Luke 5 (BOHCB)

1 Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah, 2 sai ya hangi jiragen ruwa biyu a bakin tafkin, waɗanda masu kamun kifi suka bari suna wankin abin kamun kifinsu. 3 Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki. 4 Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.” 5 Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.” 6 Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har abin kamun kifinsu suka fara tsintsinkewa. 7 Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa. 8 Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!” 9 Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama. 10 Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki.Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.” 11 Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi. 12 Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni.” 13 Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi. 14 Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.” 15 Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu. 16 Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yă yi addu’a. 17 Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yă warkar da masu ciwo. 18 Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu. 19 Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu. 20 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Saurayi, an gafarta maka zunubanka.” 21 Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?” 22 Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku? 23 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’? 24 Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.” 25 Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah. 26 Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.” 27 Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” 28 Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi. 29 Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su. 30 Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. 32 Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.” 33 Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da addu’a, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.” 34 Yesu ya amsa ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su? 35 Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.” 36 Sai ya faɗa musu wannan misali ya ce, “Ba wanda yakan yage ƙyalle daga sabuwar riga ya yi wa tsohuwar riga faci. In ya yi haka, zai yage sabuwar rigar, kuma facin daga sabuwar ba zai dace da tsohuwar rigar ba. 37 Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yă zube, salkunan kuma su lalace. 38 A’a, sai dai a zuba sabon ruwan inabi a sababbin salkuna. 39 Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’ ”

In Other Versions

Luke 5 in the ANGEFD

Luke 5 in the ANTPNG2D

Luke 5 in the AS21

Luke 5 in the BAGH

Luke 5 in the BBPNG

Luke 5 in the BBT1E

Luke 5 in the BDS

Luke 5 in the BEV

Luke 5 in the BHAD

Luke 5 in the BIB

Luke 5 in the BLPT

Luke 5 in the BNT

Luke 5 in the BNTABOOT

Luke 5 in the BNTLV

Luke 5 in the BOATCB

Luke 5 in the BOATCB2

Luke 5 in the BOBCV

Luke 5 in the BOCNT

Luke 5 in the BOECS

Luke 5 in the BOGWICC

Luke 5 in the BOHCV

Luke 5 in the BOHLNT

Luke 5 in the BOHNTLTAL

Luke 5 in the BOICB

Luke 5 in the BOILNTAP

Luke 5 in the BOITCV

Luke 5 in the BOKCV

Luke 5 in the BOKCV2

Luke 5 in the BOKHWOG

Luke 5 in the BOKSSV

Luke 5 in the BOLCB

Luke 5 in the BOLCB2

Luke 5 in the BOMCV

Luke 5 in the BONAV

Luke 5 in the BONCB

Luke 5 in the BONLT

Luke 5 in the BONUT2

Luke 5 in the BOPLNT

Luke 5 in the BOSCB

Luke 5 in the BOSNC

Luke 5 in the BOTLNT

Luke 5 in the BOVCB

Luke 5 in the BOYCB

Luke 5 in the BPBB

Luke 5 in the BPH

Luke 5 in the BSB

Luke 5 in the CCB

Luke 5 in the CUV

Luke 5 in the CUVS

Luke 5 in the DBT

Luke 5 in the DGDNT

Luke 5 in the DHNT

Luke 5 in the DNT

Luke 5 in the ELBE

Luke 5 in the EMTV

Luke 5 in the ESV

Luke 5 in the FBV

Luke 5 in the FEB

Luke 5 in the GGMNT

Luke 5 in the GNT

Luke 5 in the HARY

Luke 5 in the HNT

Luke 5 in the IRVA

Luke 5 in the IRVB

Luke 5 in the IRVG

Luke 5 in the IRVH

Luke 5 in the IRVK

Luke 5 in the IRVM

Luke 5 in the IRVM2

Luke 5 in the IRVO

Luke 5 in the IRVP

Luke 5 in the IRVT

Luke 5 in the IRVT2

Luke 5 in the IRVU

Luke 5 in the ISVN

Luke 5 in the JSNT

Luke 5 in the KAPI

Luke 5 in the KBT1ETNIK

Luke 5 in the KBV

Luke 5 in the KJV

Luke 5 in the KNFD

Luke 5 in the LBA

Luke 5 in the LBLA

Luke 5 in the LNT

Luke 5 in the LSV

Luke 5 in the MAAL

Luke 5 in the MBV

Luke 5 in the MBV2

Luke 5 in the MHNT

Luke 5 in the MKNFD

Luke 5 in the MNG

Luke 5 in the MNT

Luke 5 in the MNT2

Luke 5 in the MRS1T

Luke 5 in the NAA

Luke 5 in the NASB

Luke 5 in the NBLA

Luke 5 in the NBS

Luke 5 in the NBVTP

Luke 5 in the NET2

Luke 5 in the NIV11

Luke 5 in the NNT

Luke 5 in the NNT2

Luke 5 in the NNT3

Luke 5 in the PDDPT

Luke 5 in the PFNT

Luke 5 in the RMNT

Luke 5 in the SBIAS

Luke 5 in the SBIBS

Luke 5 in the SBIBS2

Luke 5 in the SBICS

Luke 5 in the SBIDS

Luke 5 in the SBIGS

Luke 5 in the SBIHS

Luke 5 in the SBIIS

Luke 5 in the SBIIS2

Luke 5 in the SBIIS3

Luke 5 in the SBIKS

Luke 5 in the SBIKS2

Luke 5 in the SBIMS

Luke 5 in the SBIOS

Luke 5 in the SBIPS

Luke 5 in the SBISS

Luke 5 in the SBITS

Luke 5 in the SBITS2

Luke 5 in the SBITS3

Luke 5 in the SBITS4

Luke 5 in the SBIUS

Luke 5 in the SBIVS

Luke 5 in the SBT

Luke 5 in the SBT1E

Luke 5 in the SCHL

Luke 5 in the SNT

Luke 5 in the SUSU

Luke 5 in the SUSU2

Luke 5 in the SYNO

Luke 5 in the TBIAOTANT

Luke 5 in the TBT1E

Luke 5 in the TBT1E2

Luke 5 in the TFTIP

Luke 5 in the TFTU

Luke 5 in the TGNTATF3T

Luke 5 in the THAI

Luke 5 in the TNFD

Luke 5 in the TNT

Luke 5 in the TNTIK

Luke 5 in the TNTIL

Luke 5 in the TNTIN

Luke 5 in the TNTIP

Luke 5 in the TNTIZ

Luke 5 in the TOMA

Luke 5 in the TTENT

Luke 5 in the UBG

Luke 5 in the UGV

Luke 5 in the UGV2

Luke 5 in the UGV3

Luke 5 in the VBL

Luke 5 in the VDCC

Luke 5 in the YALU

Luke 5 in the YAPE

Luke 5 in the YBVTP

Luke 5 in the ZBP