John 15 (BOHCB)

1 “Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin. 2 Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya. 3 Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku. 4 Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina. 5 “Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. 6 Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone. 7 In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. 8 Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne. 9 “Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata. 10 In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. 11 Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya. 12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. 14 Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. 15 Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. 16 Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana. 17 Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna. 18 “In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. 19 Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20 Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma. 21 Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba. 22 Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu. 23 Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma. 24 Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana. 25 Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’ 26 “Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni. 27 Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko.

In Other Versions

John 15 in the ANGEFD

John 15 in the ANTPNG2D

John 15 in the AS21

John 15 in the BAGH

John 15 in the BBPNG

John 15 in the BBT1E

John 15 in the BDS

John 15 in the BEV

John 15 in the BHAD

John 15 in the BIB

John 15 in the BLPT

John 15 in the BNT

John 15 in the BNTABOOT

John 15 in the BNTLV

John 15 in the BOATCB

John 15 in the BOATCB2

John 15 in the BOBCV

John 15 in the BOCNT

John 15 in the BOECS

John 15 in the BOGWICC

John 15 in the BOHCV

John 15 in the BOHLNT

John 15 in the BOHNTLTAL

John 15 in the BOICB

John 15 in the BOILNTAP

John 15 in the BOITCV

John 15 in the BOKCV

John 15 in the BOKCV2

John 15 in the BOKHWOG

John 15 in the BOKSSV

John 15 in the BOLCB

John 15 in the BOLCB2

John 15 in the BOMCV

John 15 in the BONAV

John 15 in the BONCB

John 15 in the BONLT

John 15 in the BONUT2

John 15 in the BOPLNT

John 15 in the BOSCB

John 15 in the BOSNC

John 15 in the BOTLNT

John 15 in the BOVCB

John 15 in the BOYCB

John 15 in the BPBB

John 15 in the BPH

John 15 in the BSB

John 15 in the CCB

John 15 in the CUV

John 15 in the CUVS

John 15 in the DBT

John 15 in the DGDNT

John 15 in the DHNT

John 15 in the DNT

John 15 in the ELBE

John 15 in the EMTV

John 15 in the ESV

John 15 in the FBV

John 15 in the FEB

John 15 in the GGMNT

John 15 in the GNT

John 15 in the HARY

John 15 in the HNT

John 15 in the IRVA

John 15 in the IRVB

John 15 in the IRVG

John 15 in the IRVH

John 15 in the IRVK

John 15 in the IRVM

John 15 in the IRVM2

John 15 in the IRVO

John 15 in the IRVP

John 15 in the IRVT

John 15 in the IRVT2

John 15 in the IRVU

John 15 in the ISVN

John 15 in the JSNT

John 15 in the KAPI

John 15 in the KBT1ETNIK

John 15 in the KBV

John 15 in the KJV

John 15 in the KNFD

John 15 in the LBA

John 15 in the LBLA

John 15 in the LNT

John 15 in the LSV

John 15 in the MAAL

John 15 in the MBV

John 15 in the MBV2

John 15 in the MHNT

John 15 in the MKNFD

John 15 in the MNG

John 15 in the MNT

John 15 in the MNT2

John 15 in the MRS1T

John 15 in the NAA

John 15 in the NASB

John 15 in the NBLA

John 15 in the NBS

John 15 in the NBVTP

John 15 in the NET2

John 15 in the NIV11

John 15 in the NNT

John 15 in the NNT2

John 15 in the NNT3

John 15 in the PDDPT

John 15 in the PFNT

John 15 in the RMNT

John 15 in the SBIAS

John 15 in the SBIBS

John 15 in the SBIBS2

John 15 in the SBICS

John 15 in the SBIDS

John 15 in the SBIGS

John 15 in the SBIHS

John 15 in the SBIIS

John 15 in the SBIIS2

John 15 in the SBIIS3

John 15 in the SBIKS

John 15 in the SBIKS2

John 15 in the SBIMS

John 15 in the SBIOS

John 15 in the SBIPS

John 15 in the SBISS

John 15 in the SBITS

John 15 in the SBITS2

John 15 in the SBITS3

John 15 in the SBITS4

John 15 in the SBIUS

John 15 in the SBIVS

John 15 in the SBT

John 15 in the SBT1E

John 15 in the SCHL

John 15 in the SNT

John 15 in the SUSU

John 15 in the SUSU2

John 15 in the SYNO

John 15 in the TBIAOTANT

John 15 in the TBT1E

John 15 in the TBT1E2

John 15 in the TFTIP

John 15 in the TFTU

John 15 in the TGNTATF3T

John 15 in the THAI

John 15 in the TNFD

John 15 in the TNT

John 15 in the TNTIK

John 15 in the TNTIL

John 15 in the TNTIN

John 15 in the TNTIP

John 15 in the TNTIZ

John 15 in the TOMA

John 15 in the TTENT

John 15 in the UBG

John 15 in the UGV

John 15 in the UGV2

John 15 in the UGV3

John 15 in the VBL

John 15 in the VDCC

John 15 in the YALU

John 15 in the YAPE

John 15 in the YBVTP

John 15 in the ZBP