James 4 (BOHCB)
1 Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne? 2 Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba. 3 Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku. 4 Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan. 5 Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce ruhun da ya sa yă zauna a cikinmu yana kishi sosai? 6 Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce,“Allah yana gāba da masu girman kaiamma yakan ba da alheri ga masu tawali’u.” 7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku. 8 Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu. 9 Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki ku kuma yi kuka. Ku mai da dariyarku ta zama makoki, farin cikinku kuma yă zama ɓacin zuciya. 10 Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku. 11 ’Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne. 12 Akwai Mai ba da doka da kuma Alƙali guda ɗaya tak, shi ne yake da ikon ceto da kuma hallakarwa. Amma kai, wane ne da za ka hukunta maƙwabcinka? 13 Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” 14 Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. 15 A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.” 16 Ga shi, kuna fariya da taƙama. Duk irin wannan taƙama mugun abu ne. 17 Saboda haka, duk wanda ya san abu mai kyan da ya kamata yă yi, bai kuwa yi ba, ya yi zunubi ke nan.
In Other Versions
James 4 in the ANGEFD
James 4 in the ANTPNG2D
James 4 in the AS21
James 4 in the BAGH
James 4 in the BBPNG
James 4 in the BBT1E
James 4 in the BDS
James 4 in the BEV
James 4 in the BHAD
James 4 in the BIB
James 4 in the BLPT
James 4 in the BNT
James 4 in the BNTABOOT
James 4 in the BNTLV
James 4 in the BOATCB
James 4 in the BOATCB2
James 4 in the BOBCV
James 4 in the BOCNT
James 4 in the BOECS
James 4 in the BOGWICC
James 4 in the BOHCV
James 4 in the BOHLNT
James 4 in the BOHNTLTAL
James 4 in the BOICB
James 4 in the BOILNTAP
James 4 in the BOITCV
James 4 in the BOKCV
James 4 in the BOKCV2
James 4 in the BOKHWOG
James 4 in the BOKSSV
James 4 in the BOLCB
James 4 in the BOLCB2
James 4 in the BOMCV
James 4 in the BONAV
James 4 in the BONCB
James 4 in the BONLT
James 4 in the BONUT2
James 4 in the BOPLNT
James 4 in the BOSCB
James 4 in the BOSNC
James 4 in the BOTLNT
James 4 in the BOVCB
James 4 in the BOYCB
James 4 in the BPBB
James 4 in the BPH
James 4 in the BSB
James 4 in the CCB
James 4 in the CUV
James 4 in the CUVS
James 4 in the DBT
James 4 in the DGDNT
James 4 in the DHNT
James 4 in the DNT
James 4 in the ELBE
James 4 in the EMTV
James 4 in the ESV
James 4 in the FBV
James 4 in the FEB
James 4 in the GGMNT
James 4 in the GNT
James 4 in the HARY
James 4 in the HNT
James 4 in the IRVA
James 4 in the IRVB
James 4 in the IRVG
James 4 in the IRVH
James 4 in the IRVK
James 4 in the IRVM
James 4 in the IRVM2
James 4 in the IRVO
James 4 in the IRVP
James 4 in the IRVT
James 4 in the IRVT2
James 4 in the IRVU
James 4 in the ISVN
James 4 in the JSNT
James 4 in the KAPI
James 4 in the KBT1ETNIK
James 4 in the KBV
James 4 in the KJV
James 4 in the KNFD
James 4 in the LBA
James 4 in the LBLA
James 4 in the LNT
James 4 in the LSV
James 4 in the MAAL
James 4 in the MBV
James 4 in the MBV2
James 4 in the MHNT
James 4 in the MKNFD
James 4 in the MNG
James 4 in the MNT
James 4 in the MNT2
James 4 in the MRS1T
James 4 in the NAA
James 4 in the NASB
James 4 in the NBLA
James 4 in the NBS
James 4 in the NBVTP
James 4 in the NET2
James 4 in the NIV11
James 4 in the NNT
James 4 in the NNT2
James 4 in the NNT3
James 4 in the PDDPT
James 4 in the PFNT
James 4 in the RMNT
James 4 in the SBIAS
James 4 in the SBIBS
James 4 in the SBIBS2
James 4 in the SBICS
James 4 in the SBIDS
James 4 in the SBIGS
James 4 in the SBIHS
James 4 in the SBIIS
James 4 in the SBIIS2
James 4 in the SBIIS3
James 4 in the SBIKS
James 4 in the SBIKS2
James 4 in the SBIMS
James 4 in the SBIOS
James 4 in the SBIPS
James 4 in the SBISS
James 4 in the SBITS
James 4 in the SBITS2
James 4 in the SBITS3
James 4 in the SBITS4
James 4 in the SBIUS
James 4 in the SBIVS
James 4 in the SBT
James 4 in the SBT1E
James 4 in the SCHL
James 4 in the SNT
James 4 in the SUSU
James 4 in the SUSU2
James 4 in the SYNO
James 4 in the TBIAOTANT
James 4 in the TBT1E
James 4 in the TBT1E2
James 4 in the TFTIP
James 4 in the TFTU
James 4 in the TGNTATF3T
James 4 in the THAI
James 4 in the TNFD
James 4 in the TNT
James 4 in the TNTIK
James 4 in the TNTIL
James 4 in the TNTIN
James 4 in the TNTIP
James 4 in the TNTIZ
James 4 in the TOMA
James 4 in the TTENT
James 4 in the UBG
James 4 in the UGV
James 4 in the UGV2
James 4 in the UGV3
James 4 in the VBL
James 4 in the VDCC
James 4 in the YALU
James 4 in the YAPE
James 4 in the YBVTP
James 4 in the ZBP