2 Peter 2 (BOHCB)

1 Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. 2 Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya. 3 Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci. 4 Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci; 5 in har bai ƙyale duniya ta dā ba sa’ad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai wa’azin adalci, da kuma waɗansu bakwai; 6 in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah; 7 in kuwa har ya ceci Lot, mai adalci, wanda ya damu ainun da ƙazamar rayuwar mutane marasa bin doka; 8 (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci) 9 in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a. 10 Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki.Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama; 11 duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji. 12 Amma waɗannan mutane suna yin saɓo a kan abubuwan da ba su fahimta ba. Suna kama da dabbobi marasa hankali, halittun da suke bin abin da jikinsu ya faɗa musu kawai, waɗanda aka haifa don a kama a hallaka, kuma kamar dabbobi su ma za su hallaka. 13 Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku. 14 Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri! 15 Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta. 16 Amma an tsawata masa saboda laifinsa ta wurin jaki, dabbar da ba ta magana, wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin. 17 Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu. 18 Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure. 19 Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi. 20 In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko. 21 Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su. 22 A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”

In Other Versions

2 Peter 2 in the ANGEFD

2 Peter 2 in the ANTPNG2D

2 Peter 2 in the AS21

2 Peter 2 in the BAGH

2 Peter 2 in the BBPNG

2 Peter 2 in the BBT1E

2 Peter 2 in the BDS

2 Peter 2 in the BEV

2 Peter 2 in the BHAD

2 Peter 2 in the BIB

2 Peter 2 in the BLPT

2 Peter 2 in the BNT

2 Peter 2 in the BNTABOOT

2 Peter 2 in the BNTLV

2 Peter 2 in the BOATCB

2 Peter 2 in the BOATCB2

2 Peter 2 in the BOBCV

2 Peter 2 in the BOCNT

2 Peter 2 in the BOECS

2 Peter 2 in the BOGWICC

2 Peter 2 in the BOHCV

2 Peter 2 in the BOHLNT

2 Peter 2 in the BOHNTLTAL

2 Peter 2 in the BOICB

2 Peter 2 in the BOILNTAP

2 Peter 2 in the BOITCV

2 Peter 2 in the BOKCV

2 Peter 2 in the BOKCV2

2 Peter 2 in the BOKHWOG

2 Peter 2 in the BOKSSV

2 Peter 2 in the BOLCB

2 Peter 2 in the BOLCB2

2 Peter 2 in the BOMCV

2 Peter 2 in the BONAV

2 Peter 2 in the BONCB

2 Peter 2 in the BONLT

2 Peter 2 in the BONUT2

2 Peter 2 in the BOPLNT

2 Peter 2 in the BOSCB

2 Peter 2 in the BOSNC

2 Peter 2 in the BOTLNT

2 Peter 2 in the BOVCB

2 Peter 2 in the BOYCB

2 Peter 2 in the BPBB

2 Peter 2 in the BPH

2 Peter 2 in the BSB

2 Peter 2 in the CCB

2 Peter 2 in the CUV

2 Peter 2 in the CUVS

2 Peter 2 in the DBT

2 Peter 2 in the DGDNT

2 Peter 2 in the DHNT

2 Peter 2 in the DNT

2 Peter 2 in the ELBE

2 Peter 2 in the EMTV

2 Peter 2 in the ESV

2 Peter 2 in the FBV

2 Peter 2 in the FEB

2 Peter 2 in the GGMNT

2 Peter 2 in the GNT

2 Peter 2 in the HARY

2 Peter 2 in the HNT

2 Peter 2 in the IRVA

2 Peter 2 in the IRVB

2 Peter 2 in the IRVG

2 Peter 2 in the IRVH

2 Peter 2 in the IRVK

2 Peter 2 in the IRVM

2 Peter 2 in the IRVM2

2 Peter 2 in the IRVO

2 Peter 2 in the IRVP

2 Peter 2 in the IRVT

2 Peter 2 in the IRVT2

2 Peter 2 in the IRVU

2 Peter 2 in the ISVN

2 Peter 2 in the JSNT

2 Peter 2 in the KAPI

2 Peter 2 in the KBT1ETNIK

2 Peter 2 in the KBV

2 Peter 2 in the KJV

2 Peter 2 in the KNFD

2 Peter 2 in the LBA

2 Peter 2 in the LBLA

2 Peter 2 in the LNT

2 Peter 2 in the LSV

2 Peter 2 in the MAAL

2 Peter 2 in the MBV

2 Peter 2 in the MBV2

2 Peter 2 in the MHNT

2 Peter 2 in the MKNFD

2 Peter 2 in the MNG

2 Peter 2 in the MNT

2 Peter 2 in the MNT2

2 Peter 2 in the MRS1T

2 Peter 2 in the NAA

2 Peter 2 in the NASB

2 Peter 2 in the NBLA

2 Peter 2 in the NBS

2 Peter 2 in the NBVTP

2 Peter 2 in the NET2

2 Peter 2 in the NIV11

2 Peter 2 in the NNT

2 Peter 2 in the NNT2

2 Peter 2 in the NNT3

2 Peter 2 in the PDDPT

2 Peter 2 in the PFNT

2 Peter 2 in the RMNT

2 Peter 2 in the SBIAS

2 Peter 2 in the SBIBS

2 Peter 2 in the SBIBS2

2 Peter 2 in the SBICS

2 Peter 2 in the SBIDS

2 Peter 2 in the SBIGS

2 Peter 2 in the SBIHS

2 Peter 2 in the SBIIS

2 Peter 2 in the SBIIS2

2 Peter 2 in the SBIIS3

2 Peter 2 in the SBIKS

2 Peter 2 in the SBIKS2

2 Peter 2 in the SBIMS

2 Peter 2 in the SBIOS

2 Peter 2 in the SBIPS

2 Peter 2 in the SBISS

2 Peter 2 in the SBITS

2 Peter 2 in the SBITS2

2 Peter 2 in the SBITS3

2 Peter 2 in the SBITS4

2 Peter 2 in the SBIUS

2 Peter 2 in the SBIVS

2 Peter 2 in the SBT

2 Peter 2 in the SBT1E

2 Peter 2 in the SCHL

2 Peter 2 in the SNT

2 Peter 2 in the SUSU

2 Peter 2 in the SUSU2

2 Peter 2 in the SYNO

2 Peter 2 in the TBIAOTANT

2 Peter 2 in the TBT1E

2 Peter 2 in the TBT1E2

2 Peter 2 in the TFTIP

2 Peter 2 in the TFTU

2 Peter 2 in the TGNTATF3T

2 Peter 2 in the THAI

2 Peter 2 in the TNFD

2 Peter 2 in the TNT

2 Peter 2 in the TNTIK

2 Peter 2 in the TNTIL

2 Peter 2 in the TNTIN

2 Peter 2 in the TNTIP

2 Peter 2 in the TNTIZ

2 Peter 2 in the TOMA

2 Peter 2 in the TTENT

2 Peter 2 in the UBG

2 Peter 2 in the UGV

2 Peter 2 in the UGV2

2 Peter 2 in the UGV3

2 Peter 2 in the VBL

2 Peter 2 in the VDCC

2 Peter 2 in the YALU

2 Peter 2 in the YAPE

2 Peter 2 in the YBVTP

2 Peter 2 in the ZBP