2 Corinthians 4 (BOHCB)

1 Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba. 2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa. 3 Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. 4 Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. 5 Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu. 6 Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi. 7 Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba. 8 A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. 9 An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. 10 Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. 11 Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. 12 Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku. 13 A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana. 14 Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku. 15 Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah. 16 Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. 17 Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. 18 Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.

In Other Versions

2 Corinthians 4 in the ANGEFD

2 Corinthians 4 in the ANTPNG2D

2 Corinthians 4 in the AS21

2 Corinthians 4 in the BAGH

2 Corinthians 4 in the BBPNG

2 Corinthians 4 in the BBT1E

2 Corinthians 4 in the BDS

2 Corinthians 4 in the BEV

2 Corinthians 4 in the BHAD

2 Corinthians 4 in the BIB

2 Corinthians 4 in the BLPT

2 Corinthians 4 in the BNT

2 Corinthians 4 in the BNTABOOT

2 Corinthians 4 in the BNTLV

2 Corinthians 4 in the BOATCB

2 Corinthians 4 in the BOATCB2

2 Corinthians 4 in the BOBCV

2 Corinthians 4 in the BOCNT

2 Corinthians 4 in the BOECS

2 Corinthians 4 in the BOGWICC

2 Corinthians 4 in the BOHCV

2 Corinthians 4 in the BOHLNT

2 Corinthians 4 in the BOHNTLTAL

2 Corinthians 4 in the BOICB

2 Corinthians 4 in the BOILNTAP

2 Corinthians 4 in the BOITCV

2 Corinthians 4 in the BOKCV

2 Corinthians 4 in the BOKCV2

2 Corinthians 4 in the BOKHWOG

2 Corinthians 4 in the BOKSSV

2 Corinthians 4 in the BOLCB

2 Corinthians 4 in the BOLCB2

2 Corinthians 4 in the BOMCV

2 Corinthians 4 in the BONAV

2 Corinthians 4 in the BONCB

2 Corinthians 4 in the BONLT

2 Corinthians 4 in the BONUT2

2 Corinthians 4 in the BOPLNT

2 Corinthians 4 in the BOSCB

2 Corinthians 4 in the BOSNC

2 Corinthians 4 in the BOTLNT

2 Corinthians 4 in the BOVCB

2 Corinthians 4 in the BOYCB

2 Corinthians 4 in the BPBB

2 Corinthians 4 in the BPH

2 Corinthians 4 in the BSB

2 Corinthians 4 in the CCB

2 Corinthians 4 in the CUV

2 Corinthians 4 in the CUVS

2 Corinthians 4 in the DBT

2 Corinthians 4 in the DGDNT

2 Corinthians 4 in the DHNT

2 Corinthians 4 in the DNT

2 Corinthians 4 in the ELBE

2 Corinthians 4 in the EMTV

2 Corinthians 4 in the ESV

2 Corinthians 4 in the FBV

2 Corinthians 4 in the FEB

2 Corinthians 4 in the GGMNT

2 Corinthians 4 in the GNT

2 Corinthians 4 in the HARY

2 Corinthians 4 in the HNT

2 Corinthians 4 in the IRVA

2 Corinthians 4 in the IRVB

2 Corinthians 4 in the IRVG

2 Corinthians 4 in the IRVH

2 Corinthians 4 in the IRVK

2 Corinthians 4 in the IRVM

2 Corinthians 4 in the IRVM2

2 Corinthians 4 in the IRVO

2 Corinthians 4 in the IRVP

2 Corinthians 4 in the IRVT

2 Corinthians 4 in the IRVT2

2 Corinthians 4 in the IRVU

2 Corinthians 4 in the ISVN

2 Corinthians 4 in the JSNT

2 Corinthians 4 in the KAPI

2 Corinthians 4 in the KBT1ETNIK

2 Corinthians 4 in the KBV

2 Corinthians 4 in the KJV

2 Corinthians 4 in the KNFD

2 Corinthians 4 in the LBA

2 Corinthians 4 in the LBLA

2 Corinthians 4 in the LNT

2 Corinthians 4 in the LSV

2 Corinthians 4 in the MAAL

2 Corinthians 4 in the MBV

2 Corinthians 4 in the MBV2

2 Corinthians 4 in the MHNT

2 Corinthians 4 in the MKNFD

2 Corinthians 4 in the MNG

2 Corinthians 4 in the MNT

2 Corinthians 4 in the MNT2

2 Corinthians 4 in the MRS1T

2 Corinthians 4 in the NAA

2 Corinthians 4 in the NASB

2 Corinthians 4 in the NBLA

2 Corinthians 4 in the NBS

2 Corinthians 4 in the NBVTP

2 Corinthians 4 in the NET2

2 Corinthians 4 in the NIV11

2 Corinthians 4 in the NNT

2 Corinthians 4 in the NNT2

2 Corinthians 4 in the NNT3

2 Corinthians 4 in the PDDPT

2 Corinthians 4 in the PFNT

2 Corinthians 4 in the RMNT

2 Corinthians 4 in the SBIAS

2 Corinthians 4 in the SBIBS

2 Corinthians 4 in the SBIBS2

2 Corinthians 4 in the SBICS

2 Corinthians 4 in the SBIDS

2 Corinthians 4 in the SBIGS

2 Corinthians 4 in the SBIHS

2 Corinthians 4 in the SBIIS

2 Corinthians 4 in the SBIIS2

2 Corinthians 4 in the SBIIS3

2 Corinthians 4 in the SBIKS

2 Corinthians 4 in the SBIKS2

2 Corinthians 4 in the SBIMS

2 Corinthians 4 in the SBIOS

2 Corinthians 4 in the SBIPS

2 Corinthians 4 in the SBISS

2 Corinthians 4 in the SBITS

2 Corinthians 4 in the SBITS2

2 Corinthians 4 in the SBITS3

2 Corinthians 4 in the SBITS4

2 Corinthians 4 in the SBIUS

2 Corinthians 4 in the SBIVS

2 Corinthians 4 in the SBT

2 Corinthians 4 in the SBT1E

2 Corinthians 4 in the SCHL

2 Corinthians 4 in the SNT

2 Corinthians 4 in the SUSU

2 Corinthians 4 in the SUSU2

2 Corinthians 4 in the SYNO

2 Corinthians 4 in the TBIAOTANT

2 Corinthians 4 in the TBT1E

2 Corinthians 4 in the TBT1E2

2 Corinthians 4 in the TFTIP

2 Corinthians 4 in the TFTU

2 Corinthians 4 in the TGNTATF3T

2 Corinthians 4 in the THAI

2 Corinthians 4 in the TNFD

2 Corinthians 4 in the TNT

2 Corinthians 4 in the TNTIK

2 Corinthians 4 in the TNTIL

2 Corinthians 4 in the TNTIN

2 Corinthians 4 in the TNTIP

2 Corinthians 4 in the TNTIZ

2 Corinthians 4 in the TOMA

2 Corinthians 4 in the TTENT

2 Corinthians 4 in the UBG

2 Corinthians 4 in the UGV

2 Corinthians 4 in the UGV2

2 Corinthians 4 in the UGV3

2 Corinthians 4 in the VBL

2 Corinthians 4 in the VDCC

2 Corinthians 4 in the YALU

2 Corinthians 4 in the YAPE

2 Corinthians 4 in the YBVTP

2 Corinthians 4 in the ZBP