2 Corinthians 11 (BOHCB)

1 Ina fata za ku yi haƙuri da ’yar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri. 2 Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa zalla. 3 Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi. 4 Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai. 5 Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba. 6 Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya. 7 Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta? 8 Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima. 9 Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka. 10 Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa. 11 Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku! 12 Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su. 13 Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. 14 Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. 15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu. 16 Ina sāke faɗa, kada wani yă ɗauka ni wawa ne. Amma in kun ɗauke ni haka, to, sai ku karɓe ni kamar yadda kuke karɓan wawa, domin in ɗan in yi taƙama. 17 A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa. 18 Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi. 19 Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna! 20 Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska. 21 Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba!Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne. 22 In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka. 23 In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. 24 Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu. 25 Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. 26 Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya. 27 Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. 28 Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi. 29 Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba? 30 In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina. 31 Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. 32 A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni. 33 Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.

In Other Versions

2 Corinthians 11 in the ANGEFD

2 Corinthians 11 in the ANTPNG2D

2 Corinthians 11 in the AS21

2 Corinthians 11 in the BAGH

2 Corinthians 11 in the BBPNG

2 Corinthians 11 in the BBT1E

2 Corinthians 11 in the BDS

2 Corinthians 11 in the BEV

2 Corinthians 11 in the BHAD

2 Corinthians 11 in the BIB

2 Corinthians 11 in the BLPT

2 Corinthians 11 in the BNT

2 Corinthians 11 in the BNTABOOT

2 Corinthians 11 in the BNTLV

2 Corinthians 11 in the BOATCB

2 Corinthians 11 in the BOATCB2

2 Corinthians 11 in the BOBCV

2 Corinthians 11 in the BOCNT

2 Corinthians 11 in the BOECS

2 Corinthians 11 in the BOGWICC

2 Corinthians 11 in the BOHCV

2 Corinthians 11 in the BOHLNT

2 Corinthians 11 in the BOHNTLTAL

2 Corinthians 11 in the BOICB

2 Corinthians 11 in the BOILNTAP

2 Corinthians 11 in the BOITCV

2 Corinthians 11 in the BOKCV

2 Corinthians 11 in the BOKCV2

2 Corinthians 11 in the BOKHWOG

2 Corinthians 11 in the BOKSSV

2 Corinthians 11 in the BOLCB

2 Corinthians 11 in the BOLCB2

2 Corinthians 11 in the BOMCV

2 Corinthians 11 in the BONAV

2 Corinthians 11 in the BONCB

2 Corinthians 11 in the BONLT

2 Corinthians 11 in the BONUT2

2 Corinthians 11 in the BOPLNT

2 Corinthians 11 in the BOSCB

2 Corinthians 11 in the BOSNC

2 Corinthians 11 in the BOTLNT

2 Corinthians 11 in the BOVCB

2 Corinthians 11 in the BOYCB

2 Corinthians 11 in the BPBB

2 Corinthians 11 in the BPH

2 Corinthians 11 in the BSB

2 Corinthians 11 in the CCB

2 Corinthians 11 in the CUV

2 Corinthians 11 in the CUVS

2 Corinthians 11 in the DBT

2 Corinthians 11 in the DGDNT

2 Corinthians 11 in the DHNT

2 Corinthians 11 in the DNT

2 Corinthians 11 in the ELBE

2 Corinthians 11 in the EMTV

2 Corinthians 11 in the ESV

2 Corinthians 11 in the FBV

2 Corinthians 11 in the FEB

2 Corinthians 11 in the GGMNT

2 Corinthians 11 in the GNT

2 Corinthians 11 in the HARY

2 Corinthians 11 in the HNT

2 Corinthians 11 in the IRVA

2 Corinthians 11 in the IRVB

2 Corinthians 11 in the IRVG

2 Corinthians 11 in the IRVH

2 Corinthians 11 in the IRVK

2 Corinthians 11 in the IRVM

2 Corinthians 11 in the IRVM2

2 Corinthians 11 in the IRVO

2 Corinthians 11 in the IRVP

2 Corinthians 11 in the IRVT

2 Corinthians 11 in the IRVT2

2 Corinthians 11 in the IRVU

2 Corinthians 11 in the ISVN

2 Corinthians 11 in the JSNT

2 Corinthians 11 in the KAPI

2 Corinthians 11 in the KBT1ETNIK

2 Corinthians 11 in the KBV

2 Corinthians 11 in the KJV

2 Corinthians 11 in the KNFD

2 Corinthians 11 in the LBA

2 Corinthians 11 in the LBLA

2 Corinthians 11 in the LNT

2 Corinthians 11 in the LSV

2 Corinthians 11 in the MAAL

2 Corinthians 11 in the MBV

2 Corinthians 11 in the MBV2

2 Corinthians 11 in the MHNT

2 Corinthians 11 in the MKNFD

2 Corinthians 11 in the MNG

2 Corinthians 11 in the MNT

2 Corinthians 11 in the MNT2

2 Corinthians 11 in the MRS1T

2 Corinthians 11 in the NAA

2 Corinthians 11 in the NASB

2 Corinthians 11 in the NBLA

2 Corinthians 11 in the NBS

2 Corinthians 11 in the NBVTP

2 Corinthians 11 in the NET2

2 Corinthians 11 in the NIV11

2 Corinthians 11 in the NNT

2 Corinthians 11 in the NNT2

2 Corinthians 11 in the NNT3

2 Corinthians 11 in the PDDPT

2 Corinthians 11 in the PFNT

2 Corinthians 11 in the RMNT

2 Corinthians 11 in the SBIAS

2 Corinthians 11 in the SBIBS

2 Corinthians 11 in the SBIBS2

2 Corinthians 11 in the SBICS

2 Corinthians 11 in the SBIDS

2 Corinthians 11 in the SBIGS

2 Corinthians 11 in the SBIHS

2 Corinthians 11 in the SBIIS

2 Corinthians 11 in the SBIIS2

2 Corinthians 11 in the SBIIS3

2 Corinthians 11 in the SBIKS

2 Corinthians 11 in the SBIKS2

2 Corinthians 11 in the SBIMS

2 Corinthians 11 in the SBIOS

2 Corinthians 11 in the SBIPS

2 Corinthians 11 in the SBISS

2 Corinthians 11 in the SBITS

2 Corinthians 11 in the SBITS2

2 Corinthians 11 in the SBITS3

2 Corinthians 11 in the SBITS4

2 Corinthians 11 in the SBIUS

2 Corinthians 11 in the SBIVS

2 Corinthians 11 in the SBT

2 Corinthians 11 in the SBT1E

2 Corinthians 11 in the SCHL

2 Corinthians 11 in the SNT

2 Corinthians 11 in the SUSU

2 Corinthians 11 in the SUSU2

2 Corinthians 11 in the SYNO

2 Corinthians 11 in the TBIAOTANT

2 Corinthians 11 in the TBT1E

2 Corinthians 11 in the TBT1E2

2 Corinthians 11 in the TFTIP

2 Corinthians 11 in the TFTU

2 Corinthians 11 in the TGNTATF3T

2 Corinthians 11 in the THAI

2 Corinthians 11 in the TNFD

2 Corinthians 11 in the TNT

2 Corinthians 11 in the TNTIK

2 Corinthians 11 in the TNTIL

2 Corinthians 11 in the TNTIN

2 Corinthians 11 in the TNTIP

2 Corinthians 11 in the TNTIZ

2 Corinthians 11 in the TOMA

2 Corinthians 11 in the TTENT

2 Corinthians 11 in the UBG

2 Corinthians 11 in the UGV

2 Corinthians 11 in the UGV2

2 Corinthians 11 in the UGV3

2 Corinthians 11 in the VBL

2 Corinthians 11 in the VDCC

2 Corinthians 11 in the YALU

2 Corinthians 11 in the YAPE

2 Corinthians 11 in the YBVTP

2 Corinthians 11 in the ZBP