Matthew 24 (BOHCB)

1 Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya sai almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali. 2 Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.” 3 Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?” 4 Yesu ya amsa, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku. 5 Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa. 6 Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna. 7 Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam. 8 Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne. 9 “Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni. 10 A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna, 11 annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa. 12 Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi, 13 amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto. 14 Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo. 15 “Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’ wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane), 16 to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. 17 Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida. 18 Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa. 19 Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin! 20 Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci. 21 Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba. 22 “Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin. 23 A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. 24 Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 25 Ga shi, na faɗa muku tun da wuri. 26 “Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata. 27 Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance. 28 Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru. 29 “Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “ ‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’ 30 “A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma. 31 Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. 32 “Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa. 33 Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa. 34 Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru. 35 Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba. 36 “Babu wanda ya san wannan rana ko sa’a, ko mala’ikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. 37 Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 38 Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi; 39 ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 40 Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya. 41 Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya. 42 “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba. 43 Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida. 44 Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba. 45 “Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci? 46 Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka. 47 Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa. 48 Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’ 49 Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. 50 Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba. 51 Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

In Other Versions

Matthew 24 in the ANGEFD

Matthew 24 in the ANTPNG2D

Matthew 24 in the AS21

Matthew 24 in the BAGH

Matthew 24 in the BBPNG

Matthew 24 in the BBT1E

Matthew 24 in the BDS

Matthew 24 in the BEV

Matthew 24 in the BHAD

Matthew 24 in the BIB

Matthew 24 in the BLPT

Matthew 24 in the BNT

Matthew 24 in the BNTABOOT

Matthew 24 in the BNTLV

Matthew 24 in the BOATCB

Matthew 24 in the BOATCB2

Matthew 24 in the BOBCV

Matthew 24 in the BOCNT

Matthew 24 in the BOECS

Matthew 24 in the BOGWICC

Matthew 24 in the BOHCV

Matthew 24 in the BOHLNT

Matthew 24 in the BOHNTLTAL

Matthew 24 in the BOICB

Matthew 24 in the BOILNTAP

Matthew 24 in the BOITCV

Matthew 24 in the BOKCV

Matthew 24 in the BOKCV2

Matthew 24 in the BOKHWOG

Matthew 24 in the BOKSSV

Matthew 24 in the BOLCB

Matthew 24 in the BOLCB2

Matthew 24 in the BOMCV

Matthew 24 in the BONAV

Matthew 24 in the BONCB

Matthew 24 in the BONLT

Matthew 24 in the BONUT2

Matthew 24 in the BOPLNT

Matthew 24 in the BOSCB

Matthew 24 in the BOSNC

Matthew 24 in the BOTLNT

Matthew 24 in the BOVCB

Matthew 24 in the BOYCB

Matthew 24 in the BPBB

Matthew 24 in the BPH

Matthew 24 in the BSB

Matthew 24 in the CCB

Matthew 24 in the CUV

Matthew 24 in the CUVS

Matthew 24 in the DBT

Matthew 24 in the DGDNT

Matthew 24 in the DHNT

Matthew 24 in the DNT

Matthew 24 in the ELBE

Matthew 24 in the EMTV

Matthew 24 in the ESV

Matthew 24 in the FBV

Matthew 24 in the FEB

Matthew 24 in the GGMNT

Matthew 24 in the GNT

Matthew 24 in the HARY

Matthew 24 in the HNT

Matthew 24 in the IRVA

Matthew 24 in the IRVB

Matthew 24 in the IRVG

Matthew 24 in the IRVH

Matthew 24 in the IRVK

Matthew 24 in the IRVM

Matthew 24 in the IRVM2

Matthew 24 in the IRVO

Matthew 24 in the IRVP

Matthew 24 in the IRVT

Matthew 24 in the IRVT2

Matthew 24 in the IRVU

Matthew 24 in the ISVN

Matthew 24 in the JSNT

Matthew 24 in the KAPI

Matthew 24 in the KBT1ETNIK

Matthew 24 in the KBV

Matthew 24 in the KJV

Matthew 24 in the KNFD

Matthew 24 in the LBA

Matthew 24 in the LBLA

Matthew 24 in the LNT

Matthew 24 in the LSV

Matthew 24 in the MAAL

Matthew 24 in the MBV

Matthew 24 in the MBV2

Matthew 24 in the MHNT

Matthew 24 in the MKNFD

Matthew 24 in the MNG

Matthew 24 in the MNT

Matthew 24 in the MNT2

Matthew 24 in the MRS1T

Matthew 24 in the NAA

Matthew 24 in the NASB

Matthew 24 in the NBLA

Matthew 24 in the NBS

Matthew 24 in the NBVTP

Matthew 24 in the NET2

Matthew 24 in the NIV11

Matthew 24 in the NNT

Matthew 24 in the NNT2

Matthew 24 in the NNT3

Matthew 24 in the PDDPT

Matthew 24 in the PFNT

Matthew 24 in the RMNT

Matthew 24 in the SBIAS

Matthew 24 in the SBIBS

Matthew 24 in the SBIBS2

Matthew 24 in the SBICS

Matthew 24 in the SBIDS

Matthew 24 in the SBIGS

Matthew 24 in the SBIHS

Matthew 24 in the SBIIS

Matthew 24 in the SBIIS2

Matthew 24 in the SBIIS3

Matthew 24 in the SBIKS

Matthew 24 in the SBIKS2

Matthew 24 in the SBIMS

Matthew 24 in the SBIOS

Matthew 24 in the SBIPS

Matthew 24 in the SBISS

Matthew 24 in the SBITS

Matthew 24 in the SBITS2

Matthew 24 in the SBITS3

Matthew 24 in the SBITS4

Matthew 24 in the SBIUS

Matthew 24 in the SBIVS

Matthew 24 in the SBT

Matthew 24 in the SBT1E

Matthew 24 in the SCHL

Matthew 24 in the SNT

Matthew 24 in the SUSU

Matthew 24 in the SUSU2

Matthew 24 in the SYNO

Matthew 24 in the TBIAOTANT

Matthew 24 in the TBT1E

Matthew 24 in the TBT1E2

Matthew 24 in the TFTIP

Matthew 24 in the TFTU

Matthew 24 in the TGNTATF3T

Matthew 24 in the THAI

Matthew 24 in the TNFD

Matthew 24 in the TNT

Matthew 24 in the TNTIK

Matthew 24 in the TNTIL

Matthew 24 in the TNTIN

Matthew 24 in the TNTIP

Matthew 24 in the TNTIZ

Matthew 24 in the TOMA

Matthew 24 in the TTENT

Matthew 24 in the UBG

Matthew 24 in the UGV

Matthew 24 in the UGV2

Matthew 24 in the UGV3

Matthew 24 in the VBL

Matthew 24 in the VDCC

Matthew 24 in the YALU

Matthew 24 in the YAPE

Matthew 24 in the YBVTP

Matthew 24 in the ZBP