Luke 13 (BOHCB)

1 A yanzun fa, akwai waɗansu da suka kasance a lokacin can, suka ba Yesu labarin Galiliyawa da Bilatus ya gauraye jininsu tare da jinin hadayunsu. 2 Yesu ya amsa ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galiliyawan sun fi dukan sauran Galiliyawa zunubi ne, shi ya sa suka sha irin wannan wahala? 3 Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka. 4 Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya a Silowam ya fāɗi a kansu, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne? 5 Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.” 6 Sai ya ba su wannan misali ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire ’ya’yan itacen, sai ya tarar ba tă yi ’ya’ya ba. 7 Sai ya ce wa mai lura da gonar inabin, ‘Yau shekara uku ke nan ina zuwa neman ’ya’yan ɓaure daga itacen nan, amma ba na samun kome. Sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri.’ 8 “Mutumin ya amsa ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ka bar shi, in yi masa banƙasa, in kuma zuba masa taki har na shekara ɗaya. 9 In kuwa ya ba da ’ya’ya shekara mai zuwa, yana da kyau! In kuwa ba haka ba, sai ka sare shi.’ ” 10 Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majami’a, 11 a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan. 12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an ’yantar da ke daga rashin lafiyarki.” 13 Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah. 14 Amma mai mulkin majami’ar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba.” 15 Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ku munafukai! Ashe, kowannenku ba yakan kunce bijiminsa ko jakinsa, yă kai shi waje yă ba shi ruwa, a ranar Asabbaci ba? 16 Ashe, bai kamata a ’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?” 17 Sa’ad da ya faɗi wannan, sai duka masu gāba da shi suka kunyata. Amma mutane kuwa suka yi murna saboda dukan abubuwan banmamaki da yake yi. 18 Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi? 19 Yana kama da ƙwayar mustad, wadda wani mutum ya ɗauka, kuma ya shuka a gonarsa. Ta yi girma, ta zama itace, kuma tsuntsayen sararin sama suka huta a rassansa.” 20 Ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah? 21 Yana kama da yisti wadda mace ta ɗauka, ta kwaɓa garin alkama mai yawa da shi, har sai da yistin ya gauraye kullun duka.” 22 Sa’ad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa. 23 Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?”Ya ce musu, 24 “Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba. 25 Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’ “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’ 26 “Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’ 27 “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’ 28 “Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje. 29 Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah. 30 Tabbatacce, akwai waɗansu da suke na ƙarshe, da za su zama na farko, na farko kuma, da za su zama na ƙarshe.” 31 A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.” 32 Ya amsa ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina. 33 Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’ 34 “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba! 35 Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”

In Other Versions

Luke 13 in the ANGEFD

Luke 13 in the ANTPNG2D

Luke 13 in the AS21

Luke 13 in the BAGH

Luke 13 in the BBPNG

Luke 13 in the BBT1E

Luke 13 in the BDS

Luke 13 in the BEV

Luke 13 in the BHAD

Luke 13 in the BIB

Luke 13 in the BLPT

Luke 13 in the BNT

Luke 13 in the BNTABOOT

Luke 13 in the BNTLV

Luke 13 in the BOATCB

Luke 13 in the BOATCB2

Luke 13 in the BOBCV

Luke 13 in the BOCNT

Luke 13 in the BOECS

Luke 13 in the BOGWICC

Luke 13 in the BOHCV

Luke 13 in the BOHLNT

Luke 13 in the BOHNTLTAL

Luke 13 in the BOICB

Luke 13 in the BOILNTAP

Luke 13 in the BOITCV

Luke 13 in the BOKCV

Luke 13 in the BOKCV2

Luke 13 in the BOKHWOG

Luke 13 in the BOKSSV

Luke 13 in the BOLCB

Luke 13 in the BOLCB2

Luke 13 in the BOMCV

Luke 13 in the BONAV

Luke 13 in the BONCB

Luke 13 in the BONLT

Luke 13 in the BONUT2

Luke 13 in the BOPLNT

Luke 13 in the BOSCB

Luke 13 in the BOSNC

Luke 13 in the BOTLNT

Luke 13 in the BOVCB

Luke 13 in the BOYCB

Luke 13 in the BPBB

Luke 13 in the BPH

Luke 13 in the BSB

Luke 13 in the CCB

Luke 13 in the CUV

Luke 13 in the CUVS

Luke 13 in the DBT

Luke 13 in the DGDNT

Luke 13 in the DHNT

Luke 13 in the DNT

Luke 13 in the ELBE

Luke 13 in the EMTV

Luke 13 in the ESV

Luke 13 in the FBV

Luke 13 in the FEB

Luke 13 in the GGMNT

Luke 13 in the GNT

Luke 13 in the HARY

Luke 13 in the HNT

Luke 13 in the IRVA

Luke 13 in the IRVB

Luke 13 in the IRVG

Luke 13 in the IRVH

Luke 13 in the IRVK

Luke 13 in the IRVM

Luke 13 in the IRVM2

Luke 13 in the IRVO

Luke 13 in the IRVP

Luke 13 in the IRVT

Luke 13 in the IRVT2

Luke 13 in the IRVU

Luke 13 in the ISVN

Luke 13 in the JSNT

Luke 13 in the KAPI

Luke 13 in the KBT1ETNIK

Luke 13 in the KBV

Luke 13 in the KJV

Luke 13 in the KNFD

Luke 13 in the LBA

Luke 13 in the LBLA

Luke 13 in the LNT

Luke 13 in the LSV

Luke 13 in the MAAL

Luke 13 in the MBV

Luke 13 in the MBV2

Luke 13 in the MHNT

Luke 13 in the MKNFD

Luke 13 in the MNG

Luke 13 in the MNT

Luke 13 in the MNT2

Luke 13 in the MRS1T

Luke 13 in the NAA

Luke 13 in the NASB

Luke 13 in the NBLA

Luke 13 in the NBS

Luke 13 in the NBVTP

Luke 13 in the NET2

Luke 13 in the NIV11

Luke 13 in the NNT

Luke 13 in the NNT2

Luke 13 in the NNT3

Luke 13 in the PDDPT

Luke 13 in the PFNT

Luke 13 in the RMNT

Luke 13 in the SBIAS

Luke 13 in the SBIBS

Luke 13 in the SBIBS2

Luke 13 in the SBICS

Luke 13 in the SBIDS

Luke 13 in the SBIGS

Luke 13 in the SBIHS

Luke 13 in the SBIIS

Luke 13 in the SBIIS2

Luke 13 in the SBIIS3

Luke 13 in the SBIKS

Luke 13 in the SBIKS2

Luke 13 in the SBIMS

Luke 13 in the SBIOS

Luke 13 in the SBIPS

Luke 13 in the SBISS

Luke 13 in the SBITS

Luke 13 in the SBITS2

Luke 13 in the SBITS3

Luke 13 in the SBITS4

Luke 13 in the SBIUS

Luke 13 in the SBIVS

Luke 13 in the SBT

Luke 13 in the SBT1E

Luke 13 in the SCHL

Luke 13 in the SNT

Luke 13 in the SUSU

Luke 13 in the SUSU2

Luke 13 in the SYNO

Luke 13 in the TBIAOTANT

Luke 13 in the TBT1E

Luke 13 in the TBT1E2

Luke 13 in the TFTIP

Luke 13 in the TFTU

Luke 13 in the TGNTATF3T

Luke 13 in the THAI

Luke 13 in the TNFD

Luke 13 in the TNT

Luke 13 in the TNTIK

Luke 13 in the TNTIL

Luke 13 in the TNTIN

Luke 13 in the TNTIP

Luke 13 in the TNTIZ

Luke 13 in the TOMA

Luke 13 in the TTENT

Luke 13 in the UBG

Luke 13 in the UGV

Luke 13 in the UGV2

Luke 13 in the UGV3

Luke 13 in the VBL

Luke 13 in the VDCC

Luke 13 in the YALU

Luke 13 in the YAPE

Luke 13 in the YBVTP

Luke 13 in the ZBP