Galatians 4 (BOHCB)
1 Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome. 2 Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa. 3 Haka yake, sa’ad da muke ’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya. 4 Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, 5 domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya. 6 Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba, Uba.” 7 Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji. 8 Dā da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda a ainihi ba alloli ba ne. 9 Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne? 10 Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokuta da shekaru na musamman! 11 Kai, kun ba ni tsoro, don ya zama kamar duk wahalar da na yi a kanku banza ne! 12 Ina roƙonku ’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba. 13 Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko. 14 Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa. 15 Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni. 16 Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan? 17 Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su. 18 Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba. 19 Ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku. 20 Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku! 21 Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba ne? 22 Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ’ya’ya biyu maza, ɗaya ta wurin mace ’yar aikin gidansa, ɗaya kuma ta wurin ainihin matarsa. 23 Ɗansa na wajen mace ’yar aikin gidansa ya zo bisa ga ƙa’idar jiki ne; amma ɗansa na wajen ainihin matarsa ya zo a sakamakon alkawarin ne. 24 Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan. 25 Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ’ya’yanta. 26 Amma Urushalimar da take sama ’yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu. 27 Gama a rubuce yake cewa,“Ki yi farin ciki, ya ke bakararriya,wadda ba ta haihuwaki ɓarke da murna, ki kuma tā da murya,ke da ba kya naƙuda;domin da yawa ne ’ya’yan macen da aka yashe,fiye da na mai miji.” 28 To, ku ’yan’uwa, ku ’ya’yan alkawari ne kamar Ishaku. 29 A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu. 30 Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan ’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace ’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.” 31 Saboda haka, ’yan’uwa, mu ba ’ya’yan mace ’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.
In Other Versions
Galatians 4 in the ANGEFD
Galatians 4 in the ANTPNG2D
Galatians 4 in the AS21
Galatians 4 in the BAGH
Galatians 4 in the BBPNG
Galatians 4 in the BBT1E
Galatians 4 in the BDS
Galatians 4 in the BEV
Galatians 4 in the BHAD
Galatians 4 in the BIB
Galatians 4 in the BLPT
Galatians 4 in the BNT
Galatians 4 in the BNTABOOT
Galatians 4 in the BNTLV
Galatians 4 in the BOATCB
Galatians 4 in the BOATCB2
Galatians 4 in the BOBCV
Galatians 4 in the BOCNT
Galatians 4 in the BOECS
Galatians 4 in the BOGWICC
Galatians 4 in the BOHCV
Galatians 4 in the BOHLNT
Galatians 4 in the BOHNTLTAL
Galatians 4 in the BOICB
Galatians 4 in the BOILNTAP
Galatians 4 in the BOITCV
Galatians 4 in the BOKCV
Galatians 4 in the BOKCV2
Galatians 4 in the BOKHWOG
Galatians 4 in the BOKSSV
Galatians 4 in the BOLCB
Galatians 4 in the BOLCB2
Galatians 4 in the BOMCV
Galatians 4 in the BONAV
Galatians 4 in the BONCB
Galatians 4 in the BONLT
Galatians 4 in the BONUT2
Galatians 4 in the BOPLNT
Galatians 4 in the BOSCB
Galatians 4 in the BOSNC
Galatians 4 in the BOTLNT
Galatians 4 in the BOVCB
Galatians 4 in the BOYCB
Galatians 4 in the BPBB
Galatians 4 in the BPH
Galatians 4 in the BSB
Galatians 4 in the CCB
Galatians 4 in the CUV
Galatians 4 in the CUVS
Galatians 4 in the DBT
Galatians 4 in the DGDNT
Galatians 4 in the DHNT
Galatians 4 in the DNT
Galatians 4 in the ELBE
Galatians 4 in the EMTV
Galatians 4 in the ESV
Galatians 4 in the FBV
Galatians 4 in the FEB
Galatians 4 in the GGMNT
Galatians 4 in the GNT
Galatians 4 in the HARY
Galatians 4 in the HNT
Galatians 4 in the IRVA
Galatians 4 in the IRVB
Galatians 4 in the IRVG
Galatians 4 in the IRVH
Galatians 4 in the IRVK
Galatians 4 in the IRVM
Galatians 4 in the IRVM2
Galatians 4 in the IRVO
Galatians 4 in the IRVP
Galatians 4 in the IRVT
Galatians 4 in the IRVT2
Galatians 4 in the IRVU
Galatians 4 in the ISVN
Galatians 4 in the JSNT
Galatians 4 in the KAPI
Galatians 4 in the KBT1ETNIK
Galatians 4 in the KBV
Galatians 4 in the KJV
Galatians 4 in the KNFD
Galatians 4 in the LBA
Galatians 4 in the LBLA
Galatians 4 in the LNT
Galatians 4 in the LSV
Galatians 4 in the MAAL
Galatians 4 in the MBV
Galatians 4 in the MBV2
Galatians 4 in the MHNT
Galatians 4 in the MKNFD
Galatians 4 in the MNG
Galatians 4 in the MNT
Galatians 4 in the MNT2
Galatians 4 in the MRS1T
Galatians 4 in the NAA
Galatians 4 in the NASB
Galatians 4 in the NBLA
Galatians 4 in the NBS
Galatians 4 in the NBVTP
Galatians 4 in the NET2
Galatians 4 in the NIV11
Galatians 4 in the NNT
Galatians 4 in the NNT2
Galatians 4 in the NNT3
Galatians 4 in the PDDPT
Galatians 4 in the PFNT
Galatians 4 in the RMNT
Galatians 4 in the SBIAS
Galatians 4 in the SBIBS
Galatians 4 in the SBIBS2
Galatians 4 in the SBICS
Galatians 4 in the SBIDS
Galatians 4 in the SBIGS
Galatians 4 in the SBIHS
Galatians 4 in the SBIIS
Galatians 4 in the SBIIS2
Galatians 4 in the SBIIS3
Galatians 4 in the SBIKS
Galatians 4 in the SBIKS2
Galatians 4 in the SBIMS
Galatians 4 in the SBIOS
Galatians 4 in the SBIPS
Galatians 4 in the SBISS
Galatians 4 in the SBITS
Galatians 4 in the SBITS2
Galatians 4 in the SBITS3
Galatians 4 in the SBITS4
Galatians 4 in the SBIUS
Galatians 4 in the SBIVS
Galatians 4 in the SBT
Galatians 4 in the SBT1E
Galatians 4 in the SCHL
Galatians 4 in the SNT
Galatians 4 in the SUSU
Galatians 4 in the SUSU2
Galatians 4 in the SYNO
Galatians 4 in the TBIAOTANT
Galatians 4 in the TBT1E
Galatians 4 in the TBT1E2
Galatians 4 in the TFTIP
Galatians 4 in the TFTU
Galatians 4 in the TGNTATF3T
Galatians 4 in the THAI
Galatians 4 in the TNFD
Galatians 4 in the TNT
Galatians 4 in the TNTIK
Galatians 4 in the TNTIL
Galatians 4 in the TNTIN
Galatians 4 in the TNTIP
Galatians 4 in the TNTIZ
Galatians 4 in the TOMA
Galatians 4 in the TTENT
Galatians 4 in the UBG
Galatians 4 in the UGV
Galatians 4 in the UGV2
Galatians 4 in the UGV3
Galatians 4 in the VBL
Galatians 4 in the VDCC
Galatians 4 in the YALU
Galatians 4 in the YAPE
Galatians 4 in the YBVTP
Galatians 4 in the ZBP