James 5 (BOHCB)

1 Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. 2 Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku. 3 Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe. 4 Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki. 5 Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka. 6 Kun hukunta kun kuma kashe mutane marasa laifi, waɗanda ba su yi gāba da ku ba. 7 Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. 8 Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa. 9 ’Yan’uwa, kada ku yi gunaguni da juna, don kada a hukunta ku. Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa! 10 ’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala. 11 Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai. 12 ’Yan’uwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari “I” naku yă zama “I”. “A’a” naku kuma yă zama “A’a”, don kada a hukunta ku. 13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo. 14 Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. 15 Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa. 16 Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani. 17 Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi. 18 Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta. 19 ’Yan’uwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi, 20 sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

In Other Versions

James 5 in the ANGEFD

James 5 in the ANTPNG2D

James 5 in the AS21

James 5 in the BAGH

James 5 in the BBPNG

James 5 in the BBT1E

James 5 in the BDS

James 5 in the BEV

James 5 in the BHAD

James 5 in the BIB

James 5 in the BLPT

James 5 in the BNT

James 5 in the BNTABOOT

James 5 in the BNTLV

James 5 in the BOATCB

James 5 in the BOATCB2

James 5 in the BOBCV

James 5 in the BOCNT

James 5 in the BOECS

James 5 in the BOGWICC

James 5 in the BOHCV

James 5 in the BOHLNT

James 5 in the BOHNTLTAL

James 5 in the BOICB

James 5 in the BOILNTAP

James 5 in the BOITCV

James 5 in the BOKCV

James 5 in the BOKCV2

James 5 in the BOKHWOG

James 5 in the BOKSSV

James 5 in the BOLCB

James 5 in the BOLCB2

James 5 in the BOMCV

James 5 in the BONAV

James 5 in the BONCB

James 5 in the BONLT

James 5 in the BONUT2

James 5 in the BOPLNT

James 5 in the BOSCB

James 5 in the BOSNC

James 5 in the BOTLNT

James 5 in the BOVCB

James 5 in the BOYCB

James 5 in the BPBB

James 5 in the BPH

James 5 in the BSB

James 5 in the CCB

James 5 in the CUV

James 5 in the CUVS

James 5 in the DBT

James 5 in the DGDNT

James 5 in the DHNT

James 5 in the DNT

James 5 in the ELBE

James 5 in the EMTV

James 5 in the ESV

James 5 in the FBV

James 5 in the FEB

James 5 in the GGMNT

James 5 in the GNT

James 5 in the HARY

James 5 in the HNT

James 5 in the IRVA

James 5 in the IRVB

James 5 in the IRVG

James 5 in the IRVH

James 5 in the IRVK

James 5 in the IRVM

James 5 in the IRVM2

James 5 in the IRVO

James 5 in the IRVP

James 5 in the IRVT

James 5 in the IRVT2

James 5 in the IRVU

James 5 in the ISVN

James 5 in the JSNT

James 5 in the KAPI

James 5 in the KBT1ETNIK

James 5 in the KBV

James 5 in the KJV

James 5 in the KNFD

James 5 in the LBA

James 5 in the LBLA

James 5 in the LNT

James 5 in the LSV

James 5 in the MAAL

James 5 in the MBV

James 5 in the MBV2

James 5 in the MHNT

James 5 in the MKNFD

James 5 in the MNG

James 5 in the MNT

James 5 in the MNT2

James 5 in the MRS1T

James 5 in the NAA

James 5 in the NASB

James 5 in the NBLA

James 5 in the NBS

James 5 in the NBVTP

James 5 in the NET2

James 5 in the NIV11

James 5 in the NNT

James 5 in the NNT2

James 5 in the NNT3

James 5 in the PDDPT

James 5 in the PFNT

James 5 in the RMNT

James 5 in the SBIAS

James 5 in the SBIBS

James 5 in the SBIBS2

James 5 in the SBICS

James 5 in the SBIDS

James 5 in the SBIGS

James 5 in the SBIHS

James 5 in the SBIIS

James 5 in the SBIIS2

James 5 in the SBIIS3

James 5 in the SBIKS

James 5 in the SBIKS2

James 5 in the SBIMS

James 5 in the SBIOS

James 5 in the SBIPS

James 5 in the SBISS

James 5 in the SBITS

James 5 in the SBITS2

James 5 in the SBITS3

James 5 in the SBITS4

James 5 in the SBIUS

James 5 in the SBIVS

James 5 in the SBT

James 5 in the SBT1E

James 5 in the SCHL

James 5 in the SNT

James 5 in the SUSU

James 5 in the SUSU2

James 5 in the SYNO

James 5 in the TBIAOTANT

James 5 in the TBT1E

James 5 in the TBT1E2

James 5 in the TFTIP

James 5 in the TFTU

James 5 in the TGNTATF3T

James 5 in the THAI

James 5 in the TNFD

James 5 in the TNT

James 5 in the TNTIK

James 5 in the TNTIL

James 5 in the TNTIN

James 5 in the TNTIP

James 5 in the TNTIZ

James 5 in the TOMA

James 5 in the TTENT

James 5 in the UBG

James 5 in the UGV

James 5 in the UGV2

James 5 in the UGV3

James 5 in the VBL

James 5 in the VDCC

James 5 in the YALU

James 5 in the YAPE

James 5 in the YBVTP

James 5 in the ZBP