Acts 17 (BOHCB)

1 Da suka bi ta Amfifolis da Afolloniya, sai suka isa Tessalonika, inda akwai majami’ar Yahudawa. 2 Kamar yadda ya saba, Bulus ya shiga majami’ar, ranakun Asabbaci uku ya yi ta yin muhawwara da su daga cikin Nassosi, 3 yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesu da nake sanar muku shi ne Kiristi.” 4 Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Hellenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba. 5 Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ’yan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka tā da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron. 6 Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ’yan’uwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa, “Waɗannan mutanen da suke tā da fitina ko’ina a duniya sun iso nan, 7 Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.” 8 Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi. 9 Sai suka sa Yason da sauran su biya kuɗin saki sa’an nan suka sallame su. 10 Da dare ya yi, sai ’yan’uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Bereya. Da suka isa can, sai suka shiga majami’ar Yahudawa. 11 Bereyawa kuwa sun fi Tessalonikawa hankali, gama sun karɓi saƙon da marmari ƙwarai, suka kuma yi ta yin bincike Nassosi kowace rana su ga ko abin da Bulus ya faɗa gaskiya ne. 12 Yahudawa da yawa suka gaskata, haka ma waɗansu manyan matan Hellenawa da kuma mazan Hellenawa da yawa. 13 Da Yahudawan da suke a Tessalonika suka ji cewa Bulus yana wa’azin maganar Allah a Bereya, sai suka je can ma, suna zuga taro suna kuma tā da hankalinsu. 14 Nan da nan ’yan’uwa suka sa Bulus yă tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka dakata a Bereya. 15 Mutanen da suka raka Bulus kuwa suka kawo shi Atens sa’an nan suka dawo da umarnai wa Sila da Timoti cewa su zo wurinsa da gaggawa. 16 Yayinda Bulus yake jiransu a Atens, ya damu ƙwarai da ya ga birnin cike da gumaka. 17 Saboda haka ya yi ta muhawwara a majami’a da Yahudawa da kuma Hellenawa masu tsoron Allah, haka kuma da waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa. 18 Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana wa’azin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana wa’azin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu. 19 Sai suka ɗauke shi suka kawo shi wurin taron Areyofagus, inda suka ce masa, “Ko za mu san mene ne sabon koyarwan nan ya ƙunsa da kake yi? 20 Kana kawo mana ra’ayoyin da suke baƙo a gare mu, kuma muna so mu san mene ne suke nufi.” 21 (Duk Atenawa da baƙin da suke zama a can suna zaman kashe wando ne kawai kuma ba abin da suke yi sai dai taɗi da kuma jin sababbin ra’ayoyi.) 22 Sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyar taron Areyofagus ya ce, “Ya ku mutanen Atens! Na dai lura cewa ta kowace hanya ku masu addini ne ƙwarai. 23 Gama sa’ad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu,Ga Allahn da ba a sani ba.To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku. 24 “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. 25 Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. 26 Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. 27 Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. 28 ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’ 29 “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa. 30 A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba. 31 Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.” 32 Sa’ad da suka ji maganar tashin matattu, waɗansunsu suka yi tsaki, amma waɗansu suka ce, “Muna so mu ƙara jin ka a kan wannan batu.” 33 Da wannan, Bulus ya bar Majalisar. 34 Waɗansu mutane kima suka zama mabiyan Bulus suka kuwa gaskata. A cikinsu kuwa akwai Diyonasiyus ɗan Majalisar Areyofagus, haka kuma wata mace mai suna Damaris, da waɗansu dai haka.

In Other Versions

Acts 17 in the ANGEFD

Acts 17 in the ANTPNG2D

Acts 17 in the AS21

Acts 17 in the BAGH

Acts 17 in the BBPNG

Acts 17 in the BBT1E

Acts 17 in the BDS

Acts 17 in the BEV

Acts 17 in the BHAD

Acts 17 in the BIB

Acts 17 in the BLPT

Acts 17 in the BNT

Acts 17 in the BNTABOOT

Acts 17 in the BNTLV

Acts 17 in the BOATCB

Acts 17 in the BOATCB2

Acts 17 in the BOBCV

Acts 17 in the BOCNT

Acts 17 in the BOECS

Acts 17 in the BOGWICC

Acts 17 in the BOHCV

Acts 17 in the BOHLNT

Acts 17 in the BOHNTLTAL

Acts 17 in the BOICB

Acts 17 in the BOILNTAP

Acts 17 in the BOITCV

Acts 17 in the BOKCV

Acts 17 in the BOKCV2

Acts 17 in the BOKHWOG

Acts 17 in the BOKSSV

Acts 17 in the BOLCB

Acts 17 in the BOLCB2

Acts 17 in the BOMCV

Acts 17 in the BONAV

Acts 17 in the BONCB

Acts 17 in the BONLT

Acts 17 in the BONUT2

Acts 17 in the BOPLNT

Acts 17 in the BOSCB

Acts 17 in the BOSNC

Acts 17 in the BOTLNT

Acts 17 in the BOVCB

Acts 17 in the BOYCB

Acts 17 in the BPBB

Acts 17 in the BPH

Acts 17 in the BSB

Acts 17 in the CCB

Acts 17 in the CUV

Acts 17 in the CUVS

Acts 17 in the DBT

Acts 17 in the DGDNT

Acts 17 in the DHNT

Acts 17 in the DNT

Acts 17 in the ELBE

Acts 17 in the EMTV

Acts 17 in the ESV

Acts 17 in the FBV

Acts 17 in the FEB

Acts 17 in the GGMNT

Acts 17 in the GNT

Acts 17 in the HARY

Acts 17 in the HNT

Acts 17 in the IRVA

Acts 17 in the IRVB

Acts 17 in the IRVG

Acts 17 in the IRVH

Acts 17 in the IRVK

Acts 17 in the IRVM

Acts 17 in the IRVM2

Acts 17 in the IRVO

Acts 17 in the IRVP

Acts 17 in the IRVT

Acts 17 in the IRVT2

Acts 17 in the IRVU

Acts 17 in the ISVN

Acts 17 in the JSNT

Acts 17 in the KAPI

Acts 17 in the KBT1ETNIK

Acts 17 in the KBV

Acts 17 in the KJV

Acts 17 in the KNFD

Acts 17 in the LBA

Acts 17 in the LBLA

Acts 17 in the LNT

Acts 17 in the LSV

Acts 17 in the MAAL

Acts 17 in the MBV

Acts 17 in the MBV2

Acts 17 in the MHNT

Acts 17 in the MKNFD

Acts 17 in the MNG

Acts 17 in the MNT

Acts 17 in the MNT2

Acts 17 in the MRS1T

Acts 17 in the NAA

Acts 17 in the NASB

Acts 17 in the NBLA

Acts 17 in the NBS

Acts 17 in the NBVTP

Acts 17 in the NET2

Acts 17 in the NIV11

Acts 17 in the NNT

Acts 17 in the NNT2

Acts 17 in the NNT3

Acts 17 in the PDDPT

Acts 17 in the PFNT

Acts 17 in the RMNT

Acts 17 in the SBIAS

Acts 17 in the SBIBS

Acts 17 in the SBIBS2

Acts 17 in the SBICS

Acts 17 in the SBIDS

Acts 17 in the SBIGS

Acts 17 in the SBIHS

Acts 17 in the SBIIS

Acts 17 in the SBIIS2

Acts 17 in the SBIIS3

Acts 17 in the SBIKS

Acts 17 in the SBIKS2

Acts 17 in the SBIMS

Acts 17 in the SBIOS

Acts 17 in the SBIPS

Acts 17 in the SBISS

Acts 17 in the SBITS

Acts 17 in the SBITS2

Acts 17 in the SBITS3

Acts 17 in the SBITS4

Acts 17 in the SBIUS

Acts 17 in the SBIVS

Acts 17 in the SBT

Acts 17 in the SBT1E

Acts 17 in the SCHL

Acts 17 in the SNT

Acts 17 in the SUSU

Acts 17 in the SUSU2

Acts 17 in the SYNO

Acts 17 in the TBIAOTANT

Acts 17 in the TBT1E

Acts 17 in the TBT1E2

Acts 17 in the TFTIP

Acts 17 in the TFTU

Acts 17 in the TGNTATF3T

Acts 17 in the THAI

Acts 17 in the TNFD

Acts 17 in the TNT

Acts 17 in the TNTIK

Acts 17 in the TNTIL

Acts 17 in the TNTIN

Acts 17 in the TNTIP

Acts 17 in the TNTIZ

Acts 17 in the TOMA

Acts 17 in the TTENT

Acts 17 in the UBG

Acts 17 in the UGV

Acts 17 in the UGV2

Acts 17 in the UGV3

Acts 17 in the VBL

Acts 17 in the VDCC

Acts 17 in the YALU

Acts 17 in the YAPE

Acts 17 in the YBVTP

Acts 17 in the ZBP