2 Timothy 2 (BOHCB)
1 Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu. 2 Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu. 3 Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu. 4 Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja. 5 Haka ma, in wani ya yi gasa a matsayi shi ɗan wasa ne, ba ya sami rawanin nasara, sai in ya yi gasar bisa ga dokoki. 6 Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona. 7 Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan. 8 Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata, 9 wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba. 10 Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka. 11 Ga wata magana tabbatacciya,“In muka mutu tare da shi,za mu rayu tare da shi; 12 in muka jimre,za mu yi mulki tare da shi.In muka yi mūsunsa,shi ma zai yi mūsunmu; 13 in ba mu da aminci,shi dai mai aminci ne,domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.” 14 Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi. 15 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai. 16 Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah. 17 Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus, 18 waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu. 19 Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu, “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yă yi nesa da aikata mugunta.” 20 A babban gida akwai kayayyakin da ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma har da na katako da na yumɓu ma; waɗansu domin hidima mai daraja waɗansu kuwa domin hidima marar daraja. 21 In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau. 22 Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta. 23 Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa. 24 Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma. 25 Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya, 26 su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa.
In Other Versions
2 Timothy 2 in the ANGEFD
2 Timothy 2 in the ANTPNG2D
2 Timothy 2 in the AS21
2 Timothy 2 in the BAGH
2 Timothy 2 in the BBPNG
2 Timothy 2 in the BBT1E
2 Timothy 2 in the BDS
2 Timothy 2 in the BEV
2 Timothy 2 in the BHAD
2 Timothy 2 in the BIB
2 Timothy 2 in the BLPT
2 Timothy 2 in the BNT
2 Timothy 2 in the BNTABOOT
2 Timothy 2 in the BNTLV
2 Timothy 2 in the BOATCB
2 Timothy 2 in the BOATCB2
2 Timothy 2 in the BOBCV
2 Timothy 2 in the BOCNT
2 Timothy 2 in the BOECS
2 Timothy 2 in the BOGWICC
2 Timothy 2 in the BOHCV
2 Timothy 2 in the BOHLNT
2 Timothy 2 in the BOHNTLTAL
2 Timothy 2 in the BOICB
2 Timothy 2 in the BOILNTAP
2 Timothy 2 in the BOITCV
2 Timothy 2 in the BOKCV
2 Timothy 2 in the BOKCV2
2 Timothy 2 in the BOKHWOG
2 Timothy 2 in the BOKSSV
2 Timothy 2 in the BOLCB
2 Timothy 2 in the BOLCB2
2 Timothy 2 in the BOMCV
2 Timothy 2 in the BONAV
2 Timothy 2 in the BONCB
2 Timothy 2 in the BONLT
2 Timothy 2 in the BONUT2
2 Timothy 2 in the BOPLNT
2 Timothy 2 in the BOSCB
2 Timothy 2 in the BOSNC
2 Timothy 2 in the BOTLNT
2 Timothy 2 in the BOVCB
2 Timothy 2 in the BOYCB
2 Timothy 2 in the BPBB
2 Timothy 2 in the BPH
2 Timothy 2 in the BSB
2 Timothy 2 in the CCB
2 Timothy 2 in the CUV
2 Timothy 2 in the CUVS
2 Timothy 2 in the DBT
2 Timothy 2 in the DGDNT
2 Timothy 2 in the DHNT
2 Timothy 2 in the DNT
2 Timothy 2 in the ELBE
2 Timothy 2 in the EMTV
2 Timothy 2 in the ESV
2 Timothy 2 in the FBV
2 Timothy 2 in the FEB
2 Timothy 2 in the GGMNT
2 Timothy 2 in the GNT
2 Timothy 2 in the HARY
2 Timothy 2 in the HNT
2 Timothy 2 in the IRVA
2 Timothy 2 in the IRVB
2 Timothy 2 in the IRVG
2 Timothy 2 in the IRVH
2 Timothy 2 in the IRVK
2 Timothy 2 in the IRVM
2 Timothy 2 in the IRVM2
2 Timothy 2 in the IRVO
2 Timothy 2 in the IRVP
2 Timothy 2 in the IRVT
2 Timothy 2 in the IRVT2
2 Timothy 2 in the IRVU
2 Timothy 2 in the ISVN
2 Timothy 2 in the JSNT
2 Timothy 2 in the KAPI
2 Timothy 2 in the KBT1ETNIK
2 Timothy 2 in the KBV
2 Timothy 2 in the KJV
2 Timothy 2 in the KNFD
2 Timothy 2 in the LBA
2 Timothy 2 in the LBLA
2 Timothy 2 in the LNT
2 Timothy 2 in the LSV
2 Timothy 2 in the MAAL
2 Timothy 2 in the MBV
2 Timothy 2 in the MBV2
2 Timothy 2 in the MHNT
2 Timothy 2 in the MKNFD
2 Timothy 2 in the MNG
2 Timothy 2 in the MNT
2 Timothy 2 in the MNT2
2 Timothy 2 in the MRS1T
2 Timothy 2 in the NAA
2 Timothy 2 in the NASB
2 Timothy 2 in the NBLA
2 Timothy 2 in the NBS
2 Timothy 2 in the NBVTP
2 Timothy 2 in the NET2
2 Timothy 2 in the NIV11
2 Timothy 2 in the NNT
2 Timothy 2 in the NNT2
2 Timothy 2 in the NNT3
2 Timothy 2 in the PDDPT
2 Timothy 2 in the PFNT
2 Timothy 2 in the RMNT
2 Timothy 2 in the SBIAS
2 Timothy 2 in the SBIBS
2 Timothy 2 in the SBIBS2
2 Timothy 2 in the SBICS
2 Timothy 2 in the SBIDS
2 Timothy 2 in the SBIGS
2 Timothy 2 in the SBIHS
2 Timothy 2 in the SBIIS
2 Timothy 2 in the SBIIS2
2 Timothy 2 in the SBIIS3
2 Timothy 2 in the SBIKS
2 Timothy 2 in the SBIKS2
2 Timothy 2 in the SBIMS
2 Timothy 2 in the SBIOS
2 Timothy 2 in the SBIPS
2 Timothy 2 in the SBISS
2 Timothy 2 in the SBITS
2 Timothy 2 in the SBITS2
2 Timothy 2 in the SBITS3
2 Timothy 2 in the SBITS4
2 Timothy 2 in the SBIUS
2 Timothy 2 in the SBIVS
2 Timothy 2 in the SBT
2 Timothy 2 in the SBT1E
2 Timothy 2 in the SCHL
2 Timothy 2 in the SNT
2 Timothy 2 in the SUSU
2 Timothy 2 in the SUSU2
2 Timothy 2 in the SYNO
2 Timothy 2 in the TBIAOTANT
2 Timothy 2 in the TBT1E
2 Timothy 2 in the TBT1E2
2 Timothy 2 in the TFTIP
2 Timothy 2 in the TFTU
2 Timothy 2 in the TGNTATF3T
2 Timothy 2 in the THAI
2 Timothy 2 in the TNFD
2 Timothy 2 in the TNT
2 Timothy 2 in the TNTIK
2 Timothy 2 in the TNTIL
2 Timothy 2 in the TNTIN
2 Timothy 2 in the TNTIP
2 Timothy 2 in the TNTIZ
2 Timothy 2 in the TOMA
2 Timothy 2 in the TTENT
2 Timothy 2 in the UBG
2 Timothy 2 in the UGV
2 Timothy 2 in the UGV2
2 Timothy 2 in the UGV3
2 Timothy 2 in the VBL
2 Timothy 2 in the VDCC
2 Timothy 2 in the YALU
2 Timothy 2 in the YAPE
2 Timothy 2 in the YBVTP
2 Timothy 2 in the ZBP