Galatians 5 (BOHCB)
1 Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta. 2 Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kuka yarda aka yi muku kaciya, wannan ya nuna Kiristi ba shi da amfani a gare ku ba ko kaɗan. 3 Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yă kiyaye dukan Doka. 4 Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi ke nan; kuka kuma fāɗi daga alheri. 5 Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu. 6 Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna. 7 Kun yi tsere mai kyau a dā. Wa ya shige gabanku ya hana ku bin gaskiya? 8 Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne. 9 “Ɗan yisti kaɗan ne yake gama dukan curin burodi.” 10 Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne. 11 ’Yan’uwa, da a ce har yanzu ina wa’azin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan. 12 Da ma a ce masu tā da hankalinku ɗin nan su yanke gabansu gaba ɗaya mana! 13 Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna. 14 Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 15 In kun ci gaba da cizo, kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna. 16 Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba. 17 Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so. 18 Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku a ƙarƙashin Doka ke nan. 19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba. 22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa. 24 Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa. 25 Da yake muna rayuwa ta Ruhu ne, bari mu ci gaba da al’amuranmu ta wurin Ruhu. 26 Kada mu zama masu girman kai, muna tsokana muna kuma jin kishin juna.
In Other Versions
Galatians 5 in the ANGEFD
Galatians 5 in the ANTPNG2D
Galatians 5 in the AS21
Galatians 5 in the BAGH
Galatians 5 in the BBPNG
Galatians 5 in the BBT1E
Galatians 5 in the BDS
Galatians 5 in the BEV
Galatians 5 in the BHAD
Galatians 5 in the BIB
Galatians 5 in the BLPT
Galatians 5 in the BNT
Galatians 5 in the BNTABOOT
Galatians 5 in the BNTLV
Galatians 5 in the BOATCB
Galatians 5 in the BOATCB2
Galatians 5 in the BOBCV
Galatians 5 in the BOCNT
Galatians 5 in the BOECS
Galatians 5 in the BOGWICC
Galatians 5 in the BOHCV
Galatians 5 in the BOHLNT
Galatians 5 in the BOHNTLTAL
Galatians 5 in the BOICB
Galatians 5 in the BOILNTAP
Galatians 5 in the BOITCV
Galatians 5 in the BOKCV
Galatians 5 in the BOKCV2
Galatians 5 in the BOKHWOG
Galatians 5 in the BOKSSV
Galatians 5 in the BOLCB
Galatians 5 in the BOLCB2
Galatians 5 in the BOMCV
Galatians 5 in the BONAV
Galatians 5 in the BONCB
Galatians 5 in the BONLT
Galatians 5 in the BONUT2
Galatians 5 in the BOPLNT
Galatians 5 in the BOSCB
Galatians 5 in the BOSNC
Galatians 5 in the BOTLNT
Galatians 5 in the BOVCB
Galatians 5 in the BOYCB
Galatians 5 in the BPBB
Galatians 5 in the BPH
Galatians 5 in the BSB
Galatians 5 in the CCB
Galatians 5 in the CUV
Galatians 5 in the CUVS
Galatians 5 in the DBT
Galatians 5 in the DGDNT
Galatians 5 in the DHNT
Galatians 5 in the DNT
Galatians 5 in the ELBE
Galatians 5 in the EMTV
Galatians 5 in the ESV
Galatians 5 in the FBV
Galatians 5 in the FEB
Galatians 5 in the GGMNT
Galatians 5 in the GNT
Galatians 5 in the HARY
Galatians 5 in the HNT
Galatians 5 in the IRVA
Galatians 5 in the IRVB
Galatians 5 in the IRVG
Galatians 5 in the IRVH
Galatians 5 in the IRVK
Galatians 5 in the IRVM
Galatians 5 in the IRVM2
Galatians 5 in the IRVO
Galatians 5 in the IRVP
Galatians 5 in the IRVT
Galatians 5 in the IRVT2
Galatians 5 in the IRVU
Galatians 5 in the ISVN
Galatians 5 in the JSNT
Galatians 5 in the KAPI
Galatians 5 in the KBT1ETNIK
Galatians 5 in the KBV
Galatians 5 in the KJV
Galatians 5 in the KNFD
Galatians 5 in the LBA
Galatians 5 in the LBLA
Galatians 5 in the LNT
Galatians 5 in the LSV
Galatians 5 in the MAAL
Galatians 5 in the MBV
Galatians 5 in the MBV2
Galatians 5 in the MHNT
Galatians 5 in the MKNFD
Galatians 5 in the MNG
Galatians 5 in the MNT
Galatians 5 in the MNT2
Galatians 5 in the MRS1T
Galatians 5 in the NAA
Galatians 5 in the NASB
Galatians 5 in the NBLA
Galatians 5 in the NBS
Galatians 5 in the NBVTP
Galatians 5 in the NET2
Galatians 5 in the NIV11
Galatians 5 in the NNT
Galatians 5 in the NNT2
Galatians 5 in the NNT3
Galatians 5 in the PDDPT
Galatians 5 in the PFNT
Galatians 5 in the RMNT
Galatians 5 in the SBIAS
Galatians 5 in the SBIBS
Galatians 5 in the SBIBS2
Galatians 5 in the SBICS
Galatians 5 in the SBIDS
Galatians 5 in the SBIGS
Galatians 5 in the SBIHS
Galatians 5 in the SBIIS
Galatians 5 in the SBIIS2
Galatians 5 in the SBIIS3
Galatians 5 in the SBIKS
Galatians 5 in the SBIKS2
Galatians 5 in the SBIMS
Galatians 5 in the SBIOS
Galatians 5 in the SBIPS
Galatians 5 in the SBISS
Galatians 5 in the SBITS
Galatians 5 in the SBITS2
Galatians 5 in the SBITS3
Galatians 5 in the SBITS4
Galatians 5 in the SBIUS
Galatians 5 in the SBIVS
Galatians 5 in the SBT
Galatians 5 in the SBT1E
Galatians 5 in the SCHL
Galatians 5 in the SNT
Galatians 5 in the SUSU
Galatians 5 in the SUSU2
Galatians 5 in the SYNO
Galatians 5 in the TBIAOTANT
Galatians 5 in the TBT1E
Galatians 5 in the TBT1E2
Galatians 5 in the TFTIP
Galatians 5 in the TFTU
Galatians 5 in the TGNTATF3T
Galatians 5 in the THAI
Galatians 5 in the TNFD
Galatians 5 in the TNT
Galatians 5 in the TNTIK
Galatians 5 in the TNTIL
Galatians 5 in the TNTIN
Galatians 5 in the TNTIP
Galatians 5 in the TNTIZ
Galatians 5 in the TOMA
Galatians 5 in the TTENT
Galatians 5 in the UBG
Galatians 5 in the UGV
Galatians 5 in the UGV2
Galatians 5 in the UGV3
Galatians 5 in the VBL
Galatians 5 in the VDCC
Galatians 5 in the YALU
Galatians 5 in the YAPE
Galatians 5 in the YBVTP
Galatians 5 in the ZBP