Luke 15 (BOHCB)

1 Yanzu fa, masu karɓar haraji da “masu zunubi” duka suna taruwa don jin koyarwar Yesu. 2 Amma Farisiyawa da malaman dokoki suka yi gunaguni, suna cewa, “Wannan mutum yana karɓan ‘masu zunubi,’ kuma yana ci tare da su.” 3 Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali ya ce, 4 “In ɗayanku yana da tumaki ɗari, sa’an nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasa’in da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba? 5 In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna, 6 ya dawo gida. Sa’an nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya ya ce, ‘Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata.’ 7 Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba. 8 “Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, sa’an nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za tă ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba? 9 In ta same shi, sai ta kira ƙawayenta da maƙwabtanta wuri ɗaya, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, na sami kuɗina da ya ɓata.’ 10 Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.” 11 Yesu ya ci gaba da cewa, “Akwai wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. 12 Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa. 13 “Bayan ’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza. 14 Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi. 15 Sai ya je ya sami aiki a wurin wani mutumin ƙasar, wanda ya aike shi a gonakinsa, ya yi kiwon aladu. 16 Ya yi marmarin cin dusan da aladun suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu. 17 “Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa! 18 Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. 19 Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’ 20 Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa. “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba. 21 “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’ 22 “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa. 23 Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali. 24 Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali. 25 “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa. 26 Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa. 27 Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’ 28 “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi. 29 Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba. 30 Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’ 31 “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne. 32 Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ”

In Other Versions

Luke 15 in the ANGEFD

Luke 15 in the ANTPNG2D

Luke 15 in the AS21

Luke 15 in the BAGH

Luke 15 in the BBPNG

Luke 15 in the BBT1E

Luke 15 in the BDS

Luke 15 in the BEV

Luke 15 in the BHAD

Luke 15 in the BIB

Luke 15 in the BLPT

Luke 15 in the BNT

Luke 15 in the BNTABOOT

Luke 15 in the BNTLV

Luke 15 in the BOATCB

Luke 15 in the BOATCB2

Luke 15 in the BOBCV

Luke 15 in the BOCNT

Luke 15 in the BOECS

Luke 15 in the BOGWICC

Luke 15 in the BOHCV

Luke 15 in the BOHLNT

Luke 15 in the BOHNTLTAL

Luke 15 in the BOICB

Luke 15 in the BOILNTAP

Luke 15 in the BOITCV

Luke 15 in the BOKCV

Luke 15 in the BOKCV2

Luke 15 in the BOKHWOG

Luke 15 in the BOKSSV

Luke 15 in the BOLCB

Luke 15 in the BOLCB2

Luke 15 in the BOMCV

Luke 15 in the BONAV

Luke 15 in the BONCB

Luke 15 in the BONLT

Luke 15 in the BONUT2

Luke 15 in the BOPLNT

Luke 15 in the BOSCB

Luke 15 in the BOSNC

Luke 15 in the BOTLNT

Luke 15 in the BOVCB

Luke 15 in the BOYCB

Luke 15 in the BPBB

Luke 15 in the BPH

Luke 15 in the BSB

Luke 15 in the CCB

Luke 15 in the CUV

Luke 15 in the CUVS

Luke 15 in the DBT

Luke 15 in the DGDNT

Luke 15 in the DHNT

Luke 15 in the DNT

Luke 15 in the ELBE

Luke 15 in the EMTV

Luke 15 in the ESV

Luke 15 in the FBV

Luke 15 in the FEB

Luke 15 in the GGMNT

Luke 15 in the GNT

Luke 15 in the HARY

Luke 15 in the HNT

Luke 15 in the IRVA

Luke 15 in the IRVB

Luke 15 in the IRVG

Luke 15 in the IRVH

Luke 15 in the IRVK

Luke 15 in the IRVM

Luke 15 in the IRVM2

Luke 15 in the IRVO

Luke 15 in the IRVP

Luke 15 in the IRVT

Luke 15 in the IRVT2

Luke 15 in the IRVU

Luke 15 in the ISVN

Luke 15 in the JSNT

Luke 15 in the KAPI

Luke 15 in the KBT1ETNIK

Luke 15 in the KBV

Luke 15 in the KJV

Luke 15 in the KNFD

Luke 15 in the LBA

Luke 15 in the LBLA

Luke 15 in the LNT

Luke 15 in the LSV

Luke 15 in the MAAL

Luke 15 in the MBV

Luke 15 in the MBV2

Luke 15 in the MHNT

Luke 15 in the MKNFD

Luke 15 in the MNG

Luke 15 in the MNT

Luke 15 in the MNT2

Luke 15 in the MRS1T

Luke 15 in the NAA

Luke 15 in the NASB

Luke 15 in the NBLA

Luke 15 in the NBS

Luke 15 in the NBVTP

Luke 15 in the NET2

Luke 15 in the NIV11

Luke 15 in the NNT

Luke 15 in the NNT2

Luke 15 in the NNT3

Luke 15 in the PDDPT

Luke 15 in the PFNT

Luke 15 in the RMNT

Luke 15 in the SBIAS

Luke 15 in the SBIBS

Luke 15 in the SBIBS2

Luke 15 in the SBICS

Luke 15 in the SBIDS

Luke 15 in the SBIGS

Luke 15 in the SBIHS

Luke 15 in the SBIIS

Luke 15 in the SBIIS2

Luke 15 in the SBIIS3

Luke 15 in the SBIKS

Luke 15 in the SBIKS2

Luke 15 in the SBIMS

Luke 15 in the SBIOS

Luke 15 in the SBIPS

Luke 15 in the SBISS

Luke 15 in the SBITS

Luke 15 in the SBITS2

Luke 15 in the SBITS3

Luke 15 in the SBITS4

Luke 15 in the SBIUS

Luke 15 in the SBIVS

Luke 15 in the SBT

Luke 15 in the SBT1E

Luke 15 in the SCHL

Luke 15 in the SNT

Luke 15 in the SUSU

Luke 15 in the SUSU2

Luke 15 in the SYNO

Luke 15 in the TBIAOTANT

Luke 15 in the TBT1E

Luke 15 in the TBT1E2

Luke 15 in the TFTIP

Luke 15 in the TFTU

Luke 15 in the TGNTATF3T

Luke 15 in the THAI

Luke 15 in the TNFD

Luke 15 in the TNT

Luke 15 in the TNTIK

Luke 15 in the TNTIL

Luke 15 in the TNTIN

Luke 15 in the TNTIP

Luke 15 in the TNTIZ

Luke 15 in the TOMA

Luke 15 in the TTENT

Luke 15 in the UBG

Luke 15 in the UGV

Luke 15 in the UGV2

Luke 15 in the UGV3

Luke 15 in the VBL

Luke 15 in the VDCC

Luke 15 in the YALU

Luke 15 in the YAPE

Luke 15 in the YBVTP

Luke 15 in the ZBP