Titus 3 (BOHCB)

1 Ka tuna wa mutane su zama masu biyayya ga masu mulki da kuma hukumomi, su zama masu biyayya suna kuma a shirye su yi kowane abin da yake mai kyau, 2 kada su zama masu ɓata sunan kowa, su zama masu salama da kulawa, su kuma zama masu matuƙar tawali’u ga dukan mutane. 3 A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna. 4 Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana, 5 sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki, 6 wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu, 7 wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami. 8 Wannan magana tabbatacciya ce, ina kuma so ka nanata waɗannan abubuwa ƙwarai, domin waɗanda suka dogara ga Allah su himmantu ga aiki mai kyau. Waɗannan abubuwa suna da kyau sosai suna kuma da amfani ga kowane mutum. 9 Amma ka guji jayayyar banza da ƙididdigar asali da gardandami da faɗace-faɗace game da Doka, gama ba su da riba kuma aikin banza ne. 10 Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi. 11 Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci. 12 Da zarar na aika Artemas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina a Nikofolis, domin na yanke shawara in ci damina a can. 13 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan da Afollos a hanyarsu ka kuma tabbata ba su rasa kome ba. 14 Dole mutanenmu su koyi ba da kansu ga aikata abin da yake nagari, domin su iya biyan bukatunsu na yau da kullum kada kuma su yi rayuwar marar amfani. 15 Dukan waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka.Ka gaggai mini da masoyanmu, masu bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku duka.

In Other Versions

Titus 3 in the ANGEFD

Titus 3 in the ANTPNG2D

Titus 3 in the AS21

Titus 3 in the BAGH

Titus 3 in the BBPNG

Titus 3 in the BBT1E

Titus 3 in the BDS

Titus 3 in the BEV

Titus 3 in the BHAD

Titus 3 in the BIB

Titus 3 in the BLPT

Titus 3 in the BNT

Titus 3 in the BNTABOOT

Titus 3 in the BNTLV

Titus 3 in the BOATCB

Titus 3 in the BOATCB2

Titus 3 in the BOBCV

Titus 3 in the BOCNT

Titus 3 in the BOECS

Titus 3 in the BOGWICC

Titus 3 in the BOHCV

Titus 3 in the BOHLNT

Titus 3 in the BOHNTLTAL

Titus 3 in the BOICB

Titus 3 in the BOILNTAP

Titus 3 in the BOITCV

Titus 3 in the BOKCV

Titus 3 in the BOKCV2

Titus 3 in the BOKHWOG

Titus 3 in the BOKSSV

Titus 3 in the BOLCB

Titus 3 in the BOLCB2

Titus 3 in the BOMCV

Titus 3 in the BONAV

Titus 3 in the BONCB

Titus 3 in the BONLT

Titus 3 in the BONUT2

Titus 3 in the BOPLNT

Titus 3 in the BOSCB

Titus 3 in the BOSNC

Titus 3 in the BOTLNT

Titus 3 in the BOVCB

Titus 3 in the BOYCB

Titus 3 in the BPBB

Titus 3 in the BPH

Titus 3 in the BSB

Titus 3 in the CCB

Titus 3 in the CUV

Titus 3 in the CUVS

Titus 3 in the DBT

Titus 3 in the DGDNT

Titus 3 in the DHNT

Titus 3 in the DNT

Titus 3 in the ELBE

Titus 3 in the EMTV

Titus 3 in the ESV

Titus 3 in the FBV

Titus 3 in the FEB

Titus 3 in the GGMNT

Titus 3 in the GNT

Titus 3 in the HARY

Titus 3 in the HNT

Titus 3 in the IRVA

Titus 3 in the IRVB

Titus 3 in the IRVG

Titus 3 in the IRVH

Titus 3 in the IRVK

Titus 3 in the IRVM

Titus 3 in the IRVM2

Titus 3 in the IRVO

Titus 3 in the IRVP

Titus 3 in the IRVT

Titus 3 in the IRVT2

Titus 3 in the IRVU

Titus 3 in the ISVN

Titus 3 in the JSNT

Titus 3 in the KAPI

Titus 3 in the KBT1ETNIK

Titus 3 in the KBV

Titus 3 in the KJV

Titus 3 in the KNFD

Titus 3 in the LBA

Titus 3 in the LBLA

Titus 3 in the LNT

Titus 3 in the LSV

Titus 3 in the MAAL

Titus 3 in the MBV

Titus 3 in the MBV2

Titus 3 in the MHNT

Titus 3 in the MKNFD

Titus 3 in the MNG

Titus 3 in the MNT

Titus 3 in the MNT2

Titus 3 in the MRS1T

Titus 3 in the NAA

Titus 3 in the NASB

Titus 3 in the NBLA

Titus 3 in the NBS

Titus 3 in the NBVTP

Titus 3 in the NET2

Titus 3 in the NIV11

Titus 3 in the NNT

Titus 3 in the NNT2

Titus 3 in the NNT3

Titus 3 in the PDDPT

Titus 3 in the PFNT

Titus 3 in the RMNT

Titus 3 in the SBIAS

Titus 3 in the SBIBS

Titus 3 in the SBIBS2

Titus 3 in the SBICS

Titus 3 in the SBIDS

Titus 3 in the SBIGS

Titus 3 in the SBIHS

Titus 3 in the SBIIS

Titus 3 in the SBIIS2

Titus 3 in the SBIIS3

Titus 3 in the SBIKS

Titus 3 in the SBIKS2

Titus 3 in the SBIMS

Titus 3 in the SBIOS

Titus 3 in the SBIPS

Titus 3 in the SBISS

Titus 3 in the SBITS

Titus 3 in the SBITS2

Titus 3 in the SBITS3

Titus 3 in the SBITS4

Titus 3 in the SBIUS

Titus 3 in the SBIVS

Titus 3 in the SBT

Titus 3 in the SBT1E

Titus 3 in the SCHL

Titus 3 in the SNT

Titus 3 in the SUSU

Titus 3 in the SUSU2

Titus 3 in the SYNO

Titus 3 in the TBIAOTANT

Titus 3 in the TBT1E

Titus 3 in the TBT1E2

Titus 3 in the TFTIP

Titus 3 in the TFTU

Titus 3 in the TGNTATF3T

Titus 3 in the THAI

Titus 3 in the TNFD

Titus 3 in the TNT

Titus 3 in the TNTIK

Titus 3 in the TNTIL

Titus 3 in the TNTIN

Titus 3 in the TNTIP

Titus 3 in the TNTIZ

Titus 3 in the TOMA

Titus 3 in the TTENT

Titus 3 in the UBG

Titus 3 in the UGV

Titus 3 in the UGV2

Titus 3 in the UGV3

Titus 3 in the VBL

Titus 3 in the VDCC

Titus 3 in the YALU

Titus 3 in the YAPE

Titus 3 in the YBVTP

Titus 3 in the ZBP