2 Peter 1 (BOHCB)

1 Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga waɗanda ta wurin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi sun sami bangaskiya mai daraja irin tamu. 2 Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu. 3 Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa. 4 Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa. 5 Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; 6 ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; 7 ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. 8 Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9 Amma in wani ba shi da su, ba shi da hangen nesa ke nan kuma makaho ne, ya kuma manta cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā. 10 Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba, 11 za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. 12 Saboda haka kullum zan tuna muku da waɗannan, ko da yake kun sansu kun kuma kahu ƙwarai cikin gaskiyar da kuke da ita yanzu. 13 A ganina ya dace in tunashe ku muddin ina raye cikin tentin wannan jiki, 14 domin na sani na kusa in ajiye shi a gefe, yadda Ubangijinmu Yesu Kiristi ya nuna mini a sarari. 15 Zan kuwa yi iyakacin ƙoƙari in ga cewa bayan rabuwata kullum za ku iya tuna da waɗannan abubuwa. 16 Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo sa’ad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido. 17 Gama ya sami girma da ɗaukaka daga Allah Uba sa’ad da murya ta zo masa daga Mafificiyar Ɗaukaka cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; da shi nake jin daɗi ƙwarai.” 18 Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama sa’ad da muke tare da shi a kan dutse mai tsarki. 19 Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku. 20 Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa. 21 Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

In Other Versions

2 Peter 1 in the ANGEFD

2 Peter 1 in the ANTPNG2D

2 Peter 1 in the AS21

2 Peter 1 in the BAGH

2 Peter 1 in the BBPNG

2 Peter 1 in the BBT1E

2 Peter 1 in the BDS

2 Peter 1 in the BEV

2 Peter 1 in the BHAD

2 Peter 1 in the BIB

2 Peter 1 in the BLPT

2 Peter 1 in the BNT

2 Peter 1 in the BNTABOOT

2 Peter 1 in the BNTLV

2 Peter 1 in the BOATCB

2 Peter 1 in the BOATCB2

2 Peter 1 in the BOBCV

2 Peter 1 in the BOCNT

2 Peter 1 in the BOECS

2 Peter 1 in the BOGWICC

2 Peter 1 in the BOHCV

2 Peter 1 in the BOHLNT

2 Peter 1 in the BOHNTLTAL

2 Peter 1 in the BOICB

2 Peter 1 in the BOILNTAP

2 Peter 1 in the BOITCV

2 Peter 1 in the BOKCV

2 Peter 1 in the BOKCV2

2 Peter 1 in the BOKHWOG

2 Peter 1 in the BOKSSV

2 Peter 1 in the BOLCB

2 Peter 1 in the BOLCB2

2 Peter 1 in the BOMCV

2 Peter 1 in the BONAV

2 Peter 1 in the BONCB

2 Peter 1 in the BONLT

2 Peter 1 in the BONUT2

2 Peter 1 in the BOPLNT

2 Peter 1 in the BOSCB

2 Peter 1 in the BOSNC

2 Peter 1 in the BOTLNT

2 Peter 1 in the BOVCB

2 Peter 1 in the BOYCB

2 Peter 1 in the BPBB

2 Peter 1 in the BPH

2 Peter 1 in the BSB

2 Peter 1 in the CCB

2 Peter 1 in the CUV

2 Peter 1 in the CUVS

2 Peter 1 in the DBT

2 Peter 1 in the DGDNT

2 Peter 1 in the DHNT

2 Peter 1 in the DNT

2 Peter 1 in the ELBE

2 Peter 1 in the EMTV

2 Peter 1 in the ESV

2 Peter 1 in the FBV

2 Peter 1 in the FEB

2 Peter 1 in the GGMNT

2 Peter 1 in the GNT

2 Peter 1 in the HARY

2 Peter 1 in the HNT

2 Peter 1 in the IRVA

2 Peter 1 in the IRVB

2 Peter 1 in the IRVG

2 Peter 1 in the IRVH

2 Peter 1 in the IRVK

2 Peter 1 in the IRVM

2 Peter 1 in the IRVM2

2 Peter 1 in the IRVO

2 Peter 1 in the IRVP

2 Peter 1 in the IRVT

2 Peter 1 in the IRVT2

2 Peter 1 in the IRVU

2 Peter 1 in the ISVN

2 Peter 1 in the JSNT

2 Peter 1 in the KAPI

2 Peter 1 in the KBT1ETNIK

2 Peter 1 in the KBV

2 Peter 1 in the KJV

2 Peter 1 in the KNFD

2 Peter 1 in the LBA

2 Peter 1 in the LBLA

2 Peter 1 in the LNT

2 Peter 1 in the LSV

2 Peter 1 in the MAAL

2 Peter 1 in the MBV

2 Peter 1 in the MBV2

2 Peter 1 in the MHNT

2 Peter 1 in the MKNFD

2 Peter 1 in the MNG

2 Peter 1 in the MNT

2 Peter 1 in the MNT2

2 Peter 1 in the MRS1T

2 Peter 1 in the NAA

2 Peter 1 in the NASB

2 Peter 1 in the NBLA

2 Peter 1 in the NBS

2 Peter 1 in the NBVTP

2 Peter 1 in the NET2

2 Peter 1 in the NIV11

2 Peter 1 in the NNT

2 Peter 1 in the NNT2

2 Peter 1 in the NNT3

2 Peter 1 in the PDDPT

2 Peter 1 in the PFNT

2 Peter 1 in the RMNT

2 Peter 1 in the SBIAS

2 Peter 1 in the SBIBS

2 Peter 1 in the SBIBS2

2 Peter 1 in the SBICS

2 Peter 1 in the SBIDS

2 Peter 1 in the SBIGS

2 Peter 1 in the SBIHS

2 Peter 1 in the SBIIS

2 Peter 1 in the SBIIS2

2 Peter 1 in the SBIIS3

2 Peter 1 in the SBIKS

2 Peter 1 in the SBIKS2

2 Peter 1 in the SBIMS

2 Peter 1 in the SBIOS

2 Peter 1 in the SBIPS

2 Peter 1 in the SBISS

2 Peter 1 in the SBITS

2 Peter 1 in the SBITS2

2 Peter 1 in the SBITS3

2 Peter 1 in the SBITS4

2 Peter 1 in the SBIUS

2 Peter 1 in the SBIVS

2 Peter 1 in the SBT

2 Peter 1 in the SBT1E

2 Peter 1 in the SCHL

2 Peter 1 in the SNT

2 Peter 1 in the SUSU

2 Peter 1 in the SUSU2

2 Peter 1 in the SYNO

2 Peter 1 in the TBIAOTANT

2 Peter 1 in the TBT1E

2 Peter 1 in the TBT1E2

2 Peter 1 in the TFTIP

2 Peter 1 in the TFTU

2 Peter 1 in the TGNTATF3T

2 Peter 1 in the THAI

2 Peter 1 in the TNFD

2 Peter 1 in the TNT

2 Peter 1 in the TNTIK

2 Peter 1 in the TNTIL

2 Peter 1 in the TNTIN

2 Peter 1 in the TNTIP

2 Peter 1 in the TNTIZ

2 Peter 1 in the TOMA

2 Peter 1 in the TTENT

2 Peter 1 in the UBG

2 Peter 1 in the UGV

2 Peter 1 in the UGV2

2 Peter 1 in the UGV3

2 Peter 1 in the VBL

2 Peter 1 in the VDCC

2 Peter 1 in the YALU

2 Peter 1 in the YAPE

2 Peter 1 in the YBVTP

2 Peter 1 in the ZBP