John 5 (BOHCB)

1 Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa. 2 To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda an kuma kewaye shi da shirayi biyar. 3 A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu. 5 Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas. 6 Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?” 7 Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.” 8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.” 9 Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya.A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce, 10 saboda haka kuwa Yahudawa suka ce wa mutumin da aka warkar, “Yau Asabbaci ne; doka ta hana ka ɗauki tabarmarka.” 11 Amma ya amsa ya ce, “Mutumin da ya warkar da ni shi ya ce mini, ‘Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’ ” 12 Sai suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan da ya ce maka ka ɗauke ta ka yi tafiya?” 13 Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can. 14 Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.” 15 Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi. 16 To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa. 17 Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.” 18 Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah. 19 Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi. 20 Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma. 21 Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama. 22 Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan, 23 don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan. 24 “Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. 25 Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu. 26 Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa. 27 Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne. 28 “Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa 29 su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci. 30 Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni. 31 “In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce. 32 Akwai wani mai ba da shaida mai kyau a kaina, na kuma san cewa shaidarsa game da ni gaskiya ce. 33 “Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya. 34 Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto. 35 Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci. 36 “Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni. 37 Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba, 38 maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba. 39 Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina, 40 duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai. 41 “Ni ba na neman yabon mutane, 42 na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku. 43 Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi. 44 Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici? 45 “Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. 46 Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni. 47 Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”

In Other Versions

John 5 in the ANGEFD

John 5 in the ANTPNG2D

John 5 in the AS21

John 5 in the BAGH

John 5 in the BBPNG

John 5 in the BBT1E

John 5 in the BDS

John 5 in the BEV

John 5 in the BHAD

John 5 in the BIB

John 5 in the BLPT

John 5 in the BNT

John 5 in the BNTABOOT

John 5 in the BNTLV

John 5 in the BOATCB

John 5 in the BOATCB2

John 5 in the BOBCV

John 5 in the BOCNT

John 5 in the BOECS

John 5 in the BOGWICC

John 5 in the BOHCV

John 5 in the BOHLNT

John 5 in the BOHNTLTAL

John 5 in the BOICB

John 5 in the BOILNTAP

John 5 in the BOITCV

John 5 in the BOKCV

John 5 in the BOKCV2

John 5 in the BOKHWOG

John 5 in the BOKSSV

John 5 in the BOLCB

John 5 in the BOLCB2

John 5 in the BOMCV

John 5 in the BONAV

John 5 in the BONCB

John 5 in the BONLT

John 5 in the BONUT2

John 5 in the BOPLNT

John 5 in the BOSCB

John 5 in the BOSNC

John 5 in the BOTLNT

John 5 in the BOVCB

John 5 in the BOYCB

John 5 in the BPBB

John 5 in the BPH

John 5 in the BSB

John 5 in the CCB

John 5 in the CUV

John 5 in the CUVS

John 5 in the DBT

John 5 in the DGDNT

John 5 in the DHNT

John 5 in the DNT

John 5 in the ELBE

John 5 in the EMTV

John 5 in the ESV

John 5 in the FBV

John 5 in the FEB

John 5 in the GGMNT

John 5 in the GNT

John 5 in the HARY

John 5 in the HNT

John 5 in the IRVA

John 5 in the IRVB

John 5 in the IRVG

John 5 in the IRVH

John 5 in the IRVK

John 5 in the IRVM

John 5 in the IRVM2

John 5 in the IRVO

John 5 in the IRVP

John 5 in the IRVT

John 5 in the IRVT2

John 5 in the IRVU

John 5 in the ISVN

John 5 in the JSNT

John 5 in the KAPI

John 5 in the KBT1ETNIK

John 5 in the KBV

John 5 in the KJV

John 5 in the KNFD

John 5 in the LBA

John 5 in the LBLA

John 5 in the LNT

John 5 in the LSV

John 5 in the MAAL

John 5 in the MBV

John 5 in the MBV2

John 5 in the MHNT

John 5 in the MKNFD

John 5 in the MNG

John 5 in the MNT

John 5 in the MNT2

John 5 in the MRS1T

John 5 in the NAA

John 5 in the NASB

John 5 in the NBLA

John 5 in the NBS

John 5 in the NBVTP

John 5 in the NET2

John 5 in the NIV11

John 5 in the NNT

John 5 in the NNT2

John 5 in the NNT3

John 5 in the PDDPT

John 5 in the PFNT

John 5 in the RMNT

John 5 in the SBIAS

John 5 in the SBIBS

John 5 in the SBIBS2

John 5 in the SBICS

John 5 in the SBIDS

John 5 in the SBIGS

John 5 in the SBIHS

John 5 in the SBIIS

John 5 in the SBIIS2

John 5 in the SBIIS3

John 5 in the SBIKS

John 5 in the SBIKS2

John 5 in the SBIMS

John 5 in the SBIOS

John 5 in the SBIPS

John 5 in the SBISS

John 5 in the SBITS

John 5 in the SBITS2

John 5 in the SBITS3

John 5 in the SBITS4

John 5 in the SBIUS

John 5 in the SBIVS

John 5 in the SBT

John 5 in the SBT1E

John 5 in the SCHL

John 5 in the SNT

John 5 in the SUSU

John 5 in the SUSU2

John 5 in the SYNO

John 5 in the TBIAOTANT

John 5 in the TBT1E

John 5 in the TBT1E2

John 5 in the TFTIP

John 5 in the TFTU

John 5 in the TGNTATF3T

John 5 in the THAI

John 5 in the TNFD

John 5 in the TNT

John 5 in the TNTIK

John 5 in the TNTIL

John 5 in the TNTIN

John 5 in the TNTIP

John 5 in the TNTIZ

John 5 in the TOMA

John 5 in the TTENT

John 5 in the UBG

John 5 in the UGV

John 5 in the UGV2

John 5 in the UGV3

John 5 in the VBL

John 5 in the VDCC

John 5 in the YALU

John 5 in the YAPE

John 5 in the YBVTP

John 5 in the ZBP