1 Corinthians 2 (BOHCB)

1 Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba. 2 Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye. 3 Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. 4 Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, 5 domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah. 6 Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. 7 A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. 8 Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. 9 Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa,“Ba idon da ya taɓa gani,ba kunnen da ya taɓa ji,ba kuma zuciyar da ta taɓa tunaninabin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.” 10 Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa.Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah. 11 Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12 Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. 13 Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya. 14 Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu. 15 Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum. 16 “Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji,har da zai koya masa?”Amma muna da tunani iri na Kiristi ne.

In Other Versions

1 Corinthians 2 in the ANGEFD

1 Corinthians 2 in the ANTPNG2D

1 Corinthians 2 in the AS21

1 Corinthians 2 in the BAGH

1 Corinthians 2 in the BBPNG

1 Corinthians 2 in the BBT1E

1 Corinthians 2 in the BDS

1 Corinthians 2 in the BEV

1 Corinthians 2 in the BHAD

1 Corinthians 2 in the BIB

1 Corinthians 2 in the BLPT

1 Corinthians 2 in the BNT

1 Corinthians 2 in the BNTABOOT

1 Corinthians 2 in the BNTLV

1 Corinthians 2 in the BOATCB

1 Corinthians 2 in the BOATCB2

1 Corinthians 2 in the BOBCV

1 Corinthians 2 in the BOCNT

1 Corinthians 2 in the BOECS

1 Corinthians 2 in the BOGWICC

1 Corinthians 2 in the BOHCV

1 Corinthians 2 in the BOHLNT

1 Corinthians 2 in the BOHNTLTAL

1 Corinthians 2 in the BOICB

1 Corinthians 2 in the BOILNTAP

1 Corinthians 2 in the BOITCV

1 Corinthians 2 in the BOKCV

1 Corinthians 2 in the BOKCV2

1 Corinthians 2 in the BOKHWOG

1 Corinthians 2 in the BOKSSV

1 Corinthians 2 in the BOLCB

1 Corinthians 2 in the BOLCB2

1 Corinthians 2 in the BOMCV

1 Corinthians 2 in the BONAV

1 Corinthians 2 in the BONCB

1 Corinthians 2 in the BONLT

1 Corinthians 2 in the BONUT2

1 Corinthians 2 in the BOPLNT

1 Corinthians 2 in the BOSCB

1 Corinthians 2 in the BOSNC

1 Corinthians 2 in the BOTLNT

1 Corinthians 2 in the BOVCB

1 Corinthians 2 in the BOYCB

1 Corinthians 2 in the BPBB

1 Corinthians 2 in the BPH

1 Corinthians 2 in the BSB

1 Corinthians 2 in the CCB

1 Corinthians 2 in the CUV

1 Corinthians 2 in the CUVS

1 Corinthians 2 in the DBT

1 Corinthians 2 in the DGDNT

1 Corinthians 2 in the DHNT

1 Corinthians 2 in the DNT

1 Corinthians 2 in the ELBE

1 Corinthians 2 in the EMTV

1 Corinthians 2 in the ESV

1 Corinthians 2 in the FBV

1 Corinthians 2 in the FEB

1 Corinthians 2 in the GGMNT

1 Corinthians 2 in the GNT

1 Corinthians 2 in the HARY

1 Corinthians 2 in the HNT

1 Corinthians 2 in the IRVA

1 Corinthians 2 in the IRVB

1 Corinthians 2 in the IRVG

1 Corinthians 2 in the IRVH

1 Corinthians 2 in the IRVK

1 Corinthians 2 in the IRVM

1 Corinthians 2 in the IRVM2

1 Corinthians 2 in the IRVO

1 Corinthians 2 in the IRVP

1 Corinthians 2 in the IRVT

1 Corinthians 2 in the IRVT2

1 Corinthians 2 in the IRVU

1 Corinthians 2 in the ISVN

1 Corinthians 2 in the JSNT

1 Corinthians 2 in the KAPI

1 Corinthians 2 in the KBT1ETNIK

1 Corinthians 2 in the KBV

1 Corinthians 2 in the KJV

1 Corinthians 2 in the KNFD

1 Corinthians 2 in the LBA

1 Corinthians 2 in the LBLA

1 Corinthians 2 in the LNT

1 Corinthians 2 in the LSV

1 Corinthians 2 in the MAAL

1 Corinthians 2 in the MBV

1 Corinthians 2 in the MBV2

1 Corinthians 2 in the MHNT

1 Corinthians 2 in the MKNFD

1 Corinthians 2 in the MNG

1 Corinthians 2 in the MNT

1 Corinthians 2 in the MNT2

1 Corinthians 2 in the MRS1T

1 Corinthians 2 in the NAA

1 Corinthians 2 in the NASB

1 Corinthians 2 in the NBLA

1 Corinthians 2 in the NBS

1 Corinthians 2 in the NBVTP

1 Corinthians 2 in the NET2

1 Corinthians 2 in the NIV11

1 Corinthians 2 in the NNT

1 Corinthians 2 in the NNT2

1 Corinthians 2 in the NNT3

1 Corinthians 2 in the PDDPT

1 Corinthians 2 in the PFNT

1 Corinthians 2 in the RMNT

1 Corinthians 2 in the SBIAS

1 Corinthians 2 in the SBIBS

1 Corinthians 2 in the SBIBS2

1 Corinthians 2 in the SBICS

1 Corinthians 2 in the SBIDS

1 Corinthians 2 in the SBIGS

1 Corinthians 2 in the SBIHS

1 Corinthians 2 in the SBIIS

1 Corinthians 2 in the SBIIS2

1 Corinthians 2 in the SBIIS3

1 Corinthians 2 in the SBIKS

1 Corinthians 2 in the SBIKS2

1 Corinthians 2 in the SBIMS

1 Corinthians 2 in the SBIOS

1 Corinthians 2 in the SBIPS

1 Corinthians 2 in the SBISS

1 Corinthians 2 in the SBITS

1 Corinthians 2 in the SBITS2

1 Corinthians 2 in the SBITS3

1 Corinthians 2 in the SBITS4

1 Corinthians 2 in the SBIUS

1 Corinthians 2 in the SBIVS

1 Corinthians 2 in the SBT

1 Corinthians 2 in the SBT1E

1 Corinthians 2 in the SCHL

1 Corinthians 2 in the SNT

1 Corinthians 2 in the SUSU

1 Corinthians 2 in the SUSU2

1 Corinthians 2 in the SYNO

1 Corinthians 2 in the TBIAOTANT

1 Corinthians 2 in the TBT1E

1 Corinthians 2 in the TBT1E2

1 Corinthians 2 in the TFTIP

1 Corinthians 2 in the TFTU

1 Corinthians 2 in the TGNTATF3T

1 Corinthians 2 in the THAI

1 Corinthians 2 in the TNFD

1 Corinthians 2 in the TNT

1 Corinthians 2 in the TNTIK

1 Corinthians 2 in the TNTIL

1 Corinthians 2 in the TNTIN

1 Corinthians 2 in the TNTIP

1 Corinthians 2 in the TNTIZ

1 Corinthians 2 in the TOMA

1 Corinthians 2 in the TTENT

1 Corinthians 2 in the UBG

1 Corinthians 2 in the UGV

1 Corinthians 2 in the UGV2

1 Corinthians 2 in the UGV3

1 Corinthians 2 in the VBL

1 Corinthians 2 in the VDCC

1 Corinthians 2 in the YALU

1 Corinthians 2 in the YAPE

1 Corinthians 2 in the YBVTP

1 Corinthians 2 in the ZBP