John 4 (BOHCB)

1 Yesu ya ji labari cewa Yahudawa sun ji cewa ya wuce Yohanna samun masu bi, yana kuma yin musu baftisma, 2 ko da yake ba Yesu ne yake baftismar ba, almajiransa ne. 3 Da ya sami wannan labari, sai ya bar Yahudiya ya sāke koma Galili. 4 To, ya zama dole yă bi ta Samariya. 5 Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf. 6 Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen sa’a ta shida ne. 7 Sa’ad da wata mutuniyar Samariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha?” 8 (Almajiransa kuwa sun shiga gari don sayi abinci.) 9 Sai mutuniyar Samariyar ta ce masa, “Kai mutumin Yahuda ne, ni kuwa mutuniyar Samariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa.) 10 Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, shi kuwa da ya ba ki ruwan rai.” 11 Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai? 12 Ka fi mahaifinmu Yaƙub ne, wanda ya ba mu rijiyar ya kuma sha daga ciki da kansa, haka ma ’ya’yansa da kuma garkunan shanunsa da tumakinsa?” 13 Yesu ya amsa ya ce, “Kowa ya sha wannan ruwa, zai sāke jin ƙishirwa, 14 amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.” 15 Sai macen ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, in yi ta zuwa nan ɗiban ruwa.” 16 Sai ya ce mata, “Je ki zo da mijinki.” 17 Sai ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.”Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji. 18 Gaskiyar ita ce, kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.” 19 Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ina gani kai annabi ne. 20 Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan, amma ku Yahudawa kun ce a Urushalima ne ya kamata a yi sujada.” 21 Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba. 22 Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake. 23 Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24 Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.” 25 Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.” 26 Sai Yesu ya ce, “Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.” 27 Suna gama magana ke nan sai almajiransa suka iso, suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma ba wanda ya ce, “Me kake so?” Ko “Me ya sa kake magana da ita?” 28 Sai macen ta bar tulunta na ruwa, ta koma cikin gari ta ce wa mutane, 29 “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi. Shin, ko shi ne Kiristi?” 30 Sai suka fita daga garin suka nufa inda yake. 31 Ana cikin haka, sai almajiransa suka roƙe shi suka ce, “Rabbi, ci abinci mana.” 32 Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku san kome a kai ba.” 33 Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?” 34 Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa. 35 Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku ɗaga idanu ku dubi gonaki! Sun isa girbi. 36 Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. 37 Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’ 38 Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.” 39 Samariyawa da yawa daga wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” 40 To, da Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi yă zauna da su, ya kuwa zauna kwana biyu. 41 Saboda kalmominsa kuwa da yawa suka gaskata. 42 Sai suka ce wa macen, “Yanzu kam mun gaskata, ba don abin da kika faɗa kawai ba; yanzu mun ji da kanmu, mun kuwa san cewa wannan mutum tabbatacce shi ne Mai Ceton duniya.” 43 Bayan kwana biyun nan sai ya bar can zuwa Galili. 44 (To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa.) 45 Da ya isa Galili, sai mutanen Galili suka marabce shi. Sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin Bikin Ƙetarewa, gama su ma sun kasance a can. 46 Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum. 47 Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa. 48 Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.” 49 Ma’aikacin hukuman ya ce, “Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu.” 50 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.”Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi. 51 Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa. 52 Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai.” 53 Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata. 54 Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili.

In Other Versions

John 4 in the ANGEFD

John 4 in the ANTPNG2D

John 4 in the AS21

John 4 in the BAGH

John 4 in the BBPNG

John 4 in the BBT1E

John 4 in the BDS

John 4 in the BEV

John 4 in the BHAD

John 4 in the BIB

John 4 in the BLPT

John 4 in the BNT

John 4 in the BNTABOOT

John 4 in the BNTLV

John 4 in the BOATCB

John 4 in the BOATCB2

John 4 in the BOBCV

John 4 in the BOCNT

John 4 in the BOECS

John 4 in the BOGWICC

John 4 in the BOHCV

John 4 in the BOHLNT

John 4 in the BOHNTLTAL

John 4 in the BOICB

John 4 in the BOILNTAP

John 4 in the BOITCV

John 4 in the BOKCV

John 4 in the BOKCV2

John 4 in the BOKHWOG

John 4 in the BOKSSV

John 4 in the BOLCB

John 4 in the BOLCB2

John 4 in the BOMCV

John 4 in the BONAV

John 4 in the BONCB

John 4 in the BONLT

John 4 in the BONUT2

John 4 in the BOPLNT

John 4 in the BOSCB

John 4 in the BOSNC

John 4 in the BOTLNT

John 4 in the BOVCB

John 4 in the BOYCB

John 4 in the BPBB

John 4 in the BPH

John 4 in the BSB

John 4 in the CCB

John 4 in the CUV

John 4 in the CUVS

John 4 in the DBT

John 4 in the DGDNT

John 4 in the DHNT

John 4 in the DNT

John 4 in the ELBE

John 4 in the EMTV

John 4 in the ESV

John 4 in the FBV

John 4 in the FEB

John 4 in the GGMNT

John 4 in the GNT

John 4 in the HARY

John 4 in the HNT

John 4 in the IRVA

John 4 in the IRVB

John 4 in the IRVG

John 4 in the IRVH

John 4 in the IRVK

John 4 in the IRVM

John 4 in the IRVM2

John 4 in the IRVO

John 4 in the IRVP

John 4 in the IRVT

John 4 in the IRVT2

John 4 in the IRVU

John 4 in the ISVN

John 4 in the JSNT

John 4 in the KAPI

John 4 in the KBT1ETNIK

John 4 in the KBV

John 4 in the KJV

John 4 in the KNFD

John 4 in the LBA

John 4 in the LBLA

John 4 in the LNT

John 4 in the LSV

John 4 in the MAAL

John 4 in the MBV

John 4 in the MBV2

John 4 in the MHNT

John 4 in the MKNFD

John 4 in the MNG

John 4 in the MNT

John 4 in the MNT2

John 4 in the MRS1T

John 4 in the NAA

John 4 in the NASB

John 4 in the NBLA

John 4 in the NBS

John 4 in the NBVTP

John 4 in the NET2

John 4 in the NIV11

John 4 in the NNT

John 4 in the NNT2

John 4 in the NNT3

John 4 in the PDDPT

John 4 in the PFNT

John 4 in the RMNT

John 4 in the SBIAS

John 4 in the SBIBS

John 4 in the SBIBS2

John 4 in the SBICS

John 4 in the SBIDS

John 4 in the SBIGS

John 4 in the SBIHS

John 4 in the SBIIS

John 4 in the SBIIS2

John 4 in the SBIIS3

John 4 in the SBIKS

John 4 in the SBIKS2

John 4 in the SBIMS

John 4 in the SBIOS

John 4 in the SBIPS

John 4 in the SBISS

John 4 in the SBITS

John 4 in the SBITS2

John 4 in the SBITS3

John 4 in the SBITS4

John 4 in the SBIUS

John 4 in the SBIVS

John 4 in the SBT

John 4 in the SBT1E

John 4 in the SCHL

John 4 in the SNT

John 4 in the SUSU

John 4 in the SUSU2

John 4 in the SYNO

John 4 in the TBIAOTANT

John 4 in the TBT1E

John 4 in the TBT1E2

John 4 in the TFTIP

John 4 in the TFTU

John 4 in the TGNTATF3T

John 4 in the THAI

John 4 in the TNFD

John 4 in the TNT

John 4 in the TNTIK

John 4 in the TNTIL

John 4 in the TNTIN

John 4 in the TNTIP

John 4 in the TNTIZ

John 4 in the TOMA

John 4 in the TTENT

John 4 in the UBG

John 4 in the UGV

John 4 in the UGV2

John 4 in the UGV3

John 4 in the VBL

John 4 in the VDCC

John 4 in the YALU

John 4 in the YAPE

John 4 in the YBVTP

John 4 in the ZBP