Luke 14 (BOHCB)
1 Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau. 2 A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. 3 Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, “Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?” 4 Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi. 5 Sai ya tambaye, su ya ce, “In wani a cikinku yana da ɗa, ko bijimi da ya faɗa a rijiya a ranar Asabbaci, ba za ku cire shi nan da nan ba?” 6 Suka rasa abin faɗi. 7 Da ya lura da yadda baƙi suna zaɓan wuraren zama masu bangirma a tebur, sai ya faɗa musu wannan misali, ya ce; 8 “In wani ya gayyace ka bikin aure, kada ka zaɓi wurin zama mai bangirma, don wataƙila akwai wani da ya fi ka girma, da aka gayyata. 9 In kuwa haka ne, wanda ya gayyace duk biyunku, zai zo ya ce maka, ‘Ka ba wa mutumin nan wurin zamanka.’ Ka ga, an ƙasƙantar da kai, kuma dole ka ɗauki wuri mafi ƙasƙanci. 10 Amma in an gayyace ka, ɗauki wuri mafi ƙasƙanci, don in wanda ya gayyace ka ya zo, zai ce maka, ‘Ka hawo nan aboki a wuri mafi girma.’ Wannan zai ɗaukaka ka a gaban dukan ’yan’uwanka baƙi. 11 Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Shi wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.” 12 Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu. 13 Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi. 14 Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.” 15 Da jin haka, sai wani da yake tare da shi a tebur ɗin, ya ce wa Yesu, “Mai albarka ne wanda zai ci abinci a bikin nan a mulkin Allah.” 16 Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa. 17 Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, don an shirya kome.’ 18 “Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce, ‘Na sayi gona yanzun nan, dole in je in ga yadda take, ina roƙonka ka yi mini haƙuri.’ 19 “Wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma yanzun nan, ina kan hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’ 20 “Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’ 21 “Bawansa ya dawo ya gaya wa maigidansa wannan. Sai maigidan ya yi fushi, ya ba da umarni ga bawansa ya ce, ‘Ka fita da sauri, ka bi titi-titi da lungu-lungu na garin, ka kawo matalauta, da guragu, da makafi, da shanyayyu.’ 22 “Bawan ya dawo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, an yi abin da ka umarta, amma har yanzu da sauran wuri.’ 23 “Maigidan ya ce wa bawansa, ‘Ka je kan hanyoyin da layi-layi na karkara, ka sa su shigo, don gidana ya cika.’ 24 Ina gaya muku, babu ko ɗaya daga cikin mutanen nan da aka gayyata da zai ɗanɗana bikina.” 25 Taron mutane mai yawa suna tafiya tare da Yesu, sai ya juya ya ce musu, 26 “Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. 27 Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. 28 “In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin. 29 Gama in ya sa tushen gini, amma bai iya gamawa ba, duk wanda ya gani zai yi masa ba’a, 30 yana cewa, ‘Wannan mutum ya fara gini, amma bai iya gamawa ba.’ 31 “Ko kuma, wane sarki ne, in zai je yaƙi da wani sarki, ai, yakan fara zama ne, ya duba ya ga, ko da mutane dubu goma, shi zai iya ƙarawa da mai zuwa da dubu ashirin? 32 In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama. 33 Haka nan fa, kowane ne a cikinku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba. 34 “Gishiri fa yana da kyau, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? 35 Ba shi da wani amfani, ko ga ƙasa, ko ga juji, sai dai a zubar da shi. “Duk mai kunnen ji, yă ji.”