1 Thessalonians 2 (BOHCB)
1 Kun sani, ’yan’uwa, cewa ziyararmu a gare ku ba tă zama a banza ba. 2 Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba. 3 Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba. 4 A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu. 5 Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu. 6 Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu.A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku, 7 amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta. 8 Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu. 9 Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah. 10 Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya. 11 Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa, 12 muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa. 13 Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya. 14 Gama ku, ’yan’uwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu. Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa, 15 waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane 16 suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Al’ummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe. 17 Amma, ’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku. 18 Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu. 19 Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne? 20 Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu.
In Other Versions
1 Thessalonians 2 in the ANGEFD
1 Thessalonians 2 in the ANTPNG2D
1 Thessalonians 2 in the BBPNG
1 Thessalonians 2 in the BBT1E
1 Thessalonians 2 in the BNTABOOT
1 Thessalonians 2 in the BNTLV
1 Thessalonians 2 in the BOATCB
1 Thessalonians 2 in the BOATCB2
1 Thessalonians 2 in the BOBCV
1 Thessalonians 2 in the BOCNT
1 Thessalonians 2 in the BOECS
1 Thessalonians 2 in the BOGWICC
1 Thessalonians 2 in the BOHCV
1 Thessalonians 2 in the BOHLNT
1 Thessalonians 2 in the BOHNTLTAL
1 Thessalonians 2 in the BOICB
1 Thessalonians 2 in the BOILNTAP
1 Thessalonians 2 in the BOITCV
1 Thessalonians 2 in the BOKCV
1 Thessalonians 2 in the BOKCV2
1 Thessalonians 2 in the BOKHWOG
1 Thessalonians 2 in the BOKSSV
1 Thessalonians 2 in the BOLCB
1 Thessalonians 2 in the BOLCB2
1 Thessalonians 2 in the BOMCV
1 Thessalonians 2 in the BONAV
1 Thessalonians 2 in the BONCB
1 Thessalonians 2 in the BONLT
1 Thessalonians 2 in the BONUT2
1 Thessalonians 2 in the BOPLNT
1 Thessalonians 2 in the BOSCB
1 Thessalonians 2 in the BOSNC
1 Thessalonians 2 in the BOTLNT
1 Thessalonians 2 in the BOVCB
1 Thessalonians 2 in the BOYCB
1 Thessalonians 2 in the DGDNT
1 Thessalonians 2 in the GGMNT
1 Thessalonians 2 in the IRVM2
1 Thessalonians 2 in the IRVT2
1 Thessalonians 2 in the KBT1ETNIK
1 Thessalonians 2 in the MKNFD
1 Thessalonians 2 in the MRS1T
1 Thessalonians 2 in the NBVTP
1 Thessalonians 2 in the NIV11
1 Thessalonians 2 in the PDDPT
1 Thessalonians 2 in the SBIAS
1 Thessalonians 2 in the SBIBS
1 Thessalonians 2 in the SBIBS2
1 Thessalonians 2 in the SBICS
1 Thessalonians 2 in the SBIDS
1 Thessalonians 2 in the SBIGS
1 Thessalonians 2 in the SBIHS
1 Thessalonians 2 in the SBIIS
1 Thessalonians 2 in the SBIIS2
1 Thessalonians 2 in the SBIIS3
1 Thessalonians 2 in the SBIKS
1 Thessalonians 2 in the SBIKS2
1 Thessalonians 2 in the SBIMS
1 Thessalonians 2 in the SBIOS
1 Thessalonians 2 in the SBIPS
1 Thessalonians 2 in the SBISS
1 Thessalonians 2 in the SBITS
1 Thessalonians 2 in the SBITS2
1 Thessalonians 2 in the SBITS3
1 Thessalonians 2 in the SBITS4
1 Thessalonians 2 in the SBIUS
1 Thessalonians 2 in the SBIVS
1 Thessalonians 2 in the SBT1E
1 Thessalonians 2 in the SUSU2
1 Thessalonians 2 in the TBIAOTANT
1 Thessalonians 2 in the TBT1E
1 Thessalonians 2 in the TBT1E2
1 Thessalonians 2 in the TFTIP
1 Thessalonians 2 in the TGNTATF3T
1 Thessalonians 2 in the TNTIK
1 Thessalonians 2 in the TNTIL
1 Thessalonians 2 in the TNTIN
1 Thessalonians 2 in the TNTIP
1 Thessalonians 2 in the TNTIZ
1 Thessalonians 2 in the TTENT