Matthew 8 (BOHCB)

1 Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi. 2 Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.” 3 Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa. 4 Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.” 5 Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako. 6 Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.” 7 Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.” 8 Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke. 9 Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yă yi.” 10 Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Isra’ila da bangaskiya mai girma haka ba. 11 Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama. 12 Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.” 13 Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke. 14 Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi. 15 Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima. 16 Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17 Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,“Ya ɗebi rashin lafiyarmu,ya kuma ɗauki cututtukanmu.” 18 Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin. 19 Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.” 20 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.” 21 Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.” 22 Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.” 23 Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi. 24 Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25 Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!” 26 Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya. 27 Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!” 28 Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya. 29 Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi? 30 Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo. 31 Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” 32 Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa. 33 Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu. 34 Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yă bar musu yanki.

In Other Versions

Matthew 8 in the ANGEFD

Matthew 8 in the ANTPNG2D

Matthew 8 in the AS21

Matthew 8 in the BAGH

Matthew 8 in the BBPNG

Matthew 8 in the BBT1E

Matthew 8 in the BDS

Matthew 8 in the BEV

Matthew 8 in the BHAD

Matthew 8 in the BIB

Matthew 8 in the BLPT

Matthew 8 in the BNT

Matthew 8 in the BNTABOOT

Matthew 8 in the BNTLV

Matthew 8 in the BOATCB

Matthew 8 in the BOATCB2

Matthew 8 in the BOBCV

Matthew 8 in the BOCNT

Matthew 8 in the BOECS

Matthew 8 in the BOGWICC

Matthew 8 in the BOHCV

Matthew 8 in the BOHLNT

Matthew 8 in the BOHNTLTAL

Matthew 8 in the BOICB

Matthew 8 in the BOILNTAP

Matthew 8 in the BOITCV

Matthew 8 in the BOKCV

Matthew 8 in the BOKCV2

Matthew 8 in the BOKHWOG

Matthew 8 in the BOKSSV

Matthew 8 in the BOLCB

Matthew 8 in the BOLCB2

Matthew 8 in the BOMCV

Matthew 8 in the BONAV

Matthew 8 in the BONCB

Matthew 8 in the BONLT

Matthew 8 in the BONUT2

Matthew 8 in the BOPLNT

Matthew 8 in the BOSCB

Matthew 8 in the BOSNC

Matthew 8 in the BOTLNT

Matthew 8 in the BOVCB

Matthew 8 in the BOYCB

Matthew 8 in the BPBB

Matthew 8 in the BPH

Matthew 8 in the BSB

Matthew 8 in the CCB

Matthew 8 in the CUV

Matthew 8 in the CUVS

Matthew 8 in the DBT

Matthew 8 in the DGDNT

Matthew 8 in the DHNT

Matthew 8 in the DNT

Matthew 8 in the ELBE

Matthew 8 in the EMTV

Matthew 8 in the ESV

Matthew 8 in the FBV

Matthew 8 in the FEB

Matthew 8 in the GGMNT

Matthew 8 in the GNT

Matthew 8 in the HARY

Matthew 8 in the HNT

Matthew 8 in the IRVA

Matthew 8 in the IRVB

Matthew 8 in the IRVG

Matthew 8 in the IRVH

Matthew 8 in the IRVK

Matthew 8 in the IRVM

Matthew 8 in the IRVM2

Matthew 8 in the IRVO

Matthew 8 in the IRVP

Matthew 8 in the IRVT

Matthew 8 in the IRVT2

Matthew 8 in the IRVU

Matthew 8 in the ISVN

Matthew 8 in the JSNT

Matthew 8 in the KAPI

Matthew 8 in the KBT1ETNIK

Matthew 8 in the KBV

Matthew 8 in the KJV

Matthew 8 in the KNFD

Matthew 8 in the LBA

Matthew 8 in the LBLA

Matthew 8 in the LNT

Matthew 8 in the LSV

Matthew 8 in the MAAL

Matthew 8 in the MBV

Matthew 8 in the MBV2

Matthew 8 in the MHNT

Matthew 8 in the MKNFD

Matthew 8 in the MNG

Matthew 8 in the MNT

Matthew 8 in the MNT2

Matthew 8 in the MRS1T

Matthew 8 in the NAA

Matthew 8 in the NASB

Matthew 8 in the NBLA

Matthew 8 in the NBS

Matthew 8 in the NBVTP

Matthew 8 in the NET2

Matthew 8 in the NIV11

Matthew 8 in the NNT

Matthew 8 in the NNT2

Matthew 8 in the NNT3

Matthew 8 in the PDDPT

Matthew 8 in the PFNT

Matthew 8 in the RMNT

Matthew 8 in the SBIAS

Matthew 8 in the SBIBS

Matthew 8 in the SBIBS2

Matthew 8 in the SBICS

Matthew 8 in the SBIDS

Matthew 8 in the SBIGS

Matthew 8 in the SBIHS

Matthew 8 in the SBIIS

Matthew 8 in the SBIIS2

Matthew 8 in the SBIIS3

Matthew 8 in the SBIKS

Matthew 8 in the SBIKS2

Matthew 8 in the SBIMS

Matthew 8 in the SBIOS

Matthew 8 in the SBIPS

Matthew 8 in the SBISS

Matthew 8 in the SBITS

Matthew 8 in the SBITS2

Matthew 8 in the SBITS3

Matthew 8 in the SBITS4

Matthew 8 in the SBIUS

Matthew 8 in the SBIVS

Matthew 8 in the SBT

Matthew 8 in the SBT1E

Matthew 8 in the SCHL

Matthew 8 in the SNT

Matthew 8 in the SUSU

Matthew 8 in the SUSU2

Matthew 8 in the SYNO

Matthew 8 in the TBIAOTANT

Matthew 8 in the TBT1E

Matthew 8 in the TBT1E2

Matthew 8 in the TFTIP

Matthew 8 in the TFTU

Matthew 8 in the TGNTATF3T

Matthew 8 in the THAI

Matthew 8 in the TNFD

Matthew 8 in the TNT

Matthew 8 in the TNTIK

Matthew 8 in the TNTIL

Matthew 8 in the TNTIN

Matthew 8 in the TNTIP

Matthew 8 in the TNTIZ

Matthew 8 in the TOMA

Matthew 8 in the TTENT

Matthew 8 in the UBG

Matthew 8 in the UGV

Matthew 8 in the UGV2

Matthew 8 in the UGV3

Matthew 8 in the VBL

Matthew 8 in the VDCC

Matthew 8 in the YALU

Matthew 8 in the YAPE

Matthew 8 in the YBVTP

Matthew 8 in the ZBP