Matthew 16 (BOHCB)
1 Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama. 2 Ya amsa ya ce, “Sa’ad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja,’ 3 da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokuta. 4 Wannan mugu da mazinacin zamani yana neman wani abin banmamaki, amma ba wata alamar da za a nuna wa wannan zamani sai dai ta Yunana.” Sai Yesu ya bar su ya tafi abinsa. 5 Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi. 6 Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku yi taka zallan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.” 7 Sai suka fara tattaunawa da junansu suna cewa, “Ko don ba mu kawo burodi ba ne.” 8 Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba? 9 Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike? 10 Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka? 11 Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.” 12 Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne. 13 Sa’ad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?” 14 Suka amsa, “Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Iliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.” 15 Ya tambaye su, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?” 16 Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai.” 17 Yesu ya amsa ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama. 18 Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hades ba za su rinjaye ta ba. 19 Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.” 20 Sa’an nan ya gargaɗe almajiransa cewa kada su faɗa wa kowa shi ne Kiristi. 21 Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi. 22 Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!” 23 Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.” 24 Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni. 25 Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi. 26 Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa? 27 Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi. 28 “Gaskiya nake gaya muku, akwai waɗansu da suke tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.”
In Other Versions
Matthew 16 in the ANGEFD
Matthew 16 in the ANTPNG2D
Matthew 16 in the AS21
Matthew 16 in the BAGH
Matthew 16 in the BBPNG
Matthew 16 in the BBT1E
Matthew 16 in the BDS
Matthew 16 in the BEV
Matthew 16 in the BHAD
Matthew 16 in the BIB
Matthew 16 in the BLPT
Matthew 16 in the BNT
Matthew 16 in the BNTABOOT
Matthew 16 in the BNTLV
Matthew 16 in the BOATCB
Matthew 16 in the BOATCB2
Matthew 16 in the BOBCV
Matthew 16 in the BOCNT
Matthew 16 in the BOECS
Matthew 16 in the BOGWICC
Matthew 16 in the BOHCV
Matthew 16 in the BOHLNT
Matthew 16 in the BOHNTLTAL
Matthew 16 in the BOICB
Matthew 16 in the BOILNTAP
Matthew 16 in the BOITCV
Matthew 16 in the BOKCV
Matthew 16 in the BOKCV2
Matthew 16 in the BOKHWOG
Matthew 16 in the BOKSSV
Matthew 16 in the BOLCB
Matthew 16 in the BOLCB2
Matthew 16 in the BOMCV
Matthew 16 in the BONAV
Matthew 16 in the BONCB
Matthew 16 in the BONLT
Matthew 16 in the BONUT2
Matthew 16 in the BOPLNT
Matthew 16 in the BOSCB
Matthew 16 in the BOSNC
Matthew 16 in the BOTLNT
Matthew 16 in the BOVCB
Matthew 16 in the BOYCB
Matthew 16 in the BPBB
Matthew 16 in the BPH
Matthew 16 in the BSB
Matthew 16 in the CCB
Matthew 16 in the CUV
Matthew 16 in the CUVS
Matthew 16 in the DBT
Matthew 16 in the DGDNT
Matthew 16 in the DHNT
Matthew 16 in the DNT
Matthew 16 in the ELBE
Matthew 16 in the EMTV
Matthew 16 in the ESV
Matthew 16 in the FBV
Matthew 16 in the FEB
Matthew 16 in the GGMNT
Matthew 16 in the GNT
Matthew 16 in the HARY
Matthew 16 in the HNT
Matthew 16 in the IRVA
Matthew 16 in the IRVB
Matthew 16 in the IRVG
Matthew 16 in the IRVH
Matthew 16 in the IRVK
Matthew 16 in the IRVM
Matthew 16 in the IRVM2
Matthew 16 in the IRVO
Matthew 16 in the IRVP
Matthew 16 in the IRVT
Matthew 16 in the IRVT2
Matthew 16 in the IRVU
Matthew 16 in the ISVN
Matthew 16 in the JSNT
Matthew 16 in the KAPI
Matthew 16 in the KBT1ETNIK
Matthew 16 in the KBV
Matthew 16 in the KJV
Matthew 16 in the KNFD
Matthew 16 in the LBA
Matthew 16 in the LBLA
Matthew 16 in the LNT
Matthew 16 in the LSV
Matthew 16 in the MAAL
Matthew 16 in the MBV
Matthew 16 in the MBV2
Matthew 16 in the MHNT
Matthew 16 in the MKNFD
Matthew 16 in the MNG
Matthew 16 in the MNT
Matthew 16 in the MNT2
Matthew 16 in the MRS1T
Matthew 16 in the NAA
Matthew 16 in the NASB
Matthew 16 in the NBLA
Matthew 16 in the NBS
Matthew 16 in the NBVTP
Matthew 16 in the NET2
Matthew 16 in the NIV11
Matthew 16 in the NNT
Matthew 16 in the NNT2
Matthew 16 in the NNT3
Matthew 16 in the PDDPT
Matthew 16 in the PFNT
Matthew 16 in the RMNT
Matthew 16 in the SBIAS
Matthew 16 in the SBIBS
Matthew 16 in the SBIBS2
Matthew 16 in the SBICS
Matthew 16 in the SBIDS
Matthew 16 in the SBIGS
Matthew 16 in the SBIHS
Matthew 16 in the SBIIS
Matthew 16 in the SBIIS2
Matthew 16 in the SBIIS3
Matthew 16 in the SBIKS
Matthew 16 in the SBIKS2
Matthew 16 in the SBIMS
Matthew 16 in the SBIOS
Matthew 16 in the SBIPS
Matthew 16 in the SBISS
Matthew 16 in the SBITS
Matthew 16 in the SBITS2
Matthew 16 in the SBITS3
Matthew 16 in the SBITS4
Matthew 16 in the SBIUS
Matthew 16 in the SBIVS
Matthew 16 in the SBT
Matthew 16 in the SBT1E
Matthew 16 in the SCHL
Matthew 16 in the SNT
Matthew 16 in the SUSU
Matthew 16 in the SUSU2
Matthew 16 in the SYNO
Matthew 16 in the TBIAOTANT
Matthew 16 in the TBT1E
Matthew 16 in the TBT1E2
Matthew 16 in the TFTIP
Matthew 16 in the TFTU
Matthew 16 in the TGNTATF3T
Matthew 16 in the THAI
Matthew 16 in the TNFD
Matthew 16 in the TNT
Matthew 16 in the TNTIK
Matthew 16 in the TNTIL
Matthew 16 in the TNTIN
Matthew 16 in the TNTIP
Matthew 16 in the TNTIZ
Matthew 16 in the TOMA
Matthew 16 in the TTENT
Matthew 16 in the UBG
Matthew 16 in the UGV
Matthew 16 in the UGV2
Matthew 16 in the UGV3
Matthew 16 in the VBL
Matthew 16 in the VDCC
Matthew 16 in the YALU
Matthew 16 in the YAPE
Matthew 16 in the YBVTP
Matthew 16 in the ZBP