2 Corinthians 3 (BOHCB)

1 Yabon kanmu ne kuma muka fara yi? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi? 2 Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă santa, yă kuma karanta ta. 3 Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane. 4 Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah. 5 Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne. 6 Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai. 7 To, in hidimar da ta kawo mutuwa, wadda an rubuta a kan allon dutse, ta zo da ɗaukaka har Isra’ilawa suka kāsa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ko da yake mai shuɗewa ce, 8 ashe, hidimar Ruhu ba za tă fi wannan ɗaukaka ba? 9 In hidimar da take jawo wa mutane hukunci tana da ɗaukaka haka, to, lalle, hidimar da take kawo adalci za tă fi ta ɗaukaka nesa! 10 Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu. 11 In kuma aba mai shuɗewa ta zo da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwammame, lalle ne yă kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa! 12 Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan. 13 Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Isra’ilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa. 14 Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi. 15 Har yă zuwa yau, duk sa’ad da ake karatun littattafan Musa, lulluɓin nan yakan rufe zukatansu. 16 Amma duk sa’ad da wani ya juyo ga Ubangiji, akan kawar da lulluɓin. 17 Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ’yanci yake. 18 Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka.

In Other Versions

2 Corinthians 3 in the ANGEFD

2 Corinthians 3 in the ANTPNG2D

2 Corinthians 3 in the AS21

2 Corinthians 3 in the BAGH

2 Corinthians 3 in the BBPNG

2 Corinthians 3 in the BBT1E

2 Corinthians 3 in the BDS

2 Corinthians 3 in the BEV

2 Corinthians 3 in the BHAD

2 Corinthians 3 in the BIB

2 Corinthians 3 in the BLPT

2 Corinthians 3 in the BNT

2 Corinthians 3 in the BNTABOOT

2 Corinthians 3 in the BNTLV

2 Corinthians 3 in the BOATCB

2 Corinthians 3 in the BOATCB2

2 Corinthians 3 in the BOBCV

2 Corinthians 3 in the BOCNT

2 Corinthians 3 in the BOECS

2 Corinthians 3 in the BOGWICC

2 Corinthians 3 in the BOHCV

2 Corinthians 3 in the BOHLNT

2 Corinthians 3 in the BOHNTLTAL

2 Corinthians 3 in the BOICB

2 Corinthians 3 in the BOILNTAP

2 Corinthians 3 in the BOITCV

2 Corinthians 3 in the BOKCV

2 Corinthians 3 in the BOKCV2

2 Corinthians 3 in the BOKHWOG

2 Corinthians 3 in the BOKSSV

2 Corinthians 3 in the BOLCB

2 Corinthians 3 in the BOLCB2

2 Corinthians 3 in the BOMCV

2 Corinthians 3 in the BONAV

2 Corinthians 3 in the BONCB

2 Corinthians 3 in the BONLT

2 Corinthians 3 in the BONUT2

2 Corinthians 3 in the BOPLNT

2 Corinthians 3 in the BOSCB

2 Corinthians 3 in the BOSNC

2 Corinthians 3 in the BOTLNT

2 Corinthians 3 in the BOVCB

2 Corinthians 3 in the BOYCB

2 Corinthians 3 in the BPBB

2 Corinthians 3 in the BPH

2 Corinthians 3 in the BSB

2 Corinthians 3 in the CCB

2 Corinthians 3 in the CUV

2 Corinthians 3 in the CUVS

2 Corinthians 3 in the DBT

2 Corinthians 3 in the DGDNT

2 Corinthians 3 in the DHNT

2 Corinthians 3 in the DNT

2 Corinthians 3 in the ELBE

2 Corinthians 3 in the EMTV

2 Corinthians 3 in the ESV

2 Corinthians 3 in the FBV

2 Corinthians 3 in the FEB

2 Corinthians 3 in the GGMNT

2 Corinthians 3 in the GNT

2 Corinthians 3 in the HARY

2 Corinthians 3 in the HNT

2 Corinthians 3 in the IRVA

2 Corinthians 3 in the IRVB

2 Corinthians 3 in the IRVG

2 Corinthians 3 in the IRVH

2 Corinthians 3 in the IRVK

2 Corinthians 3 in the IRVM

2 Corinthians 3 in the IRVM2

2 Corinthians 3 in the IRVO

2 Corinthians 3 in the IRVP

2 Corinthians 3 in the IRVT

2 Corinthians 3 in the IRVT2

2 Corinthians 3 in the IRVU

2 Corinthians 3 in the ISVN

2 Corinthians 3 in the JSNT

2 Corinthians 3 in the KAPI

2 Corinthians 3 in the KBT1ETNIK

2 Corinthians 3 in the KBV

2 Corinthians 3 in the KJV

2 Corinthians 3 in the KNFD

2 Corinthians 3 in the LBA

2 Corinthians 3 in the LBLA

2 Corinthians 3 in the LNT

2 Corinthians 3 in the LSV

2 Corinthians 3 in the MAAL

2 Corinthians 3 in the MBV

2 Corinthians 3 in the MBV2

2 Corinthians 3 in the MHNT

2 Corinthians 3 in the MKNFD

2 Corinthians 3 in the MNG

2 Corinthians 3 in the MNT

2 Corinthians 3 in the MNT2

2 Corinthians 3 in the MRS1T

2 Corinthians 3 in the NAA

2 Corinthians 3 in the NASB

2 Corinthians 3 in the NBLA

2 Corinthians 3 in the NBS

2 Corinthians 3 in the NBVTP

2 Corinthians 3 in the NET2

2 Corinthians 3 in the NIV11

2 Corinthians 3 in the NNT

2 Corinthians 3 in the NNT2

2 Corinthians 3 in the NNT3

2 Corinthians 3 in the PDDPT

2 Corinthians 3 in the PFNT

2 Corinthians 3 in the RMNT

2 Corinthians 3 in the SBIAS

2 Corinthians 3 in the SBIBS

2 Corinthians 3 in the SBIBS2

2 Corinthians 3 in the SBICS

2 Corinthians 3 in the SBIDS

2 Corinthians 3 in the SBIGS

2 Corinthians 3 in the SBIHS

2 Corinthians 3 in the SBIIS

2 Corinthians 3 in the SBIIS2

2 Corinthians 3 in the SBIIS3

2 Corinthians 3 in the SBIKS

2 Corinthians 3 in the SBIKS2

2 Corinthians 3 in the SBIMS

2 Corinthians 3 in the SBIOS

2 Corinthians 3 in the SBIPS

2 Corinthians 3 in the SBISS

2 Corinthians 3 in the SBITS

2 Corinthians 3 in the SBITS2

2 Corinthians 3 in the SBITS3

2 Corinthians 3 in the SBITS4

2 Corinthians 3 in the SBIUS

2 Corinthians 3 in the SBIVS

2 Corinthians 3 in the SBT

2 Corinthians 3 in the SBT1E

2 Corinthians 3 in the SCHL

2 Corinthians 3 in the SNT

2 Corinthians 3 in the SUSU

2 Corinthians 3 in the SUSU2

2 Corinthians 3 in the SYNO

2 Corinthians 3 in the TBIAOTANT

2 Corinthians 3 in the TBT1E

2 Corinthians 3 in the TBT1E2

2 Corinthians 3 in the TFTIP

2 Corinthians 3 in the TFTU

2 Corinthians 3 in the TGNTATF3T

2 Corinthians 3 in the THAI

2 Corinthians 3 in the TNFD

2 Corinthians 3 in the TNT

2 Corinthians 3 in the TNTIK

2 Corinthians 3 in the TNTIL

2 Corinthians 3 in the TNTIN

2 Corinthians 3 in the TNTIP

2 Corinthians 3 in the TNTIZ

2 Corinthians 3 in the TOMA

2 Corinthians 3 in the TTENT

2 Corinthians 3 in the UBG

2 Corinthians 3 in the UGV

2 Corinthians 3 in the UGV2

2 Corinthians 3 in the UGV3

2 Corinthians 3 in the VBL

2 Corinthians 3 in the VDCC

2 Corinthians 3 in the YALU

2 Corinthians 3 in the YAPE

2 Corinthians 3 in the YBVTP

2 Corinthians 3 in the ZBP