Galatians 2 (BOHCB)
1 Bayan shekara goma sha huɗu sai na sāke haurawa zuwa Urushalima, a wannan lokaci na tafi tare da Barnabas. Na kuma ɗauki Titus muka tafi tare. 2 Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Da na kai can, sai na bayyana musu bisharar da nake wa’azi a cikin Al’ummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yă zama a banza. 3 Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi mutumin Al’ummai ne. 4 Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu ’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi. 5 Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku. 6 Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba. 7 A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai, kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa. 8 Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai. 9 Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa. 10 Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi. 11 Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake. 12 Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Al’ummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Al’ummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya. 13 Sauran Yahudawa suka haɗa kai da shi a munafuncinsa har Barnabas ma ya bauɗe. 14 Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa? 15 “Mu da muke Yahudawa ta wurin haihuwa ba Al’ummai masu zunubi ba, 16 mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka. 17 “In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Kiristi, sa’an nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Kiristi yana ƙarfafa zunubi ke nan? A’a, ko kusa! 18 In na sāke gina abin da na rushe, na zama mai karyar Doka ke nan. 19 “Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah. 20 An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina. 21 Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!”
In Other Versions
Galatians 2 in the ANGEFD
Galatians 2 in the ANTPNG2D
Galatians 2 in the AS21
Galatians 2 in the BAGH
Galatians 2 in the BBPNG
Galatians 2 in the BBT1E
Galatians 2 in the BDS
Galatians 2 in the BEV
Galatians 2 in the BHAD
Galatians 2 in the BIB
Galatians 2 in the BLPT
Galatians 2 in the BNT
Galatians 2 in the BNTABOOT
Galatians 2 in the BNTLV
Galatians 2 in the BOATCB
Galatians 2 in the BOATCB2
Galatians 2 in the BOBCV
Galatians 2 in the BOCNT
Galatians 2 in the BOECS
Galatians 2 in the BOGWICC
Galatians 2 in the BOHCV
Galatians 2 in the BOHLNT
Galatians 2 in the BOHNTLTAL
Galatians 2 in the BOICB
Galatians 2 in the BOILNTAP
Galatians 2 in the BOITCV
Galatians 2 in the BOKCV
Galatians 2 in the BOKCV2
Galatians 2 in the BOKHWOG
Galatians 2 in the BOKSSV
Galatians 2 in the BOLCB
Galatians 2 in the BOLCB2
Galatians 2 in the BOMCV
Galatians 2 in the BONAV
Galatians 2 in the BONCB
Galatians 2 in the BONLT
Galatians 2 in the BONUT2
Galatians 2 in the BOPLNT
Galatians 2 in the BOSCB
Galatians 2 in the BOSNC
Galatians 2 in the BOTLNT
Galatians 2 in the BOVCB
Galatians 2 in the BOYCB
Galatians 2 in the BPBB
Galatians 2 in the BPH
Galatians 2 in the BSB
Galatians 2 in the CCB
Galatians 2 in the CUV
Galatians 2 in the CUVS
Galatians 2 in the DBT
Galatians 2 in the DGDNT
Galatians 2 in the DHNT
Galatians 2 in the DNT
Galatians 2 in the ELBE
Galatians 2 in the EMTV
Galatians 2 in the ESV
Galatians 2 in the FBV
Galatians 2 in the FEB
Galatians 2 in the GGMNT
Galatians 2 in the GNT
Galatians 2 in the HARY
Galatians 2 in the HNT
Galatians 2 in the IRVA
Galatians 2 in the IRVB
Galatians 2 in the IRVG
Galatians 2 in the IRVH
Galatians 2 in the IRVK
Galatians 2 in the IRVM
Galatians 2 in the IRVM2
Galatians 2 in the IRVO
Galatians 2 in the IRVP
Galatians 2 in the IRVT
Galatians 2 in the IRVT2
Galatians 2 in the IRVU
Galatians 2 in the ISVN
Galatians 2 in the JSNT
Galatians 2 in the KAPI
Galatians 2 in the KBT1ETNIK
Galatians 2 in the KBV
Galatians 2 in the KJV
Galatians 2 in the KNFD
Galatians 2 in the LBA
Galatians 2 in the LBLA
Galatians 2 in the LNT
Galatians 2 in the LSV
Galatians 2 in the MAAL
Galatians 2 in the MBV
Galatians 2 in the MBV2
Galatians 2 in the MHNT
Galatians 2 in the MKNFD
Galatians 2 in the MNG
Galatians 2 in the MNT
Galatians 2 in the MNT2
Galatians 2 in the MRS1T
Galatians 2 in the NAA
Galatians 2 in the NASB
Galatians 2 in the NBLA
Galatians 2 in the NBS
Galatians 2 in the NBVTP
Galatians 2 in the NET2
Galatians 2 in the NIV11
Galatians 2 in the NNT
Galatians 2 in the NNT2
Galatians 2 in the NNT3
Galatians 2 in the PDDPT
Galatians 2 in the PFNT
Galatians 2 in the RMNT
Galatians 2 in the SBIAS
Galatians 2 in the SBIBS
Galatians 2 in the SBIBS2
Galatians 2 in the SBICS
Galatians 2 in the SBIDS
Galatians 2 in the SBIGS
Galatians 2 in the SBIHS
Galatians 2 in the SBIIS
Galatians 2 in the SBIIS2
Galatians 2 in the SBIIS3
Galatians 2 in the SBIKS
Galatians 2 in the SBIKS2
Galatians 2 in the SBIMS
Galatians 2 in the SBIOS
Galatians 2 in the SBIPS
Galatians 2 in the SBISS
Galatians 2 in the SBITS
Galatians 2 in the SBITS2
Galatians 2 in the SBITS3
Galatians 2 in the SBITS4
Galatians 2 in the SBIUS
Galatians 2 in the SBIVS
Galatians 2 in the SBT
Galatians 2 in the SBT1E
Galatians 2 in the SCHL
Galatians 2 in the SNT
Galatians 2 in the SUSU
Galatians 2 in the SUSU2
Galatians 2 in the SYNO
Galatians 2 in the TBIAOTANT
Galatians 2 in the TBT1E
Galatians 2 in the TBT1E2
Galatians 2 in the TFTIP
Galatians 2 in the TFTU
Galatians 2 in the TGNTATF3T
Galatians 2 in the THAI
Galatians 2 in the TNFD
Galatians 2 in the TNT
Galatians 2 in the TNTIK
Galatians 2 in the TNTIL
Galatians 2 in the TNTIN
Galatians 2 in the TNTIP
Galatians 2 in the TNTIZ
Galatians 2 in the TOMA
Galatians 2 in the TTENT
Galatians 2 in the UBG
Galatians 2 in the UGV
Galatians 2 in the UGV2
Galatians 2 in the UGV3
Galatians 2 in the VBL
Galatians 2 in the VDCC
Galatians 2 in the YALU
Galatians 2 in the YAPE
Galatians 2 in the YBVTP
Galatians 2 in the ZBP