Matthew 21 (BOHCB)

1 Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu, 2 yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini. 3 In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.” 4 Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa, 5 “Ku ce wa Diyar Sihiyona,‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki,mai tawali’u yana a kan jaki,a kan aholaki, ɗan jaki.’ ” 6 Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. 7 Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu. 8 Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya. 9 Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa,“Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!” 10 Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?” 11 Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.” 12 Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. 13 Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’ amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ” 14 Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su. 15 Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su. 16 Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?”Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa, “ ‘Daga leɓunan yara da jarirai kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?” 17 Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana. 18 Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa. 19 Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane. 20 Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?” 21 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru. 22 In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.” 23 Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?” 24 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. 25 Baftismar Yohanna, daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?”Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’ 26 In kuma muka ce, ‘Daga mutane,’ muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.” 27 Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.” 28 “Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’ 29 “Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi. 30 “Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba. 31 “Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?”Suka amsa, “Na farin.”Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah. 32 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.” 33 “Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya. 34 Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ’yan hayan, su karɓo masa ’ya’yan inabi. 35 “Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun. 36 Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin. 37 A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’ 38 “Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’ 39 Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi. 40 “To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da ’yan hayan nan?” 41 Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.” 42 Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi ne ya zama dutsen kusurwar gini. Ubangiji ne ya aikata wannan, kuma abin mamaki ne a idanunmu’? 43 “Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani. 44 Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.” 45 Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake. 46 Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne.

In Other Versions

Matthew 21 in the ANGEFD

Matthew 21 in the ANTPNG2D

Matthew 21 in the AS21

Matthew 21 in the BAGH

Matthew 21 in the BBPNG

Matthew 21 in the BBT1E

Matthew 21 in the BDS

Matthew 21 in the BEV

Matthew 21 in the BHAD

Matthew 21 in the BIB

Matthew 21 in the BLPT

Matthew 21 in the BNT

Matthew 21 in the BNTABOOT

Matthew 21 in the BNTLV

Matthew 21 in the BOATCB

Matthew 21 in the BOATCB2

Matthew 21 in the BOBCV

Matthew 21 in the BOCNT

Matthew 21 in the BOECS

Matthew 21 in the BOGWICC

Matthew 21 in the BOHCV

Matthew 21 in the BOHLNT

Matthew 21 in the BOHNTLTAL

Matthew 21 in the BOICB

Matthew 21 in the BOILNTAP

Matthew 21 in the BOITCV

Matthew 21 in the BOKCV

Matthew 21 in the BOKCV2

Matthew 21 in the BOKHWOG

Matthew 21 in the BOKSSV

Matthew 21 in the BOLCB

Matthew 21 in the BOLCB2

Matthew 21 in the BOMCV

Matthew 21 in the BONAV

Matthew 21 in the BONCB

Matthew 21 in the BONLT

Matthew 21 in the BONUT2

Matthew 21 in the BOPLNT

Matthew 21 in the BOSCB

Matthew 21 in the BOSNC

Matthew 21 in the BOTLNT

Matthew 21 in the BOVCB

Matthew 21 in the BOYCB

Matthew 21 in the BPBB

Matthew 21 in the BPH

Matthew 21 in the BSB

Matthew 21 in the CCB

Matthew 21 in the CUV

Matthew 21 in the CUVS

Matthew 21 in the DBT

Matthew 21 in the DGDNT

Matthew 21 in the DHNT

Matthew 21 in the DNT

Matthew 21 in the ELBE

Matthew 21 in the EMTV

Matthew 21 in the ESV

Matthew 21 in the FBV

Matthew 21 in the FEB

Matthew 21 in the GGMNT

Matthew 21 in the GNT

Matthew 21 in the HARY

Matthew 21 in the HNT

Matthew 21 in the IRVA

Matthew 21 in the IRVB

Matthew 21 in the IRVG

Matthew 21 in the IRVH

Matthew 21 in the IRVK

Matthew 21 in the IRVM

Matthew 21 in the IRVM2

Matthew 21 in the IRVO

Matthew 21 in the IRVP

Matthew 21 in the IRVT

Matthew 21 in the IRVT2

Matthew 21 in the IRVU

Matthew 21 in the ISVN

Matthew 21 in the JSNT

Matthew 21 in the KAPI

Matthew 21 in the KBT1ETNIK

Matthew 21 in the KBV

Matthew 21 in the KJV

Matthew 21 in the KNFD

Matthew 21 in the LBA

Matthew 21 in the LBLA

Matthew 21 in the LNT

Matthew 21 in the LSV

Matthew 21 in the MAAL

Matthew 21 in the MBV

Matthew 21 in the MBV2

Matthew 21 in the MHNT

Matthew 21 in the MKNFD

Matthew 21 in the MNG

Matthew 21 in the MNT

Matthew 21 in the MNT2

Matthew 21 in the MRS1T

Matthew 21 in the NAA

Matthew 21 in the NASB

Matthew 21 in the NBLA

Matthew 21 in the NBS

Matthew 21 in the NBVTP

Matthew 21 in the NET2

Matthew 21 in the NIV11

Matthew 21 in the NNT

Matthew 21 in the NNT2

Matthew 21 in the NNT3

Matthew 21 in the PDDPT

Matthew 21 in the PFNT

Matthew 21 in the RMNT

Matthew 21 in the SBIAS

Matthew 21 in the SBIBS

Matthew 21 in the SBIBS2

Matthew 21 in the SBICS

Matthew 21 in the SBIDS

Matthew 21 in the SBIGS

Matthew 21 in the SBIHS

Matthew 21 in the SBIIS

Matthew 21 in the SBIIS2

Matthew 21 in the SBIIS3

Matthew 21 in the SBIKS

Matthew 21 in the SBIKS2

Matthew 21 in the SBIMS

Matthew 21 in the SBIOS

Matthew 21 in the SBIPS

Matthew 21 in the SBISS

Matthew 21 in the SBITS

Matthew 21 in the SBITS2

Matthew 21 in the SBITS3

Matthew 21 in the SBITS4

Matthew 21 in the SBIUS

Matthew 21 in the SBIVS

Matthew 21 in the SBT

Matthew 21 in the SBT1E

Matthew 21 in the SCHL

Matthew 21 in the SNT

Matthew 21 in the SUSU

Matthew 21 in the SUSU2

Matthew 21 in the SYNO

Matthew 21 in the TBIAOTANT

Matthew 21 in the TBT1E

Matthew 21 in the TBT1E2

Matthew 21 in the TFTIP

Matthew 21 in the TFTU

Matthew 21 in the TGNTATF3T

Matthew 21 in the THAI

Matthew 21 in the TNFD

Matthew 21 in the TNT

Matthew 21 in the TNTIK

Matthew 21 in the TNTIL

Matthew 21 in the TNTIN

Matthew 21 in the TNTIP

Matthew 21 in the TNTIZ

Matthew 21 in the TOMA

Matthew 21 in the TTENT

Matthew 21 in the UBG

Matthew 21 in the UGV

Matthew 21 in the UGV2

Matthew 21 in the UGV3

Matthew 21 in the VBL

Matthew 21 in the VDCC

Matthew 21 in the YALU

Matthew 21 in the YAPE

Matthew 21 in the YBVTP

Matthew 21 in the ZBP