1 Corinthians 3 (BOHCB)

1 ’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai. 2 Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba. 3 Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba? 4 Gama sa’ad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba? 5 Shin, wane ne Afollos? Wane ne kuma Bulus? Ai, bayi ne kawai waɗanda ta wurinsu kuka gaskata, kamar yadda Ubangiji ya ba kowannensu aikinsa. 6 Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi banruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma. 7 Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi banruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwa su yi girma. 8 Mutumin da ya yi shuki, da mutumin da ya yi banruwa nufinsu ɗaya ne, kuma kowannensu zai sami lada gwargwadon aikinsa. 9 Gama mu abokan aiki ne na Allah; ku kuwa gonar ce ta Allah, ginin Allah kuma. 10 Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yă lura da yadda yake gini. 11 Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi. 12 In wani ya yi gini a kan tushen ginin nan da zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja, itace, ciyawa ko kara, 13 aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za tă bayyana aikin, wutar kuwa za tă gwada ingancin aikin kowa. 14 In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada. 15 In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne. 16 Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku? 17 Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan. 18 Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”; 20 kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.” 21 Saboda haka, kada wani yă yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne, 22 ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba, ai, duka naku ne, 23 ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

In Other Versions

1 Corinthians 3 in the ANGEFD

1 Corinthians 3 in the ANTPNG2D

1 Corinthians 3 in the AS21

1 Corinthians 3 in the BAGH

1 Corinthians 3 in the BBPNG

1 Corinthians 3 in the BBT1E

1 Corinthians 3 in the BDS

1 Corinthians 3 in the BEV

1 Corinthians 3 in the BHAD

1 Corinthians 3 in the BIB

1 Corinthians 3 in the BLPT

1 Corinthians 3 in the BNT

1 Corinthians 3 in the BNTABOOT

1 Corinthians 3 in the BNTLV

1 Corinthians 3 in the BOATCB

1 Corinthians 3 in the BOATCB2

1 Corinthians 3 in the BOBCV

1 Corinthians 3 in the BOCNT

1 Corinthians 3 in the BOECS

1 Corinthians 3 in the BOGWICC

1 Corinthians 3 in the BOHCV

1 Corinthians 3 in the BOHLNT

1 Corinthians 3 in the BOHNTLTAL

1 Corinthians 3 in the BOICB

1 Corinthians 3 in the BOILNTAP

1 Corinthians 3 in the BOITCV

1 Corinthians 3 in the BOKCV

1 Corinthians 3 in the BOKCV2

1 Corinthians 3 in the BOKHWOG

1 Corinthians 3 in the BOKSSV

1 Corinthians 3 in the BOLCB

1 Corinthians 3 in the BOLCB2

1 Corinthians 3 in the BOMCV

1 Corinthians 3 in the BONAV

1 Corinthians 3 in the BONCB

1 Corinthians 3 in the BONLT

1 Corinthians 3 in the BONUT2

1 Corinthians 3 in the BOPLNT

1 Corinthians 3 in the BOSCB

1 Corinthians 3 in the BOSNC

1 Corinthians 3 in the BOTLNT

1 Corinthians 3 in the BOVCB

1 Corinthians 3 in the BOYCB

1 Corinthians 3 in the BPBB

1 Corinthians 3 in the BPH

1 Corinthians 3 in the BSB

1 Corinthians 3 in the CCB

1 Corinthians 3 in the CUV

1 Corinthians 3 in the CUVS

1 Corinthians 3 in the DBT

1 Corinthians 3 in the DGDNT

1 Corinthians 3 in the DHNT

1 Corinthians 3 in the DNT

1 Corinthians 3 in the ELBE

1 Corinthians 3 in the EMTV

1 Corinthians 3 in the ESV

1 Corinthians 3 in the FBV

1 Corinthians 3 in the FEB

1 Corinthians 3 in the GGMNT

1 Corinthians 3 in the GNT

1 Corinthians 3 in the HARY

1 Corinthians 3 in the HNT

1 Corinthians 3 in the IRVA

1 Corinthians 3 in the IRVB

1 Corinthians 3 in the IRVG

1 Corinthians 3 in the IRVH

1 Corinthians 3 in the IRVK

1 Corinthians 3 in the IRVM

1 Corinthians 3 in the IRVM2

1 Corinthians 3 in the IRVO

1 Corinthians 3 in the IRVP

1 Corinthians 3 in the IRVT

1 Corinthians 3 in the IRVT2

1 Corinthians 3 in the IRVU

1 Corinthians 3 in the ISVN

1 Corinthians 3 in the JSNT

1 Corinthians 3 in the KAPI

1 Corinthians 3 in the KBT1ETNIK

1 Corinthians 3 in the KBV

1 Corinthians 3 in the KJV

1 Corinthians 3 in the KNFD

1 Corinthians 3 in the LBA

1 Corinthians 3 in the LBLA

1 Corinthians 3 in the LNT

1 Corinthians 3 in the LSV

1 Corinthians 3 in the MAAL

1 Corinthians 3 in the MBV

1 Corinthians 3 in the MBV2

1 Corinthians 3 in the MHNT

1 Corinthians 3 in the MKNFD

1 Corinthians 3 in the MNG

1 Corinthians 3 in the MNT

1 Corinthians 3 in the MNT2

1 Corinthians 3 in the MRS1T

1 Corinthians 3 in the NAA

1 Corinthians 3 in the NASB

1 Corinthians 3 in the NBLA

1 Corinthians 3 in the NBS

1 Corinthians 3 in the NBVTP

1 Corinthians 3 in the NET2

1 Corinthians 3 in the NIV11

1 Corinthians 3 in the NNT

1 Corinthians 3 in the NNT2

1 Corinthians 3 in the NNT3

1 Corinthians 3 in the PDDPT

1 Corinthians 3 in the PFNT

1 Corinthians 3 in the RMNT

1 Corinthians 3 in the SBIAS

1 Corinthians 3 in the SBIBS

1 Corinthians 3 in the SBIBS2

1 Corinthians 3 in the SBICS

1 Corinthians 3 in the SBIDS

1 Corinthians 3 in the SBIGS

1 Corinthians 3 in the SBIHS

1 Corinthians 3 in the SBIIS

1 Corinthians 3 in the SBIIS2

1 Corinthians 3 in the SBIIS3

1 Corinthians 3 in the SBIKS

1 Corinthians 3 in the SBIKS2

1 Corinthians 3 in the SBIMS

1 Corinthians 3 in the SBIOS

1 Corinthians 3 in the SBIPS

1 Corinthians 3 in the SBISS

1 Corinthians 3 in the SBITS

1 Corinthians 3 in the SBITS2

1 Corinthians 3 in the SBITS3

1 Corinthians 3 in the SBITS4

1 Corinthians 3 in the SBIUS

1 Corinthians 3 in the SBIVS

1 Corinthians 3 in the SBT

1 Corinthians 3 in the SBT1E

1 Corinthians 3 in the SCHL

1 Corinthians 3 in the SNT

1 Corinthians 3 in the SUSU

1 Corinthians 3 in the SUSU2

1 Corinthians 3 in the SYNO

1 Corinthians 3 in the TBIAOTANT

1 Corinthians 3 in the TBT1E

1 Corinthians 3 in the TBT1E2

1 Corinthians 3 in the TFTIP

1 Corinthians 3 in the TFTU

1 Corinthians 3 in the TGNTATF3T

1 Corinthians 3 in the THAI

1 Corinthians 3 in the TNFD

1 Corinthians 3 in the TNT

1 Corinthians 3 in the TNTIK

1 Corinthians 3 in the TNTIL

1 Corinthians 3 in the TNTIN

1 Corinthians 3 in the TNTIP

1 Corinthians 3 in the TNTIZ

1 Corinthians 3 in the TOMA

1 Corinthians 3 in the TTENT

1 Corinthians 3 in the UBG

1 Corinthians 3 in the UGV

1 Corinthians 3 in the UGV2

1 Corinthians 3 in the UGV3

1 Corinthians 3 in the VBL

1 Corinthians 3 in the VDCC

1 Corinthians 3 in the YALU

1 Corinthians 3 in the YAPE

1 Corinthians 3 in the YBVTP

1 Corinthians 3 in the ZBP