Hebrews 2 (BOHCB)
1 Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce. 2 Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace, 3 yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi. 4 Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa. 5 Ba ga mala’iku ba ne ya sa su yi mulkin duniya mai zuwa, wanda muke magana a kai ba. 6 Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa,“Mene ne mutum, da kake tuna da shi,ɗan mutum da kake kula da shi? 7 Ka sa shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku;ka naɗa shi da ɗaukaka da girma, 8 ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.”Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba. 9 Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa. 10 Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala. 11 Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa. 12 Ya ce,“Zan sanar da sunanka ga ’yan’uwana;a gaban jama’a zan rera yabonka.” 13 Har wa yau ya ce,“Zan dogara gare shi.”Ya kuma ce,“Ga ni, da ’ya’yan da Allah ya ba ni.” 14 Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis 15 ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta. 16 Gama tabbatacce ba mala’iku ne ya taimaka ba, sai dai zuriyar Ibrahim. 17 Saboda wannan dole a mai da shi kamar ’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane. 18 Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.
In Other Versions
Hebrews 2 in the ANGEFD
Hebrews 2 in the ANTPNG2D
Hebrews 2 in the AS21
Hebrews 2 in the BAGH
Hebrews 2 in the BBPNG
Hebrews 2 in the BBT1E
Hebrews 2 in the BDS
Hebrews 2 in the BEV
Hebrews 2 in the BHAD
Hebrews 2 in the BIB
Hebrews 2 in the BLPT
Hebrews 2 in the BNT
Hebrews 2 in the BNTABOOT
Hebrews 2 in the BNTLV
Hebrews 2 in the BOATCB
Hebrews 2 in the BOATCB2
Hebrews 2 in the BOBCV
Hebrews 2 in the BOCNT
Hebrews 2 in the BOECS
Hebrews 2 in the BOGWICC
Hebrews 2 in the BOHCV
Hebrews 2 in the BOHLNT
Hebrews 2 in the BOHNTLTAL
Hebrews 2 in the BOICB
Hebrews 2 in the BOILNTAP
Hebrews 2 in the BOITCV
Hebrews 2 in the BOKCV
Hebrews 2 in the BOKCV2
Hebrews 2 in the BOKHWOG
Hebrews 2 in the BOKSSV
Hebrews 2 in the BOLCB
Hebrews 2 in the BOLCB2
Hebrews 2 in the BOMCV
Hebrews 2 in the BONAV
Hebrews 2 in the BONCB
Hebrews 2 in the BONLT
Hebrews 2 in the BONUT2
Hebrews 2 in the BOPLNT
Hebrews 2 in the BOSCB
Hebrews 2 in the BOSNC
Hebrews 2 in the BOTLNT
Hebrews 2 in the BOVCB
Hebrews 2 in the BOYCB
Hebrews 2 in the BPBB
Hebrews 2 in the BPH
Hebrews 2 in the BSB
Hebrews 2 in the CCB
Hebrews 2 in the CUV
Hebrews 2 in the CUVS
Hebrews 2 in the DBT
Hebrews 2 in the DGDNT
Hebrews 2 in the DHNT
Hebrews 2 in the DNT
Hebrews 2 in the ELBE
Hebrews 2 in the EMTV
Hebrews 2 in the ESV
Hebrews 2 in the FBV
Hebrews 2 in the FEB
Hebrews 2 in the GGMNT
Hebrews 2 in the GNT
Hebrews 2 in the HARY
Hebrews 2 in the HNT
Hebrews 2 in the IRVA
Hebrews 2 in the IRVB
Hebrews 2 in the IRVG
Hebrews 2 in the IRVH
Hebrews 2 in the IRVK
Hebrews 2 in the IRVM
Hebrews 2 in the IRVM2
Hebrews 2 in the IRVO
Hebrews 2 in the IRVP
Hebrews 2 in the IRVT
Hebrews 2 in the IRVT2
Hebrews 2 in the IRVU
Hebrews 2 in the ISVN
Hebrews 2 in the JSNT
Hebrews 2 in the KAPI
Hebrews 2 in the KBT1ETNIK
Hebrews 2 in the KBV
Hebrews 2 in the KJV
Hebrews 2 in the KNFD
Hebrews 2 in the LBA
Hebrews 2 in the LBLA
Hebrews 2 in the LNT
Hebrews 2 in the LSV
Hebrews 2 in the MAAL
Hebrews 2 in the MBV
Hebrews 2 in the MBV2
Hebrews 2 in the MHNT
Hebrews 2 in the MKNFD
Hebrews 2 in the MNG
Hebrews 2 in the MNT
Hebrews 2 in the MNT2
Hebrews 2 in the MRS1T
Hebrews 2 in the NAA
Hebrews 2 in the NASB
Hebrews 2 in the NBLA
Hebrews 2 in the NBS
Hebrews 2 in the NBVTP
Hebrews 2 in the NET2
Hebrews 2 in the NIV11
Hebrews 2 in the NNT
Hebrews 2 in the NNT2
Hebrews 2 in the NNT3
Hebrews 2 in the PDDPT
Hebrews 2 in the PFNT
Hebrews 2 in the RMNT
Hebrews 2 in the SBIAS
Hebrews 2 in the SBIBS
Hebrews 2 in the SBIBS2
Hebrews 2 in the SBICS
Hebrews 2 in the SBIDS
Hebrews 2 in the SBIGS
Hebrews 2 in the SBIHS
Hebrews 2 in the SBIIS
Hebrews 2 in the SBIIS2
Hebrews 2 in the SBIIS3
Hebrews 2 in the SBIKS
Hebrews 2 in the SBIKS2
Hebrews 2 in the SBIMS
Hebrews 2 in the SBIOS
Hebrews 2 in the SBIPS
Hebrews 2 in the SBISS
Hebrews 2 in the SBITS
Hebrews 2 in the SBITS2
Hebrews 2 in the SBITS3
Hebrews 2 in the SBITS4
Hebrews 2 in the SBIUS
Hebrews 2 in the SBIVS
Hebrews 2 in the SBT
Hebrews 2 in the SBT1E
Hebrews 2 in the SCHL
Hebrews 2 in the SNT
Hebrews 2 in the SUSU
Hebrews 2 in the SUSU2
Hebrews 2 in the SYNO
Hebrews 2 in the TBIAOTANT
Hebrews 2 in the TBT1E
Hebrews 2 in the TBT1E2
Hebrews 2 in the TFTIP
Hebrews 2 in the TFTU
Hebrews 2 in the TGNTATF3T
Hebrews 2 in the THAI
Hebrews 2 in the TNFD
Hebrews 2 in the TNT
Hebrews 2 in the TNTIK
Hebrews 2 in the TNTIL
Hebrews 2 in the TNTIN
Hebrews 2 in the TNTIP
Hebrews 2 in the TNTIZ
Hebrews 2 in the TOMA
Hebrews 2 in the TTENT
Hebrews 2 in the UBG
Hebrews 2 in the UGV
Hebrews 2 in the UGV2
Hebrews 2 in the UGV3
Hebrews 2 in the VBL
Hebrews 2 in the VDCC
Hebrews 2 in the YALU
Hebrews 2 in the YAPE
Hebrews 2 in the YBVTP
Hebrews 2 in the ZBP