Acts 27 (BOHCB)

1 Sa’ad da aka yanke shawara cewa za mu tashi a jirgin ruwa zuwa Italiya, sai aka danƙa Bulus da waɗansu ’yan kurkuku a hannun wani jarumin mai suna Juliyos, wanda yake na Bataliyar Babban Sarki. 2 Muka shiga jirgin ruwa daga Andiramitiyum wanda yake shirin tashi zuwa tasoshin da suke bakin tekun lardin Asiya, sai muka kama tafiya. Aristarkus, mutumin Makidoniya daga Tessalonika, yana tare da mu. 3 Kashegari muka sauka a Sidon; Juliyos kuwa, cikin alheri ga Bulus, ya bar shi yă je wajen abokansa domin su biya masa bukatunsa. 4 Daga can kuma muka sāke kama tafiya muka zaga ta bayan tsibirin Saifurus saboda iska tana gāba da mu. 5 Sa’ad da muka ƙetare tekun da yake sassan gaɓar Silisiya da Famfiliya sai muka sauka a Mira ta Lisiya. 6 A can jarumin ya sami wani jirgin ruwan Alekzandariyan da za shi Italiya sai ya sa mu a ciki. 7 Tafiyar ta ɗauki kwanaki da yawa muna yi kaɗan-kaɗan da ƙyar muka iso kusa da gaɓar Kinidus. Da iskar ta hana mu ci gaba, sai muka bi ta bayan tsibirin Kirit ɗaura da Salmone. 8 Muka ci gaba a gefen gaɓar da ƙyar har muka iso wani wurin da ake kira Kyakkyawan Mafaka, kusa da garin Laseya. 9 An riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya kuwa ta riga ta zama da hatsari domin a lokacin Azumi ya riga ta wuce. Saboda haka Bulus ya gargaɗe su, 10 ya ce, “Mutane, ina gani tafiyarmu za tă zama da masifa ta kuma kawo babbar hasara ga jirgin ruwan da kaya, da kuma ga rayukanmu ma.” 11 Amma jarumin, a maimakon ya saurari abin da Bulus ya ce, sai ya bi shawarar matuƙi da kuma mai jirgin ruwan. 12 Da yake tashar jirgin ruwan ba tă dace a ci damina a can ba, yawanci suka ba yanke shawara cewa mu ci gaba da tafiya, da bege za mu kai Funis mu ci damina a can. Wannan tashar jirgin ruwa ne a Kirit, tana fuskantar kudu maso yamma da kuma arewa maso yamma. 13 Da iska ta fara busowa daga kudu a hankali, sai suka yi tsammani sun sami abin da suke nema; saboda haka suka janye ƙugiyar jirgin ruwa suka bi ta gefen tsibirin Kirit. 14 Ba a jima ba, sai ga wata guguwar iska mai ƙarfin da ake kira “’Yar arewa maso gabas,” ta buga daga tsibirin. 15 Iskar ta ci ƙarfin jirgin ruwan har ya kāsa fuskantar iskar; saboda haka muka sallamar mata tă yi ta tura mu. 16 Da muka bi ta bayan wani ɗan tsibirin da ake kira Kauda, da ƙyar muka jawo ɗan ƙaramin jirgin kusa da jirgin. 17 Da mutanen suka jawo shi cikin babban jirgin ruwan, sai suka sa igiyoyi ta ƙarƙashin jirgin ruwan kanta don su ɗaɗɗaura shi. Don gudun kada a fyaɗa mu da yashin gaɓar Sirtis, sai suka saukar da ƙugiyar jirgin ruwan, suka bari aka yi ta tura jirgin haka. 18 Haka muka yi ta shan bugun guguwar hadarin nan kashegari suka fara jajjefar da kayan da jirgin yake ɗauke da su a cikin teku. 19 A rana ta uku, da hannuwansu suka jefar da kayan aikin jirgin ruwan a cikin teku. 20 Da dai aka yi kwana da kwanaki ba a ga rana ko taurari ba guguwar iska kuma ta ci gaba da bugowa, a ƙarshe muka fid da zuciya za mu tsira. 21 Bayan mutanen sun daɗe ba su ci abinci ba, Bulus ya miƙe tsaye a gabansu ya ce, “Mutane, da kun ji shawarata na kada ku tashi daga Kirit, da ba ku fāɗa wannan masifa da hasara ba. 22 Amma yanzu ina ƙarfafa ku ku yi ƙarfin hali, domin ba ɗayanku da zai rasa ransa; jirgin ruwan ne kaɗai zai hallaka. 23 Jiya da dare wani mala’ikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni 24 ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lalle za ka tsaya a gaban Kaisar a yi maka shari’a; Allah kuma cikin alherinsa ya ba ka dukan rayukan mutanen da suke tafiya tare da kai.’ 25 Saboda haka ku yi ƙarfin hali, ku jama’a, gama gaskata Allah a kan cewa yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka zai faru. 26 Duk da haka, dole a fyaɗa mu a wani tsibiri.” 27 A dare na goma sha huɗu iska dai tana ta korarmu a Tekun Adiriyatik, wajen tsakar dare sai masu tuƙin jirgin suka zaci sun yi kusa da ƙasa. 28 Sai suka gwada zurfin ruwan suka ga ya kai ƙafa ɗari da ashirin. Bayan ɗan lokaci kaɗan suka sāke gwadawa suka ga zurfin ya kai ƙafa tasa’in. 29 Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki ƙugiyoyin jirgin guda huɗu daga bayan jirgin suka yi fata gari ya waye. 30 Cikin ƙoƙarin tserewa daga jirgin, sai masu tuƙin jirgin suka saukar da ɗan ƙaramin jirgin ruwan cikin tekun, suka yi kamar za su saki waɗansu ƙugiyoyi daga sashen gaba na babban jirgin ne. 31 Sai Bulus ya ce wa jarumin da kuma sojojin, “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba za ku tsira ba.” 32 Sai sojojin suka yayyanke igiyoyin da suke riƙe da ɗan ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa. 33 Kafin gari ya waye Bulus ya roƙe su duka su ci abinci. Ya ce, “Kwana goma sha huɗu ke nan, kuna zama cikin zulumi kun kuma kasance ba abinci, ba ku ci kome ba. 34 Ina roƙonku yanzu ku ci abinci. Kuna bukatarsa don ku rayu. Ba ɗayanku da zai rasa ko gashin kansa guda ɗaya.” 35 Bayan da ya faɗi haka, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya ga Allah a gabansu duka. Sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci. 36 Dukansu kuwa suka sami ƙarfafawa, suka kuma ci abinci. 37 Dukanmu a jirgin kuwa mutane 276 ne. 38 Sa’ad da suka ci iyakar abin da suke so, sai suka rage nauyin jirgin ta wurin zubar da hatsin a cikin tekun. 39 Da gari ya waye, ba su gane ƙasar da suke ba, amma suka ga wani lungu da gaci mai yashi, sai suka yanke shawara su kai jirgin can in za su iya. 40 Da suka yanke ƙugiyoyin, sai suka bar su a cikin teku a lokaci guda kuma suka ɓalle maɗaurin abin juya jirgin. Sai suka tā da filafilan gaban jirgin daidai yadda iska za tă tura shi gaba, sa’an nan suka nufi gaci. 41 Amma jirgin ruwan ya shiga yashi ya kafe. Kan jirgin ya shiga cikin yashin ya kāsa motsi, sai jirgin ya fara farfashewa ta baya saboda haukan raƙuman ruwa. 42 Sojojin suka yi niyya su kakkashe ’yan kurkukun don hana waninsu yă yi iyo yă tsere. 43 Amma jarumin ya so yă ceci ran Bulus, sai ya hana su aiwatar da niyyarsu. Ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci. 44 Sauran kuma su bi katakai zuwa can ko kuma a kan tarkacen jirgin ruwan. Ta haka kowa ya kai bakin teku lafiya.

In Other Versions

Acts 27 in the ANGEFD

Acts 27 in the ANTPNG2D

Acts 27 in the AS21

Acts 27 in the BAGH

Acts 27 in the BBPNG

Acts 27 in the BBT1E

Acts 27 in the BDS

Acts 27 in the BEV

Acts 27 in the BHAD

Acts 27 in the BIB

Acts 27 in the BLPT

Acts 27 in the BNT

Acts 27 in the BNTABOOT

Acts 27 in the BNTLV

Acts 27 in the BOATCB

Acts 27 in the BOATCB2

Acts 27 in the BOBCV

Acts 27 in the BOCNT

Acts 27 in the BOECS

Acts 27 in the BOGWICC

Acts 27 in the BOHCV

Acts 27 in the BOHLNT

Acts 27 in the BOHNTLTAL

Acts 27 in the BOICB

Acts 27 in the BOILNTAP

Acts 27 in the BOITCV

Acts 27 in the BOKCV

Acts 27 in the BOKCV2

Acts 27 in the BOKHWOG

Acts 27 in the BOKSSV

Acts 27 in the BOLCB

Acts 27 in the BOLCB2

Acts 27 in the BOMCV

Acts 27 in the BONAV

Acts 27 in the BONCB

Acts 27 in the BONLT

Acts 27 in the BONUT2

Acts 27 in the BOPLNT

Acts 27 in the BOSCB

Acts 27 in the BOSNC

Acts 27 in the BOTLNT

Acts 27 in the BOVCB

Acts 27 in the BOYCB

Acts 27 in the BPBB

Acts 27 in the BPH

Acts 27 in the BSB

Acts 27 in the CCB

Acts 27 in the CUV

Acts 27 in the CUVS

Acts 27 in the DBT

Acts 27 in the DGDNT

Acts 27 in the DHNT

Acts 27 in the DNT

Acts 27 in the ELBE

Acts 27 in the EMTV

Acts 27 in the ESV

Acts 27 in the FBV

Acts 27 in the FEB

Acts 27 in the GGMNT

Acts 27 in the GNT

Acts 27 in the HARY

Acts 27 in the HNT

Acts 27 in the IRVA

Acts 27 in the IRVB

Acts 27 in the IRVG

Acts 27 in the IRVH

Acts 27 in the IRVK

Acts 27 in the IRVM

Acts 27 in the IRVM2

Acts 27 in the IRVO

Acts 27 in the IRVP

Acts 27 in the IRVT

Acts 27 in the IRVT2

Acts 27 in the IRVU

Acts 27 in the ISVN

Acts 27 in the JSNT

Acts 27 in the KAPI

Acts 27 in the KBT1ETNIK

Acts 27 in the KBV

Acts 27 in the KJV

Acts 27 in the KNFD

Acts 27 in the LBA

Acts 27 in the LBLA

Acts 27 in the LNT

Acts 27 in the LSV

Acts 27 in the MAAL

Acts 27 in the MBV

Acts 27 in the MBV2

Acts 27 in the MHNT

Acts 27 in the MKNFD

Acts 27 in the MNG

Acts 27 in the MNT

Acts 27 in the MNT2

Acts 27 in the MRS1T

Acts 27 in the NAA

Acts 27 in the NASB

Acts 27 in the NBLA

Acts 27 in the NBS

Acts 27 in the NBVTP

Acts 27 in the NET2

Acts 27 in the NIV11

Acts 27 in the NNT

Acts 27 in the NNT2

Acts 27 in the NNT3

Acts 27 in the PDDPT

Acts 27 in the PFNT

Acts 27 in the RMNT

Acts 27 in the SBIAS

Acts 27 in the SBIBS

Acts 27 in the SBIBS2

Acts 27 in the SBICS

Acts 27 in the SBIDS

Acts 27 in the SBIGS

Acts 27 in the SBIHS

Acts 27 in the SBIIS

Acts 27 in the SBIIS2

Acts 27 in the SBIIS3

Acts 27 in the SBIKS

Acts 27 in the SBIKS2

Acts 27 in the SBIMS

Acts 27 in the SBIOS

Acts 27 in the SBIPS

Acts 27 in the SBISS

Acts 27 in the SBITS

Acts 27 in the SBITS2

Acts 27 in the SBITS3

Acts 27 in the SBITS4

Acts 27 in the SBIUS

Acts 27 in the SBIVS

Acts 27 in the SBT

Acts 27 in the SBT1E

Acts 27 in the SCHL

Acts 27 in the SNT

Acts 27 in the SUSU

Acts 27 in the SUSU2

Acts 27 in the SYNO

Acts 27 in the TBIAOTANT

Acts 27 in the TBT1E

Acts 27 in the TBT1E2

Acts 27 in the TFTIP

Acts 27 in the TFTU

Acts 27 in the TGNTATF3T

Acts 27 in the THAI

Acts 27 in the TNFD

Acts 27 in the TNT

Acts 27 in the TNTIK

Acts 27 in the TNTIL

Acts 27 in the TNTIN

Acts 27 in the TNTIP

Acts 27 in the TNTIZ

Acts 27 in the TOMA

Acts 27 in the TTENT

Acts 27 in the UBG

Acts 27 in the UGV

Acts 27 in the UGV2

Acts 27 in the UGV3

Acts 27 in the VBL

Acts 27 in the VDCC

Acts 27 in the YALU

Acts 27 in the YAPE

Acts 27 in the YBVTP

Acts 27 in the ZBP