Luke 4 (BOHCB)
1 Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada, 2 inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa. 3 Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.” 4 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’” 5 Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya. 6 Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama. 7 Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.” 8 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’” 9 Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa. 10 Gama a rubuce yake,“ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,su kiyaye ka da kyau; 11 za su tallafe ka da hannuwansu,don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’” 12 Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’” 13 Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu. 14 Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a ƙauyuka. 15 Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, kowa kuwa ya yabe shi. 16 Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu. 17 Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta, 18 “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne. 19 In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.” 20 Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa. 21 Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.” 22 Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?” 23 Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ” 24 Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa. 25 Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar. 26 Duk da haka, ba a aiki Iliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon. 27 Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.” 28 Dukan mutanen da suke cikin majami’a suka fusata ƙwarai da jin wannan. 29 Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa, 30 amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa. 31 Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a Galili, a ranar Asabbaci kuma, ya fara koya wa mutane. 32 Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin saƙonsa yana da iko. 33 A cikin majami’ar, akwai wani mutum mai aljani, wani mugun ruhu. Mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, 34 “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki na Allah!” 35 Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, “Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!” Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, sa’an nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni. 36 Dukan mutanen suka yi mamaki, suka ce wa junansu, “Wace irin koyarwa ce haka? Da ƙarfi da iko, yana ba wa mugayen ruhohin umarni suna kuma fita!” 37 Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a cikin ƙasar. 38 Yesu ya fita daga majami’ar, ya tafi gidan Siman. Surukar Siman kuwa tana fama da zazzaɓi mai tsanani, sai suka roƙi Yesu yă taimake ta. 39 Sai ya sunkuya kusa da ita, ya kuma tsawata wa zazzaɓin, sai zazzaɓin ya sāke ta. Nan take ta tashi, ta yi musu hidima. 40 Rana tana fāɗuwa, sai mutane suka yi ta kawo wa Yesu dukan waɗanda suke da cuta iri-iri, sai ya ɗibiya wa kowannensu hannuwansa, ya warkar da su. 41 Bugu da ƙari, aljanu suka fiffita daga cikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya kwaɓe su, ya hana su magana, don sun san cewa shi ne Kiristi. 42 Da gari yana wayewa, sai Yesu ya je inda ba kowa. Mutane suka yi ta nemansa, da suka zo inda yake, sai suka yi ƙoƙari su hana shi barinsu. 43 Amma ya ce, “Dole in yi wa’azin bisharar mulkin Allah ga sauran garuruwa, saboda wannan ne aka aiko ni.” 44 Sai ya dinga yin wa’azi a majami’un Yahudiya.