Ephesians 1 (BOHCB)

1 Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da kuma suke amintattu cikin Kiristi Yesu. 2 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne. 7 A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8 wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. 9 Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. 10 Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa. 11 A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi. 12 Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah. 13 An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. 14 Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne. 15 Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah, 16 ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17 Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18 Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. 19 Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan 20 da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. 21 Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. 22 Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya. 23 Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.

In Other Versions

Ephesians 1 in the ANGEFD

Ephesians 1 in the ANTPNG2D

Ephesians 1 in the AS21

Ephesians 1 in the BAGH

Ephesians 1 in the BBPNG

Ephesians 1 in the BBT1E

Ephesians 1 in the BDS

Ephesians 1 in the BEV

Ephesians 1 in the BHAD

Ephesians 1 in the BIB

Ephesians 1 in the BLPT

Ephesians 1 in the BNT

Ephesians 1 in the BNTABOOT

Ephesians 1 in the BNTLV

Ephesians 1 in the BOATCB

Ephesians 1 in the BOATCB2

Ephesians 1 in the BOBCV

Ephesians 1 in the BOCNT

Ephesians 1 in the BOECS

Ephesians 1 in the BOGWICC

Ephesians 1 in the BOHCV

Ephesians 1 in the BOHLNT

Ephesians 1 in the BOHNTLTAL

Ephesians 1 in the BOICB

Ephesians 1 in the BOILNTAP

Ephesians 1 in the BOITCV

Ephesians 1 in the BOKCV

Ephesians 1 in the BOKCV2

Ephesians 1 in the BOKHWOG

Ephesians 1 in the BOKSSV

Ephesians 1 in the BOLCB

Ephesians 1 in the BOLCB2

Ephesians 1 in the BOMCV

Ephesians 1 in the BONAV

Ephesians 1 in the BONCB

Ephesians 1 in the BONLT

Ephesians 1 in the BONUT2

Ephesians 1 in the BOPLNT

Ephesians 1 in the BOSCB

Ephesians 1 in the BOSNC

Ephesians 1 in the BOTLNT

Ephesians 1 in the BOVCB

Ephesians 1 in the BOYCB

Ephesians 1 in the BPBB

Ephesians 1 in the BPH

Ephesians 1 in the BSB

Ephesians 1 in the CCB

Ephesians 1 in the CUV

Ephesians 1 in the CUVS

Ephesians 1 in the DBT

Ephesians 1 in the DGDNT

Ephesians 1 in the DHNT

Ephesians 1 in the DNT

Ephesians 1 in the ELBE

Ephesians 1 in the EMTV

Ephesians 1 in the ESV

Ephesians 1 in the FBV

Ephesians 1 in the FEB

Ephesians 1 in the GGMNT

Ephesians 1 in the GNT

Ephesians 1 in the HARY

Ephesians 1 in the HNT

Ephesians 1 in the IRVA

Ephesians 1 in the IRVB

Ephesians 1 in the IRVG

Ephesians 1 in the IRVH

Ephesians 1 in the IRVK

Ephesians 1 in the IRVM

Ephesians 1 in the IRVM2

Ephesians 1 in the IRVO

Ephesians 1 in the IRVP

Ephesians 1 in the IRVT

Ephesians 1 in the IRVT2

Ephesians 1 in the IRVU

Ephesians 1 in the ISVN

Ephesians 1 in the JSNT

Ephesians 1 in the KAPI

Ephesians 1 in the KBT1ETNIK

Ephesians 1 in the KBV

Ephesians 1 in the KJV

Ephesians 1 in the KNFD

Ephesians 1 in the LBA

Ephesians 1 in the LBLA

Ephesians 1 in the LNT

Ephesians 1 in the LSV

Ephesians 1 in the MAAL

Ephesians 1 in the MBV

Ephesians 1 in the MBV2

Ephesians 1 in the MHNT

Ephesians 1 in the MKNFD

Ephesians 1 in the MNG

Ephesians 1 in the MNT

Ephesians 1 in the MNT2

Ephesians 1 in the MRS1T

Ephesians 1 in the NAA

Ephesians 1 in the NASB

Ephesians 1 in the NBLA

Ephesians 1 in the NBS

Ephesians 1 in the NBVTP

Ephesians 1 in the NET2

Ephesians 1 in the NIV11

Ephesians 1 in the NNT

Ephesians 1 in the NNT2

Ephesians 1 in the NNT3

Ephesians 1 in the PDDPT

Ephesians 1 in the PFNT

Ephesians 1 in the RMNT

Ephesians 1 in the SBIAS

Ephesians 1 in the SBIBS

Ephesians 1 in the SBIBS2

Ephesians 1 in the SBICS

Ephesians 1 in the SBIDS

Ephesians 1 in the SBIGS

Ephesians 1 in the SBIHS

Ephesians 1 in the SBIIS

Ephesians 1 in the SBIIS2

Ephesians 1 in the SBIIS3

Ephesians 1 in the SBIKS

Ephesians 1 in the SBIKS2

Ephesians 1 in the SBIMS

Ephesians 1 in the SBIOS

Ephesians 1 in the SBIPS

Ephesians 1 in the SBISS

Ephesians 1 in the SBITS

Ephesians 1 in the SBITS2

Ephesians 1 in the SBITS3

Ephesians 1 in the SBITS4

Ephesians 1 in the SBIUS

Ephesians 1 in the SBIVS

Ephesians 1 in the SBT

Ephesians 1 in the SBT1E

Ephesians 1 in the SCHL

Ephesians 1 in the SNT

Ephesians 1 in the SUSU

Ephesians 1 in the SUSU2

Ephesians 1 in the SYNO

Ephesians 1 in the TBIAOTANT

Ephesians 1 in the TBT1E

Ephesians 1 in the TBT1E2

Ephesians 1 in the TFTIP

Ephesians 1 in the TFTU

Ephesians 1 in the TGNTATF3T

Ephesians 1 in the THAI

Ephesians 1 in the TNFD

Ephesians 1 in the TNT

Ephesians 1 in the TNTIK

Ephesians 1 in the TNTIL

Ephesians 1 in the TNTIN

Ephesians 1 in the TNTIP

Ephesians 1 in the TNTIZ

Ephesians 1 in the TOMA

Ephesians 1 in the TTENT

Ephesians 1 in the UBG

Ephesians 1 in the UGV

Ephesians 1 in the UGV2

Ephesians 1 in the UGV3

Ephesians 1 in the VBL

Ephesians 1 in the VDCC

Ephesians 1 in the YALU

Ephesians 1 in the YAPE

Ephesians 1 in the YBVTP

Ephesians 1 in the ZBP