Matthew 28 (BOHCB)

1 Bayan ranar Asabbaci, da sassafe, a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin tare da ɗaya Maryamun, suka je don su ga kabarin. 2 Sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa. Don wani mala’ikan Ubangiji ya sauka daga sama, ya je kabarin, ya gungurar da dutsen, ya kuma zauna a kai. 3 Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara. 4 Masu gadin kabarin kuma suka ji tsoro ƙwarai, suka yi rawan jiki, suka zama kamar matattu. 5 Mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne. 6 Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta. 7 Sai ku tafi da sauri ku gaya wa almajiransa cewa, ‘Ya tashi daga matattu, ya kuma ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi.’ Ga shi na faɗa muku.” 8 Sai matan suka bar kabarin da hanzari, da tsoro, sai dai cike da farin ciki, suka tafi a guje don su gaya wa almajiransa. 9 Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su ya ce, “Gaisuwa.” Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada. 10 Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku tafi ku gaya wa ’yan’uwana, su tafi Galili. A can za su gan ni.” 11 Yayinda matan nan suna cikin tafiya, sai waɗansu daga cikin masu gadin suka shiga gari, suka ba wa manyan firistoci labarin duk abin da ya faru. 12 Da manyan firistoci da dattawa suka taru, sai suka ƙulla wata dabara, suka ba wa sojojin kuɗi mai yawa. 13 Suka ce musu, “Ku, za ku ce, ‘Almajiransa ne sun zo da dare suka sace shi, lokacin da muke barci.’ 14 In wannan labari ya kai kunnen gwamna, za mu lallashe shi, mu kuma kāre ku daga duk wata wahala.” 15 Sai sojojin suka karɓi kuɗin, suka kuma yi kamar yadda aka umarce su. Wannan labarin kuwa shi ne ake bazawa ko’ina a cikin Yahudawa, har yă zuwa yau. 16 Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. 17 Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18 Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”

In Other Versions

Matthew 28 in the ANGEFD

Matthew 28 in the ANTPNG2D

Matthew 28 in the AS21

Matthew 28 in the BAGH

Matthew 28 in the BBPNG

Matthew 28 in the BBT1E

Matthew 28 in the BDS

Matthew 28 in the BEV

Matthew 28 in the BHAD

Matthew 28 in the BIB

Matthew 28 in the BLPT

Matthew 28 in the BNT

Matthew 28 in the BNTABOOT

Matthew 28 in the BNTLV

Matthew 28 in the BOATCB

Matthew 28 in the BOATCB2

Matthew 28 in the BOBCV

Matthew 28 in the BOCNT

Matthew 28 in the BOECS

Matthew 28 in the BOGWICC

Matthew 28 in the BOHCV

Matthew 28 in the BOHLNT

Matthew 28 in the BOHNTLTAL

Matthew 28 in the BOICB

Matthew 28 in the BOILNTAP

Matthew 28 in the BOITCV

Matthew 28 in the BOKCV

Matthew 28 in the BOKCV2

Matthew 28 in the BOKHWOG

Matthew 28 in the BOKSSV

Matthew 28 in the BOLCB

Matthew 28 in the BOLCB2

Matthew 28 in the BOMCV

Matthew 28 in the BONAV

Matthew 28 in the BONCB

Matthew 28 in the BONLT

Matthew 28 in the BONUT2

Matthew 28 in the BOPLNT

Matthew 28 in the BOSCB

Matthew 28 in the BOSNC

Matthew 28 in the BOTLNT

Matthew 28 in the BOVCB

Matthew 28 in the BOYCB

Matthew 28 in the BPBB

Matthew 28 in the BPH

Matthew 28 in the BSB

Matthew 28 in the CCB

Matthew 28 in the CUV

Matthew 28 in the CUVS

Matthew 28 in the DBT

Matthew 28 in the DGDNT

Matthew 28 in the DHNT

Matthew 28 in the DNT

Matthew 28 in the ELBE

Matthew 28 in the EMTV

Matthew 28 in the ESV

Matthew 28 in the FBV

Matthew 28 in the FEB

Matthew 28 in the GGMNT

Matthew 28 in the GNT

Matthew 28 in the HARY

Matthew 28 in the HNT

Matthew 28 in the IRVA

Matthew 28 in the IRVB

Matthew 28 in the IRVG

Matthew 28 in the IRVH

Matthew 28 in the IRVK

Matthew 28 in the IRVM

Matthew 28 in the IRVM2

Matthew 28 in the IRVO

Matthew 28 in the IRVP

Matthew 28 in the IRVT

Matthew 28 in the IRVT2

Matthew 28 in the IRVU

Matthew 28 in the ISVN

Matthew 28 in the JSNT

Matthew 28 in the KAPI

Matthew 28 in the KBT1ETNIK

Matthew 28 in the KBV

Matthew 28 in the KJV

Matthew 28 in the KNFD

Matthew 28 in the LBA

Matthew 28 in the LBLA

Matthew 28 in the LNT

Matthew 28 in the LSV

Matthew 28 in the MAAL

Matthew 28 in the MBV

Matthew 28 in the MBV2

Matthew 28 in the MHNT

Matthew 28 in the MKNFD

Matthew 28 in the MNG

Matthew 28 in the MNT

Matthew 28 in the MNT2

Matthew 28 in the MRS1T

Matthew 28 in the NAA

Matthew 28 in the NASB

Matthew 28 in the NBLA

Matthew 28 in the NBS

Matthew 28 in the NBVTP

Matthew 28 in the NET2

Matthew 28 in the NIV11

Matthew 28 in the NNT

Matthew 28 in the NNT2

Matthew 28 in the NNT3

Matthew 28 in the PDDPT

Matthew 28 in the PFNT

Matthew 28 in the RMNT

Matthew 28 in the SBIAS

Matthew 28 in the SBIBS

Matthew 28 in the SBIBS2

Matthew 28 in the SBICS

Matthew 28 in the SBIDS

Matthew 28 in the SBIGS

Matthew 28 in the SBIHS

Matthew 28 in the SBIIS

Matthew 28 in the SBIIS2

Matthew 28 in the SBIIS3

Matthew 28 in the SBIKS

Matthew 28 in the SBIKS2

Matthew 28 in the SBIMS

Matthew 28 in the SBIOS

Matthew 28 in the SBIPS

Matthew 28 in the SBISS

Matthew 28 in the SBITS

Matthew 28 in the SBITS2

Matthew 28 in the SBITS3

Matthew 28 in the SBITS4

Matthew 28 in the SBIUS

Matthew 28 in the SBIVS

Matthew 28 in the SBT

Matthew 28 in the SBT1E

Matthew 28 in the SCHL

Matthew 28 in the SNT

Matthew 28 in the SUSU

Matthew 28 in the SUSU2

Matthew 28 in the SYNO

Matthew 28 in the TBIAOTANT

Matthew 28 in the TBT1E

Matthew 28 in the TBT1E2

Matthew 28 in the TFTIP

Matthew 28 in the TFTU

Matthew 28 in the TGNTATF3T

Matthew 28 in the THAI

Matthew 28 in the TNFD

Matthew 28 in the TNT

Matthew 28 in the TNTIK

Matthew 28 in the TNTIL

Matthew 28 in the TNTIN

Matthew 28 in the TNTIP

Matthew 28 in the TNTIZ

Matthew 28 in the TOMA

Matthew 28 in the TTENT

Matthew 28 in the UBG

Matthew 28 in the UGV

Matthew 28 in the UGV2

Matthew 28 in the UGV3

Matthew 28 in the VBL

Matthew 28 in the VDCC

Matthew 28 in the YALU

Matthew 28 in the YAPE

Matthew 28 in the YBVTP

Matthew 28 in the ZBP