1 Thessalonians 4 (BOHCB)
1 A ƙarshe, ’yan’uwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau. 2 Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu. 3 Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; 4 don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, 5 ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; 6 cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. 7 Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki. 8 Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki. 9 Yanzu kuwa game da ƙaunar ’yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna. 10 Gaskiyar kuwa ita ce, kuna ƙaunar dukan ’yan’uwa ko’ina a Makidoniya. Duk da haka muna ƙara gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku yi haka sau da sau. 11 Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku, 12 don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa. 13 ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14 Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. 15 Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16 Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17 Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. 18 Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.
In Other Versions
1 Thessalonians 4 in the ANGEFD
1 Thessalonians 4 in the ANTPNG2D
1 Thessalonians 4 in the BBPNG
1 Thessalonians 4 in the BBT1E
1 Thessalonians 4 in the BNTABOOT
1 Thessalonians 4 in the BNTLV
1 Thessalonians 4 in the BOATCB
1 Thessalonians 4 in the BOATCB2
1 Thessalonians 4 in the BOBCV
1 Thessalonians 4 in the BOCNT
1 Thessalonians 4 in the BOECS
1 Thessalonians 4 in the BOGWICC
1 Thessalonians 4 in the BOHCV
1 Thessalonians 4 in the BOHLNT
1 Thessalonians 4 in the BOHNTLTAL
1 Thessalonians 4 in the BOICB
1 Thessalonians 4 in the BOILNTAP
1 Thessalonians 4 in the BOITCV
1 Thessalonians 4 in the BOKCV
1 Thessalonians 4 in the BOKCV2
1 Thessalonians 4 in the BOKHWOG
1 Thessalonians 4 in the BOKSSV
1 Thessalonians 4 in the BOLCB
1 Thessalonians 4 in the BOLCB2
1 Thessalonians 4 in the BOMCV
1 Thessalonians 4 in the BONAV
1 Thessalonians 4 in the BONCB
1 Thessalonians 4 in the BONLT
1 Thessalonians 4 in the BONUT2
1 Thessalonians 4 in the BOPLNT
1 Thessalonians 4 in the BOSCB
1 Thessalonians 4 in the BOSNC
1 Thessalonians 4 in the BOTLNT
1 Thessalonians 4 in the BOVCB
1 Thessalonians 4 in the BOYCB
1 Thessalonians 4 in the DGDNT
1 Thessalonians 4 in the GGMNT
1 Thessalonians 4 in the IRVM2
1 Thessalonians 4 in the IRVT2
1 Thessalonians 4 in the KBT1ETNIK
1 Thessalonians 4 in the MKNFD
1 Thessalonians 4 in the MRS1T
1 Thessalonians 4 in the NBVTP
1 Thessalonians 4 in the NIV11
1 Thessalonians 4 in the PDDPT
1 Thessalonians 4 in the SBIAS
1 Thessalonians 4 in the SBIBS
1 Thessalonians 4 in the SBIBS2
1 Thessalonians 4 in the SBICS
1 Thessalonians 4 in the SBIDS
1 Thessalonians 4 in the SBIGS
1 Thessalonians 4 in the SBIHS
1 Thessalonians 4 in the SBIIS
1 Thessalonians 4 in the SBIIS2
1 Thessalonians 4 in the SBIIS3
1 Thessalonians 4 in the SBIKS
1 Thessalonians 4 in the SBIKS2
1 Thessalonians 4 in the SBIMS
1 Thessalonians 4 in the SBIOS
1 Thessalonians 4 in the SBIPS
1 Thessalonians 4 in the SBISS
1 Thessalonians 4 in the SBITS
1 Thessalonians 4 in the SBITS2
1 Thessalonians 4 in the SBITS3
1 Thessalonians 4 in the SBITS4
1 Thessalonians 4 in the SBIUS
1 Thessalonians 4 in the SBIVS
1 Thessalonians 4 in the SBT1E
1 Thessalonians 4 in the SUSU2
1 Thessalonians 4 in the TBIAOTANT
1 Thessalonians 4 in the TBT1E
1 Thessalonians 4 in the TBT1E2
1 Thessalonians 4 in the TFTIP
1 Thessalonians 4 in the TGNTATF3T
1 Thessalonians 4 in the TNTIK
1 Thessalonians 4 in the TNTIL
1 Thessalonians 4 in the TNTIN
1 Thessalonians 4 in the TNTIP
1 Thessalonians 4 in the TNTIZ
1 Thessalonians 4 in the TTENT