Mark 16 in the BOICB
Mark 16 in the BOILNTAP
Mark 16 in the BOITCV
Mark 16 in the BOKCV
Mark 16 in the BOKCV2
Mark 16 in the BOKHWOG
Mark 16 in the BOKSSV
Mark 16 in the BOLCB
Mark 16 in the BOLCB2
Mark 16 in the BOMCV
Mark 16 in the BONAV
Mark 16 in the BONCB
Mark 16 in the BONLT
Mark 16 in the BONUT2
Mark 16 in the BOPLNT
Mark 16 in the BOSCB
Mark 16 in the BOSNC
Mark 16 in the BOTLNT
Mark 16 in the BOVCB
Mark 16 in the BOYCB
Mark 16 in the BPBB
Mark 16 in the BPH
Mark 16 in the BSB
Mark 16 in the CCB
Mark 16 in the CUV
Mark 16 in the CUVS
Mark 16 in the DBT
Mark 16 in the DGDNT
Mark 16 in the DHNT
Mark 16 in the DNT
Mark 16 in the ELBE
Mark 16 in the EMTV
Mark 16 in the ESV
Mark 16 in the FBV
Mark 16 in the FEB
Mark 16 in the GGMNT
Mark 16 in the GNT
Mark 16 in the HARY
Mark 16 in the HNT
Mark 16 in the IRVA
Mark 16 in the IRVB
Mark 16 in the IRVG
Mark 16 in the IRVH
Mark 16 in the IRVK
Mark 16 in the IRVM
Mark 16 in the IRVM2
Mark 16 in the IRVO
Mark 16 in the IRVP
Mark 16 in the IRVT
Mark 16 in the IRVT2
Mark 16 in the IRVU
Mark 16 in the ISVN
Mark 16 in the JSNT
Mark 16 in the KAPI
Mark 16 in the KBT1ETNIK
Mark 16 in the KBV
Mark 16 in the KJV
Mark 16 in the KNFD
Mark 16 in the LBA
Mark 16 in the LBLA
Mark 16 in the LNT
Mark 16 in the LSV
Mark 16 in the MAAL
Mark 16 in the MBV
Mark 16 in the MBV2
Mark 16 in the MHNT
Mark 16 in the MKNFD
Mark 16 in the MNG
Mark 16 in the MNT
Mark 16 in the MNT2
Mark 16 in the MRS1T
Mark 16 in the NAA
Mark 16 in the NASB
Mark 16 in the NBLA
Mark 16 in the NBS
Mark 16 in the NBVTP
Mark 16 in the NET2
Mark 16 in the NIV11
Mark 16 in the NNT
Mark 16 in the NNT2
Mark 16 in the NNT3
Mark 16 in the PDDPT
Mark 16 in the PFNT
Mark 16 in the RMNT
Mark 16 in the SBIAS
Mark 16 in the SBIBS
Mark 16 in the SBIBS2
Mark 16 in the SBICS
Mark 16 in the SBIDS
Mark 16 in the SBIGS
Mark 16 in the SBIHS
Mark 16 in the SBIIS
Mark 16 in the SBIIS2
Mark 16 in the SBIIS3
Mark 16 in the SBIKS
Mark 16 in the SBIKS2
Mark 16 in the SBIMS
Mark 16 in the SBIOS
Mark 16 in the SBIPS
Mark 16 in the SBISS
Mark 16 in the SBITS
Mark 16 in the SBITS2
Mark 16 in the SBITS3
Mark 16 in the SBITS4
Mark 16 in the SBIUS
Mark 16 in the SBIVS
Mark 16 in the SBT
Mark 16 in the SBT1E
Mark 16 in the SCHL
Mark 16 in the SNT
Mark 16 in the SUSU
Mark 16 in the SUSU2
Mark 16 in the SYNO
Mark 16 in the TBIAOTANT
Mark 16 in the TBT1E
Mark 16 in the TBT1E2
Mark 16 in the TFTIP
Mark 16 in the TFTU
Mark 16 in the TGNTATF3T
Mark 16 in the THAI
Mark 16 in the TNFD
Mark 16 in the TNT
Mark 16 in the TNTIK
Mark 16 in the TNTIL
Mark 16 in the TNTIN
Mark 16 in the TNTIP
Mark 16 in the TNTIZ
Mark 16 in the TOMA
Mark 16 in the TTENT
Mark 16 in the UBG
Mark 16 in the UGV
Mark 16 in the UGV2
Mark 16 in the UGV3
Mark 16 in the VBL
Mark 16 in the VDCC
Mark 16 in the YALU
Mark 16 in the YAPE
Mark 16 in the YBVTP
Mark 16 in the ZBP