Luke 20 (BOHCB)

1 Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa. 2 Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?” 3 Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini, 4 baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?” 5 Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 6 Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.” 7 Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.” 8 Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.” 9 Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya. 10 A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi. 11 Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi. 12 Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje. 13 “Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’ 14 “Amma da ’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’ 15 Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi. “To, me mai gonar inabin zai yi da su? 16 Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.”Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!” 17 Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’, 18 Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.” 19 Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane. 20 Sai suka sa masa ido, suka aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko. 21 Sai ’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. 22 Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?” 23 Ya gane makircinsu, sai ya ce musu, 24 “Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?”Suka amsa, “Na Kaisar.” 25 Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.” 26 Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru. 27 Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa, 28 “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’ 29 To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya. 30 Na biyun, 31 da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya. 32 A ƙarshe, ita macen ma ta mutu. 33 Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.” 34 Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, 35 amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba. 36 Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne. 37 Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’ 38 Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.” 39 Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!” 40 Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi. 41 Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’ 42 Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, 43 sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’ 44 Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?” 45 Yayinda dukan mutane suna cikin sauraronsa, sai Yesu ya ce wa almajiransa, 46 “Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna sha’awan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majami’u, da wuraren bangirma a bukukkuwa. 47 Suna mamaye gidajen gwauraye, kuma don burga, suna dogayen addu’o’i. Ga irin waɗannan mutane, za a yi musu hukunci mai tsanani sosai.”

In Other Versions

Luke 20 in the ANGEFD

Luke 20 in the ANTPNG2D

Luke 20 in the AS21

Luke 20 in the BAGH

Luke 20 in the BBPNG

Luke 20 in the BBT1E

Luke 20 in the BDS

Luke 20 in the BEV

Luke 20 in the BHAD

Luke 20 in the BIB

Luke 20 in the BLPT

Luke 20 in the BNT

Luke 20 in the BNTABOOT

Luke 20 in the BNTLV

Luke 20 in the BOATCB

Luke 20 in the BOATCB2

Luke 20 in the BOBCV

Luke 20 in the BOCNT

Luke 20 in the BOECS

Luke 20 in the BOGWICC

Luke 20 in the BOHCV

Luke 20 in the BOHLNT

Luke 20 in the BOHNTLTAL

Luke 20 in the BOICB

Luke 20 in the BOILNTAP

Luke 20 in the BOITCV

Luke 20 in the BOKCV

Luke 20 in the BOKCV2

Luke 20 in the BOKHWOG

Luke 20 in the BOKSSV

Luke 20 in the BOLCB

Luke 20 in the BOLCB2

Luke 20 in the BOMCV

Luke 20 in the BONAV

Luke 20 in the BONCB

Luke 20 in the BONLT

Luke 20 in the BONUT2

Luke 20 in the BOPLNT

Luke 20 in the BOSCB

Luke 20 in the BOSNC

Luke 20 in the BOTLNT

Luke 20 in the BOVCB

Luke 20 in the BOYCB

Luke 20 in the BPBB

Luke 20 in the BPH

Luke 20 in the BSB

Luke 20 in the CCB

Luke 20 in the CUV

Luke 20 in the CUVS

Luke 20 in the DBT

Luke 20 in the DGDNT

Luke 20 in the DHNT

Luke 20 in the DNT

Luke 20 in the ELBE

Luke 20 in the EMTV

Luke 20 in the ESV

Luke 20 in the FBV

Luke 20 in the FEB

Luke 20 in the GGMNT

Luke 20 in the GNT

Luke 20 in the HARY

Luke 20 in the HNT

Luke 20 in the IRVA

Luke 20 in the IRVB

Luke 20 in the IRVG

Luke 20 in the IRVH

Luke 20 in the IRVK

Luke 20 in the IRVM

Luke 20 in the IRVM2

Luke 20 in the IRVO

Luke 20 in the IRVP

Luke 20 in the IRVT

Luke 20 in the IRVT2

Luke 20 in the IRVU

Luke 20 in the ISVN

Luke 20 in the JSNT

Luke 20 in the KAPI

Luke 20 in the KBT1ETNIK

Luke 20 in the KBV

Luke 20 in the KJV

Luke 20 in the KNFD

Luke 20 in the LBA

Luke 20 in the LBLA

Luke 20 in the LNT

Luke 20 in the LSV

Luke 20 in the MAAL

Luke 20 in the MBV

Luke 20 in the MBV2

Luke 20 in the MHNT

Luke 20 in the MKNFD

Luke 20 in the MNG

Luke 20 in the MNT

Luke 20 in the MNT2

Luke 20 in the MRS1T

Luke 20 in the NAA

Luke 20 in the NASB

Luke 20 in the NBLA

Luke 20 in the NBS

Luke 20 in the NBVTP

Luke 20 in the NET2

Luke 20 in the NIV11

Luke 20 in the NNT

Luke 20 in the NNT2

Luke 20 in the NNT3

Luke 20 in the PDDPT

Luke 20 in the PFNT

Luke 20 in the RMNT

Luke 20 in the SBIAS

Luke 20 in the SBIBS

Luke 20 in the SBIBS2

Luke 20 in the SBICS

Luke 20 in the SBIDS

Luke 20 in the SBIGS

Luke 20 in the SBIHS

Luke 20 in the SBIIS

Luke 20 in the SBIIS2

Luke 20 in the SBIIS3

Luke 20 in the SBIKS

Luke 20 in the SBIKS2

Luke 20 in the SBIMS

Luke 20 in the SBIOS

Luke 20 in the SBIPS

Luke 20 in the SBISS

Luke 20 in the SBITS

Luke 20 in the SBITS2

Luke 20 in the SBITS3

Luke 20 in the SBITS4

Luke 20 in the SBIUS

Luke 20 in the SBIVS

Luke 20 in the SBT

Luke 20 in the SBT1E

Luke 20 in the SCHL

Luke 20 in the SNT

Luke 20 in the SUSU

Luke 20 in the SUSU2

Luke 20 in the SYNO

Luke 20 in the TBIAOTANT

Luke 20 in the TBT1E

Luke 20 in the TBT1E2

Luke 20 in the TFTIP

Luke 20 in the TFTU

Luke 20 in the TGNTATF3T

Luke 20 in the THAI

Luke 20 in the TNFD

Luke 20 in the TNT

Luke 20 in the TNTIK

Luke 20 in the TNTIL

Luke 20 in the TNTIN

Luke 20 in the TNTIP

Luke 20 in the TNTIZ

Luke 20 in the TOMA

Luke 20 in the TTENT

Luke 20 in the UBG

Luke 20 in the UGV

Luke 20 in the UGV2

Luke 20 in the UGV3

Luke 20 in the VBL

Luke 20 in the VDCC

Luke 20 in the YALU

Luke 20 in the YAPE

Luke 20 in the YBVTP

Luke 20 in the ZBP