Matthew 17 (BOHCB)
1 Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. 2 A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya. 3 Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu. 4 Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” 5 Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!” 6 Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice. 7 Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8 Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai. 9 Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an tā da Ɗan Mutum daga matattu.” 10 Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Iliya ya fara zuwa?” 11 Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa. 12 Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.” 13 Sa’an nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne. 14 Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. 15 Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. 16 Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.” 17 Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.” 18 Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke. 19 Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?” 20 Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.” 22 Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, “Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane. 23 Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki. 24 Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?” 25 Ya amsa ya ce “I, yana biya.”Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?” 26 Bitrus ya amsa ya ce, “Daga wurin waɗansu.”Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa ’ya’yan ke nan. 27 Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”
In Other Versions
Matthew 17 in the ANGEFD
Matthew 17 in the ANTPNG2D
Matthew 17 in the AS21
Matthew 17 in the BAGH
Matthew 17 in the BBPNG
Matthew 17 in the BBT1E
Matthew 17 in the BDS
Matthew 17 in the BEV
Matthew 17 in the BHAD
Matthew 17 in the BIB
Matthew 17 in the BLPT
Matthew 17 in the BNT
Matthew 17 in the BNTABOOT
Matthew 17 in the BNTLV
Matthew 17 in the BOATCB
Matthew 17 in the BOATCB2
Matthew 17 in the BOBCV
Matthew 17 in the BOCNT
Matthew 17 in the BOECS
Matthew 17 in the BOGWICC
Matthew 17 in the BOHCV
Matthew 17 in the BOHLNT
Matthew 17 in the BOHNTLTAL
Matthew 17 in the BOICB
Matthew 17 in the BOILNTAP
Matthew 17 in the BOITCV
Matthew 17 in the BOKCV
Matthew 17 in the BOKCV2
Matthew 17 in the BOKHWOG
Matthew 17 in the BOKSSV
Matthew 17 in the BOLCB
Matthew 17 in the BOLCB2
Matthew 17 in the BOMCV
Matthew 17 in the BONAV
Matthew 17 in the BONCB
Matthew 17 in the BONLT
Matthew 17 in the BONUT2
Matthew 17 in the BOPLNT
Matthew 17 in the BOSCB
Matthew 17 in the BOSNC
Matthew 17 in the BOTLNT
Matthew 17 in the BOVCB
Matthew 17 in the BOYCB
Matthew 17 in the BPBB
Matthew 17 in the BPH
Matthew 17 in the BSB
Matthew 17 in the CCB
Matthew 17 in the CUV
Matthew 17 in the CUVS
Matthew 17 in the DBT
Matthew 17 in the DGDNT
Matthew 17 in the DHNT
Matthew 17 in the DNT
Matthew 17 in the ELBE
Matthew 17 in the EMTV
Matthew 17 in the ESV
Matthew 17 in the FBV
Matthew 17 in the FEB
Matthew 17 in the GGMNT
Matthew 17 in the GNT
Matthew 17 in the HARY
Matthew 17 in the HNT
Matthew 17 in the IRVA
Matthew 17 in the IRVB
Matthew 17 in the IRVG
Matthew 17 in the IRVH
Matthew 17 in the IRVK
Matthew 17 in the IRVM
Matthew 17 in the IRVM2
Matthew 17 in the IRVO
Matthew 17 in the IRVP
Matthew 17 in the IRVT
Matthew 17 in the IRVT2
Matthew 17 in the IRVU
Matthew 17 in the ISVN
Matthew 17 in the JSNT
Matthew 17 in the KAPI
Matthew 17 in the KBT1ETNIK
Matthew 17 in the KBV
Matthew 17 in the KJV
Matthew 17 in the KNFD
Matthew 17 in the LBA
Matthew 17 in the LBLA
Matthew 17 in the LNT
Matthew 17 in the LSV
Matthew 17 in the MAAL
Matthew 17 in the MBV
Matthew 17 in the MBV2
Matthew 17 in the MHNT
Matthew 17 in the MKNFD
Matthew 17 in the MNG
Matthew 17 in the MNT
Matthew 17 in the MNT2
Matthew 17 in the MRS1T
Matthew 17 in the NAA
Matthew 17 in the NASB
Matthew 17 in the NBLA
Matthew 17 in the NBS
Matthew 17 in the NBVTP
Matthew 17 in the NET2
Matthew 17 in the NIV11
Matthew 17 in the NNT
Matthew 17 in the NNT2
Matthew 17 in the NNT3
Matthew 17 in the PDDPT
Matthew 17 in the PFNT
Matthew 17 in the RMNT
Matthew 17 in the SBIAS
Matthew 17 in the SBIBS
Matthew 17 in the SBIBS2
Matthew 17 in the SBICS
Matthew 17 in the SBIDS
Matthew 17 in the SBIGS
Matthew 17 in the SBIHS
Matthew 17 in the SBIIS
Matthew 17 in the SBIIS2
Matthew 17 in the SBIIS3
Matthew 17 in the SBIKS
Matthew 17 in the SBIKS2
Matthew 17 in the SBIMS
Matthew 17 in the SBIOS
Matthew 17 in the SBIPS
Matthew 17 in the SBISS
Matthew 17 in the SBITS
Matthew 17 in the SBITS2
Matthew 17 in the SBITS3
Matthew 17 in the SBITS4
Matthew 17 in the SBIUS
Matthew 17 in the SBIVS
Matthew 17 in the SBT
Matthew 17 in the SBT1E
Matthew 17 in the SCHL
Matthew 17 in the SNT
Matthew 17 in the SUSU
Matthew 17 in the SUSU2
Matthew 17 in the SYNO
Matthew 17 in the TBIAOTANT
Matthew 17 in the TBT1E
Matthew 17 in the TBT1E2
Matthew 17 in the TFTIP
Matthew 17 in the TFTU
Matthew 17 in the TGNTATF3T
Matthew 17 in the THAI
Matthew 17 in the TNFD
Matthew 17 in the TNT
Matthew 17 in the TNTIK
Matthew 17 in the TNTIL
Matthew 17 in the TNTIN
Matthew 17 in the TNTIP
Matthew 17 in the TNTIZ
Matthew 17 in the TOMA
Matthew 17 in the TTENT
Matthew 17 in the UBG
Matthew 17 in the UGV
Matthew 17 in the UGV2
Matthew 17 in the UGV3
Matthew 17 in the VBL
Matthew 17 in the VDCC
Matthew 17 in the YALU
Matthew 17 in the YAPE
Matthew 17 in the YBVTP
Matthew 17 in the ZBP