Acts 10 (BOHCB)

1 A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya. 2 Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa. 3 Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!” 4 Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?”Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah. 5 Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus. 6 Yana zama tare da Siman, mai aikin fatu, wanda gidansa ke bakin teku.” 7 Sa’ad da mala’ikan da ya yi masa magana ya tafi, sai Korneliyus ya kira biyu daga cikin bayinsa da kuma wani soja mai ibada wanda yake ɗaya a cikin masu yin masa hidima. 8 Ya fada musu duk abin da ya faru sa’an nan ya aike su Yoffa. 9 Wajen tsakar rana kashegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yă yi addu’a. 10 Yunwa ta kama shi ya kuwa so yă ci wani abu, yayinda ake shirya abinci, sai wahayi ya zo masa. 11 Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu. 12 Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu ja da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama. 13 Sa’an nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.” 14 Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.” 15 Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.” 16 Wannan ya faru har sau uku, sai nan da nan aka ɗauke mayafin zuwa sama. 17 Tun Bitrus yana cikin tunani game da ma’anar wahayin nan, sai ga mutanen da Korneliyus ya aika sun sami gidan Siman suna kuma tsaye a ƙofar. 18 Suka yi sallama, suna tambaya ko Siman wanda aka sani da suna Bitrus yana zama a can. 19 Yayinda Bitrus yana cikin tunani game da wahayin, sai Ruhu ya ce masa, “Siman, ga mutum uku suna nemanka. 20 Saboda haka ka tashi ka sauka. Kada ka yi wata-wata, gama ni ne na aiko su.” 21 Sai Bitrus ya sauka ya ce wa mutanen, “Ni ne kuke nema. Me ya kawo ku?” 22 Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani mala’ika mai tsarki ya faɗa masa, yă sa ka zo gidansa don yă ji abin da za ka faɗa.” 23 Sai Bitrus ya gayyaci mutanen cikin gida su zama baƙinsa.Kashegari Bitrus ya tafi tare da su, waɗansu ’yan’uwa daga Yoffa kuwa suka tafi tare da shi. 24 Kashegari sai ya iso Kaisariya. Korneliyus kuwa yana nan yana jiransu, ya kuma gayyaci ’yan’uwansa da abokansa na kusa. 25 Da Bitrus ya shiga gidan, Korneliyus ya sadu da shi ya kuma fāɗi a gabansa cikin bangirma. 26 Amma Bitrus ya sa shi ya tashi. Ya ce, “Tashi, ni mutum ne kawai.” 27 Yana magana da shi, sai Bitrus ya shiga ciki ya kuma tarar da taron mutane da yawa. 28 Sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san cewa dokarmu ta hana mutumin Yahuda yin cuɗanya, ko ya ziyarci Ba’al’umme. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in kira wani mutum marar tsarki ko marar tsabta. 29 Don haka sa’ad da aka aika in zo, na zo ba wata faɗa. To, ko zan san abin da ya sa ka aika in zo?” 30 Korneliyus ya amsa ya ce, “Kwana huɗu da suka wuce ina a gidana ina addu’a a wannan lokaci, wajen ƙarfe uku na yamma. Ba zato ba tsammani sai ga wani mutum cikin tufafi masu walƙiya ya tsaya a gabana 31 ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji addu’arka, ya kuma tuna da kyautanka ga matalauta. 32 Ka aika zuwa Yoffa don a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. Shi baƙo ne a gidan Siman mai aikin fatu, wanda yake zama a bakin teku.’ 33 Saboda haka na aika a zo da kai nan da nan, ya kuma yi kyau da ka zo. To ga mu duka a nan a gaban Allah don mu saurari dukan abin da Ubangiji ya umarce ka ka faɗa mana.” 34 Sa’an nan Bitrus ya fara magana ya ce, “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai 35 amma yana karɓan mutane daga kowace al’ummar da take tsoronsa suke kuma aikata abin da yake daidai. 36 Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa. 37 Kun san abin da ya faru a dukan Yahudiya, farawa daga Galili bayan baftismar da Yohanna ya yi wa’azi, 38 yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi. 39 “Mu kuwa shaidu ne na dukan abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da kuma a Urushalima. Suka kashe shi ta wurin rataye shi a kan itace, 40 amma Allah ya tashe shi daga matattu a rana ta uku, ya sa kuma aka gan shi. 41 Ba dukan mutane ne suka gan shi ba, amma ta wurin shaidun da Allah ya riga ya zaɓa, ta wurinmu da muka ci muka kuma sha tare da shi bayan tashinsa daga matattu. 42 Ya umarce mu mu yi wa’azi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yă zama mai shari’a na masu rai da na matattu. 43 Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.” 44 Tun Bitrus yana cikin faɗin waɗannan kalmomi, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka wa duk waɗanda suka ji saƙon. 45 Masu bin da suke da kaciya waɗanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki cewa an ba da kyautar Ruhu Mai Tsarki har ma a kan Al’ummai. 46 Gama sun ji su suna magana da waɗansu harsuna suna kuma yabon Allah.Sai Bitrus ya ce, 47 “Wani zai iya hana a yi wa waɗannan mutane baftisma da ruwa? Sun karɓi Ruhu Mai Tsarki kamar yadda muka karɓa.” 48 Saboda haka ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Kiristi. Sa’an nan suka roƙi Bitrus yă zauna da su na ’yan kwanaki.

In Other Versions

Acts 10 in the ANGEFD

Acts 10 in the ANTPNG2D

Acts 10 in the AS21

Acts 10 in the BAGH

Acts 10 in the BBPNG

Acts 10 in the BBT1E

Acts 10 in the BDS

Acts 10 in the BEV

Acts 10 in the BHAD

Acts 10 in the BIB

Acts 10 in the BLPT

Acts 10 in the BNT

Acts 10 in the BNTABOOT

Acts 10 in the BNTLV

Acts 10 in the BOATCB

Acts 10 in the BOATCB2

Acts 10 in the BOBCV

Acts 10 in the BOCNT

Acts 10 in the BOECS

Acts 10 in the BOGWICC

Acts 10 in the BOHCV

Acts 10 in the BOHLNT

Acts 10 in the BOHNTLTAL

Acts 10 in the BOICB

Acts 10 in the BOILNTAP

Acts 10 in the BOITCV

Acts 10 in the BOKCV

Acts 10 in the BOKCV2

Acts 10 in the BOKHWOG

Acts 10 in the BOKSSV

Acts 10 in the BOLCB

Acts 10 in the BOLCB2

Acts 10 in the BOMCV

Acts 10 in the BONAV

Acts 10 in the BONCB

Acts 10 in the BONLT

Acts 10 in the BONUT2

Acts 10 in the BOPLNT

Acts 10 in the BOSCB

Acts 10 in the BOSNC

Acts 10 in the BOTLNT

Acts 10 in the BOVCB

Acts 10 in the BOYCB

Acts 10 in the BPBB

Acts 10 in the BPH

Acts 10 in the BSB

Acts 10 in the CCB

Acts 10 in the CUV

Acts 10 in the CUVS

Acts 10 in the DBT

Acts 10 in the DGDNT

Acts 10 in the DHNT

Acts 10 in the DNT

Acts 10 in the ELBE

Acts 10 in the EMTV

Acts 10 in the ESV

Acts 10 in the FBV

Acts 10 in the FEB

Acts 10 in the GGMNT

Acts 10 in the GNT

Acts 10 in the HARY

Acts 10 in the HNT

Acts 10 in the IRVA

Acts 10 in the IRVB

Acts 10 in the IRVG

Acts 10 in the IRVH

Acts 10 in the IRVK

Acts 10 in the IRVM

Acts 10 in the IRVM2

Acts 10 in the IRVO

Acts 10 in the IRVP

Acts 10 in the IRVT

Acts 10 in the IRVT2

Acts 10 in the IRVU

Acts 10 in the ISVN

Acts 10 in the JSNT

Acts 10 in the KAPI

Acts 10 in the KBT1ETNIK

Acts 10 in the KBV

Acts 10 in the KJV

Acts 10 in the KNFD

Acts 10 in the LBA

Acts 10 in the LBLA

Acts 10 in the LNT

Acts 10 in the LSV

Acts 10 in the MAAL

Acts 10 in the MBV

Acts 10 in the MBV2

Acts 10 in the MHNT

Acts 10 in the MKNFD

Acts 10 in the MNG

Acts 10 in the MNT

Acts 10 in the MNT2

Acts 10 in the MRS1T

Acts 10 in the NAA

Acts 10 in the NASB

Acts 10 in the NBLA

Acts 10 in the NBS

Acts 10 in the NBVTP

Acts 10 in the NET2

Acts 10 in the NIV11

Acts 10 in the NNT

Acts 10 in the NNT2

Acts 10 in the NNT3

Acts 10 in the PDDPT

Acts 10 in the PFNT

Acts 10 in the RMNT

Acts 10 in the SBIAS

Acts 10 in the SBIBS

Acts 10 in the SBIBS2

Acts 10 in the SBICS

Acts 10 in the SBIDS

Acts 10 in the SBIGS

Acts 10 in the SBIHS

Acts 10 in the SBIIS

Acts 10 in the SBIIS2

Acts 10 in the SBIIS3

Acts 10 in the SBIKS

Acts 10 in the SBIKS2

Acts 10 in the SBIMS

Acts 10 in the SBIOS

Acts 10 in the SBIPS

Acts 10 in the SBISS

Acts 10 in the SBITS

Acts 10 in the SBITS2

Acts 10 in the SBITS3

Acts 10 in the SBITS4

Acts 10 in the SBIUS

Acts 10 in the SBIVS

Acts 10 in the SBT

Acts 10 in the SBT1E

Acts 10 in the SCHL

Acts 10 in the SNT

Acts 10 in the SUSU

Acts 10 in the SUSU2

Acts 10 in the SYNO

Acts 10 in the TBIAOTANT

Acts 10 in the TBT1E

Acts 10 in the TBT1E2

Acts 10 in the TFTIP

Acts 10 in the TFTU

Acts 10 in the TGNTATF3T

Acts 10 in the THAI

Acts 10 in the TNFD

Acts 10 in the TNT

Acts 10 in the TNTIK

Acts 10 in the TNTIL

Acts 10 in the TNTIN

Acts 10 in the TNTIP

Acts 10 in the TNTIZ

Acts 10 in the TOMA

Acts 10 in the TTENT

Acts 10 in the UBG

Acts 10 in the UGV

Acts 10 in the UGV2

Acts 10 in the UGV3

Acts 10 in the VBL

Acts 10 in the VDCC

Acts 10 in the YALU

Acts 10 in the YAPE

Acts 10 in the YBVTP

Acts 10 in the ZBP