1 Corinthians 10 (BOHCB)

1 Ba na so ku kasance da rashin sani, ’yan’uwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku. 2 An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku. 3 Dukansu sun ci abincin ruhaniya guda 4 suka kuma sha ruwan ruhaniyan nan guda; gama sun sha daga dutsen ruhaniya nan, wanda ya yi tafiya tare da su, wannan dutsen kuwa Kiristi ne. 5 Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu ko’ina a cikin hamada. 6 To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi. 7 Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.” 8 Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu. 9 Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su. 10 Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su. 11 Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12 Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi! 13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara. 14 Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka. 15 Ina magana da ku a kan ku mutane ne fa masu azanci; ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa. 16 Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba? 17 Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda. 18 Ku dubi mutanen Isra’ila mana. Ashe, waɗanda suke cin hadayu, ba ɗaya suke da juna cikin cin hadayun da aka miƙa a bagade ba? 19 To, me kuke tsammani nake nufi a nan? Hadayar da aka miƙa wa gunki ce wani abu, ko kuma gunkin ne wani abu? 20 A’a, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu. 21 Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a teburin aljanu. 22 Ashe, so muke mu tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne? 23 “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa. 24 Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma. 25 Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito, 26 gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.” 27 In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito. 28 Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yă kasance babu laifi 29 ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shari’anta ’yancina? 30 In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah? 31 Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah. 32 Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah 33 kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto.

In Other Versions

1 Corinthians 10 in the ANGEFD

1 Corinthians 10 in the ANTPNG2D

1 Corinthians 10 in the AS21

1 Corinthians 10 in the BAGH

1 Corinthians 10 in the BBPNG

1 Corinthians 10 in the BBT1E

1 Corinthians 10 in the BDS

1 Corinthians 10 in the BEV

1 Corinthians 10 in the BHAD

1 Corinthians 10 in the BIB

1 Corinthians 10 in the BLPT

1 Corinthians 10 in the BNT

1 Corinthians 10 in the BNTABOOT

1 Corinthians 10 in the BNTLV

1 Corinthians 10 in the BOATCB

1 Corinthians 10 in the BOATCB2

1 Corinthians 10 in the BOBCV

1 Corinthians 10 in the BOCNT

1 Corinthians 10 in the BOECS

1 Corinthians 10 in the BOGWICC

1 Corinthians 10 in the BOHCV

1 Corinthians 10 in the BOHLNT

1 Corinthians 10 in the BOHNTLTAL

1 Corinthians 10 in the BOICB

1 Corinthians 10 in the BOILNTAP

1 Corinthians 10 in the BOITCV

1 Corinthians 10 in the BOKCV

1 Corinthians 10 in the BOKCV2

1 Corinthians 10 in the BOKHWOG

1 Corinthians 10 in the BOKSSV

1 Corinthians 10 in the BOLCB

1 Corinthians 10 in the BOLCB2

1 Corinthians 10 in the BOMCV

1 Corinthians 10 in the BONAV

1 Corinthians 10 in the BONCB

1 Corinthians 10 in the BONLT

1 Corinthians 10 in the BONUT2

1 Corinthians 10 in the BOPLNT

1 Corinthians 10 in the BOSCB

1 Corinthians 10 in the BOSNC

1 Corinthians 10 in the BOTLNT

1 Corinthians 10 in the BOVCB

1 Corinthians 10 in the BOYCB

1 Corinthians 10 in the BPBB

1 Corinthians 10 in the BPH

1 Corinthians 10 in the BSB

1 Corinthians 10 in the CCB

1 Corinthians 10 in the CUV

1 Corinthians 10 in the CUVS

1 Corinthians 10 in the DBT

1 Corinthians 10 in the DGDNT

1 Corinthians 10 in the DHNT

1 Corinthians 10 in the DNT

1 Corinthians 10 in the ELBE

1 Corinthians 10 in the EMTV

1 Corinthians 10 in the ESV

1 Corinthians 10 in the FBV

1 Corinthians 10 in the FEB

1 Corinthians 10 in the GGMNT

1 Corinthians 10 in the GNT

1 Corinthians 10 in the HARY

1 Corinthians 10 in the HNT

1 Corinthians 10 in the IRVA

1 Corinthians 10 in the IRVB

1 Corinthians 10 in the IRVG

1 Corinthians 10 in the IRVH

1 Corinthians 10 in the IRVK

1 Corinthians 10 in the IRVM

1 Corinthians 10 in the IRVM2

1 Corinthians 10 in the IRVO

1 Corinthians 10 in the IRVP

1 Corinthians 10 in the IRVT

1 Corinthians 10 in the IRVT2

1 Corinthians 10 in the IRVU

1 Corinthians 10 in the ISVN

1 Corinthians 10 in the JSNT

1 Corinthians 10 in the KAPI

1 Corinthians 10 in the KBT1ETNIK

1 Corinthians 10 in the KBV

1 Corinthians 10 in the KJV

1 Corinthians 10 in the KNFD

1 Corinthians 10 in the LBA

1 Corinthians 10 in the LBLA

1 Corinthians 10 in the LNT

1 Corinthians 10 in the LSV

1 Corinthians 10 in the MAAL

1 Corinthians 10 in the MBV

1 Corinthians 10 in the MBV2

1 Corinthians 10 in the MHNT

1 Corinthians 10 in the MKNFD

1 Corinthians 10 in the MNG

1 Corinthians 10 in the MNT

1 Corinthians 10 in the MNT2

1 Corinthians 10 in the MRS1T

1 Corinthians 10 in the NAA

1 Corinthians 10 in the NASB

1 Corinthians 10 in the NBLA

1 Corinthians 10 in the NBS

1 Corinthians 10 in the NBVTP

1 Corinthians 10 in the NET2

1 Corinthians 10 in the NIV11

1 Corinthians 10 in the NNT

1 Corinthians 10 in the NNT2

1 Corinthians 10 in the NNT3

1 Corinthians 10 in the PDDPT

1 Corinthians 10 in the PFNT

1 Corinthians 10 in the RMNT

1 Corinthians 10 in the SBIAS

1 Corinthians 10 in the SBIBS

1 Corinthians 10 in the SBIBS2

1 Corinthians 10 in the SBICS

1 Corinthians 10 in the SBIDS

1 Corinthians 10 in the SBIGS

1 Corinthians 10 in the SBIHS

1 Corinthians 10 in the SBIIS

1 Corinthians 10 in the SBIIS2

1 Corinthians 10 in the SBIIS3

1 Corinthians 10 in the SBIKS

1 Corinthians 10 in the SBIKS2

1 Corinthians 10 in the SBIMS

1 Corinthians 10 in the SBIOS

1 Corinthians 10 in the SBIPS

1 Corinthians 10 in the SBISS

1 Corinthians 10 in the SBITS

1 Corinthians 10 in the SBITS2

1 Corinthians 10 in the SBITS3

1 Corinthians 10 in the SBITS4

1 Corinthians 10 in the SBIUS

1 Corinthians 10 in the SBIVS

1 Corinthians 10 in the SBT

1 Corinthians 10 in the SBT1E

1 Corinthians 10 in the SCHL

1 Corinthians 10 in the SNT

1 Corinthians 10 in the SUSU

1 Corinthians 10 in the SUSU2

1 Corinthians 10 in the SYNO

1 Corinthians 10 in the TBIAOTANT

1 Corinthians 10 in the TBT1E

1 Corinthians 10 in the TBT1E2

1 Corinthians 10 in the TFTIP

1 Corinthians 10 in the TFTU

1 Corinthians 10 in the TGNTATF3T

1 Corinthians 10 in the THAI

1 Corinthians 10 in the TNFD

1 Corinthians 10 in the TNT

1 Corinthians 10 in the TNTIK

1 Corinthians 10 in the TNTIL

1 Corinthians 10 in the TNTIN

1 Corinthians 10 in the TNTIP

1 Corinthians 10 in the TNTIZ

1 Corinthians 10 in the TOMA

1 Corinthians 10 in the TTENT

1 Corinthians 10 in the UBG

1 Corinthians 10 in the UGV

1 Corinthians 10 in the UGV2

1 Corinthians 10 in the UGV3

1 Corinthians 10 in the VBL

1 Corinthians 10 in the VDCC

1 Corinthians 10 in the YALU

1 Corinthians 10 in the YAPE

1 Corinthians 10 in the YBVTP

1 Corinthians 10 in the ZBP