Galatians 1 (BOHCB)
1 Bulus manzo, aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da kuma Allah Uba, wanda ya tā da Yesu daga matattu. 2 Dukan ’yan’uwan kuma da suke tare da ni a nan, Suna gai da ikkilisiyoyi a Galatiya. 3 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. 4 Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu, 5 a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin. 6 Ina mamaki yadda kuka yi saurin yashe wanda ya kira ku ta wurin alherin Kiristi, kuna juyewa ga wata bishara dabam 7 wadda a gaskiya ba bishara ba ce ko kaɗan. Tabbatacce waɗansu mutane suna birkitar da ku, suna kuma ƙoƙari su karkatar da bisharar Kiristi. 8 Amma ko mu, ko mala’ika daga sama ya yi wa’azin wata bishara dabam da wadda muka yi muku, bari yă zama la’ananne har abada! 9 Kamar yadda muka riga muka faɗa, haka yanzu ma ina ƙara cewa in wani yana muku wa’azin wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, bari yă zama la’ananne har abada! 10 Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba. 11 Ina so ku sani ’yan’uwa, cewa bisharar da nake wa’azi, ba mutum ne ya ƙago ta ba. 12 Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne. 13 Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta. 14 Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin al’adun kakannina. 15 Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi 16 yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba. 17 Ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na hanzarta na tafi ƙasar Arabiya, daga baya sai na koma Damaskus. 18 Bayan shekara uku, sai na haura zuwa Urushalima domin in sadu da Bitrus, na kuwa zauna tare da shi kwana goma sha biyar. 19 Ban ga wani a ciki sauran manzanni ba, sai dai Yaƙub ɗan’uwan Ubangiji. 20 Ina tabbatar muku a gaban Allah cewa abin da nake rubuta muku ba ƙarya ba ne. 21 Daga baya sai na tafi Suriya da Silisiya. 22 Ikkilisiyoyin da suke cikin Kiristi da suke a Yahudiya ba su san ni ba tukuna. 23 Sun dai sami labari ne kawai cewa, “Mutumin da dā yake tsananta mana yanzu yana wa’azin bangaskiyar da dā ya yi ƙoƙari yă hallaka.” 24 Sai suka yabi Allah saboda ni.
In Other Versions
Galatians 1 in the ANGEFD
Galatians 1 in the ANTPNG2D
Galatians 1 in the AS21
Galatians 1 in the BAGH
Galatians 1 in the BBPNG
Galatians 1 in the BBT1E
Galatians 1 in the BDS
Galatians 1 in the BEV
Galatians 1 in the BHAD
Galatians 1 in the BIB
Galatians 1 in the BLPT
Galatians 1 in the BNT
Galatians 1 in the BNTABOOT
Galatians 1 in the BNTLV
Galatians 1 in the BOATCB
Galatians 1 in the BOATCB2
Galatians 1 in the BOBCV
Galatians 1 in the BOCNT
Galatians 1 in the BOECS
Galatians 1 in the BOGWICC
Galatians 1 in the BOHCV
Galatians 1 in the BOHLNT
Galatians 1 in the BOHNTLTAL
Galatians 1 in the BOICB
Galatians 1 in the BOILNTAP
Galatians 1 in the BOITCV
Galatians 1 in the BOKCV
Galatians 1 in the BOKCV2
Galatians 1 in the BOKHWOG
Galatians 1 in the BOKSSV
Galatians 1 in the BOLCB
Galatians 1 in the BOLCB2
Galatians 1 in the BOMCV
Galatians 1 in the BONAV
Galatians 1 in the BONCB
Galatians 1 in the BONLT
Galatians 1 in the BONUT2
Galatians 1 in the BOPLNT
Galatians 1 in the BOSCB
Galatians 1 in the BOSNC
Galatians 1 in the BOTLNT
Galatians 1 in the BOVCB
Galatians 1 in the BOYCB
Galatians 1 in the BPBB
Galatians 1 in the BPH
Galatians 1 in the BSB
Galatians 1 in the CCB
Galatians 1 in the CUV
Galatians 1 in the CUVS
Galatians 1 in the DBT
Galatians 1 in the DGDNT
Galatians 1 in the DHNT
Galatians 1 in the DNT
Galatians 1 in the ELBE
Galatians 1 in the EMTV
Galatians 1 in the ESV
Galatians 1 in the FBV
Galatians 1 in the FEB
Galatians 1 in the GGMNT
Galatians 1 in the GNT
Galatians 1 in the HARY
Galatians 1 in the HNT
Galatians 1 in the IRVA
Galatians 1 in the IRVB
Galatians 1 in the IRVG
Galatians 1 in the IRVH
Galatians 1 in the IRVK
Galatians 1 in the IRVM
Galatians 1 in the IRVM2
Galatians 1 in the IRVO
Galatians 1 in the IRVP
Galatians 1 in the IRVT
Galatians 1 in the IRVT2
Galatians 1 in the IRVU
Galatians 1 in the ISVN
Galatians 1 in the JSNT
Galatians 1 in the KAPI
Galatians 1 in the KBT1ETNIK
Galatians 1 in the KBV
Galatians 1 in the KJV
Galatians 1 in the KNFD
Galatians 1 in the LBA
Galatians 1 in the LBLA
Galatians 1 in the LNT
Galatians 1 in the LSV
Galatians 1 in the MAAL
Galatians 1 in the MBV
Galatians 1 in the MBV2
Galatians 1 in the MHNT
Galatians 1 in the MKNFD
Galatians 1 in the MNG
Galatians 1 in the MNT
Galatians 1 in the MNT2
Galatians 1 in the MRS1T
Galatians 1 in the NAA
Galatians 1 in the NASB
Galatians 1 in the NBLA
Galatians 1 in the NBS
Galatians 1 in the NBVTP
Galatians 1 in the NET2
Galatians 1 in the NIV11
Galatians 1 in the NNT
Galatians 1 in the NNT2
Galatians 1 in the NNT3
Galatians 1 in the PDDPT
Galatians 1 in the PFNT
Galatians 1 in the RMNT
Galatians 1 in the SBIAS
Galatians 1 in the SBIBS
Galatians 1 in the SBIBS2
Galatians 1 in the SBICS
Galatians 1 in the SBIDS
Galatians 1 in the SBIGS
Galatians 1 in the SBIHS
Galatians 1 in the SBIIS
Galatians 1 in the SBIIS2
Galatians 1 in the SBIIS3
Galatians 1 in the SBIKS
Galatians 1 in the SBIKS2
Galatians 1 in the SBIMS
Galatians 1 in the SBIOS
Galatians 1 in the SBIPS
Galatians 1 in the SBISS
Galatians 1 in the SBITS
Galatians 1 in the SBITS2
Galatians 1 in the SBITS3
Galatians 1 in the SBITS4
Galatians 1 in the SBIUS
Galatians 1 in the SBIVS
Galatians 1 in the SBT
Galatians 1 in the SBT1E
Galatians 1 in the SCHL
Galatians 1 in the SNT
Galatians 1 in the SUSU
Galatians 1 in the SUSU2
Galatians 1 in the SYNO
Galatians 1 in the TBIAOTANT
Galatians 1 in the TBT1E
Galatians 1 in the TBT1E2
Galatians 1 in the TFTIP
Galatians 1 in the TFTU
Galatians 1 in the TGNTATF3T
Galatians 1 in the THAI
Galatians 1 in the TNFD
Galatians 1 in the TNT
Galatians 1 in the TNTIK
Galatians 1 in the TNTIL
Galatians 1 in the TNTIN
Galatians 1 in the TNTIP
Galatians 1 in the TNTIZ
Galatians 1 in the TOMA
Galatians 1 in the TTENT
Galatians 1 in the UBG
Galatians 1 in the UGV
Galatians 1 in the UGV2
Galatians 1 in the UGV3
Galatians 1 in the VBL
Galatians 1 in the VDCC
Galatians 1 in the YALU
Galatians 1 in the YAPE
Galatians 1 in the YBVTP
Galatians 1 in the ZBP