Matthew 4 (BOHCB)
1 Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. 2 Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa. 3 Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.” 4 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’” 5 Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali. 6 Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake,“ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,za su tallafe ka da hannuwansu,don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’” 7 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’” 8 Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9 Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.” 10 Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’” 11 Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima. 12 Da Yesu ya ji labari cewa an kulle Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili. 13 Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali 14 don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, 15 “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali,da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun,wannan yankin Galili ta Al’ummai, 16 mutanen da suke zama cikin duhusun ga babban haske;haske kuma ya haskakaa kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.” 17 Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.” 18 Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne. 19 Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.” 20 Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi. 21 Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su, 22 nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu. 23 Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane. 24 Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su. 25 Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis, Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi.
In Other Versions
Matthew 4 in the ANGEFD
Matthew 4 in the ANTPNG2D
Matthew 4 in the AS21
Matthew 4 in the BAGH
Matthew 4 in the BBPNG
Matthew 4 in the BBT1E
Matthew 4 in the BDS
Matthew 4 in the BEV
Matthew 4 in the BHAD
Matthew 4 in the BIB
Matthew 4 in the BLPT
Matthew 4 in the BNT
Matthew 4 in the BNTABOOT
Matthew 4 in the BNTLV
Matthew 4 in the BOATCB
Matthew 4 in the BOATCB2
Matthew 4 in the BOBCV
Matthew 4 in the BOCNT
Matthew 4 in the BOECS
Matthew 4 in the BOGWICC
Matthew 4 in the BOHCV
Matthew 4 in the BOHLNT
Matthew 4 in the BOHNTLTAL
Matthew 4 in the BOICB
Matthew 4 in the BOILNTAP
Matthew 4 in the BOITCV
Matthew 4 in the BOKCV
Matthew 4 in the BOKCV2
Matthew 4 in the BOKHWOG
Matthew 4 in the BOKSSV
Matthew 4 in the BOLCB
Matthew 4 in the BOLCB2
Matthew 4 in the BOMCV
Matthew 4 in the BONAV
Matthew 4 in the BONCB
Matthew 4 in the BONLT
Matthew 4 in the BONUT2
Matthew 4 in the BOPLNT
Matthew 4 in the BOSCB
Matthew 4 in the BOSNC
Matthew 4 in the BOTLNT
Matthew 4 in the BOVCB
Matthew 4 in the BOYCB
Matthew 4 in the BPBB
Matthew 4 in the BPH
Matthew 4 in the BSB
Matthew 4 in the CCB
Matthew 4 in the CUV
Matthew 4 in the CUVS
Matthew 4 in the DBT
Matthew 4 in the DGDNT
Matthew 4 in the DHNT
Matthew 4 in the DNT
Matthew 4 in the ELBE
Matthew 4 in the EMTV
Matthew 4 in the ESV
Matthew 4 in the FBV
Matthew 4 in the FEB
Matthew 4 in the GGMNT
Matthew 4 in the GNT
Matthew 4 in the HARY
Matthew 4 in the HNT
Matthew 4 in the IRVA
Matthew 4 in the IRVB
Matthew 4 in the IRVG
Matthew 4 in the IRVH
Matthew 4 in the IRVK
Matthew 4 in the IRVM
Matthew 4 in the IRVM2
Matthew 4 in the IRVO
Matthew 4 in the IRVP
Matthew 4 in the IRVT
Matthew 4 in the IRVT2
Matthew 4 in the IRVU
Matthew 4 in the ISVN
Matthew 4 in the JSNT
Matthew 4 in the KAPI
Matthew 4 in the KBT1ETNIK
Matthew 4 in the KBV
Matthew 4 in the KJV
Matthew 4 in the KNFD
Matthew 4 in the LBA
Matthew 4 in the LBLA
Matthew 4 in the LNT
Matthew 4 in the LSV
Matthew 4 in the MAAL
Matthew 4 in the MBV
Matthew 4 in the MBV2
Matthew 4 in the MHNT
Matthew 4 in the MKNFD
Matthew 4 in the MNG
Matthew 4 in the MNT
Matthew 4 in the MNT2
Matthew 4 in the MRS1T
Matthew 4 in the NAA
Matthew 4 in the NASB
Matthew 4 in the NBLA
Matthew 4 in the NBS
Matthew 4 in the NBVTP
Matthew 4 in the NET2
Matthew 4 in the NIV11
Matthew 4 in the NNT
Matthew 4 in the NNT2
Matthew 4 in the NNT3
Matthew 4 in the PDDPT
Matthew 4 in the PFNT
Matthew 4 in the RMNT
Matthew 4 in the SBIAS
Matthew 4 in the SBIBS
Matthew 4 in the SBIBS2
Matthew 4 in the SBICS
Matthew 4 in the SBIDS
Matthew 4 in the SBIGS
Matthew 4 in the SBIHS
Matthew 4 in the SBIIS
Matthew 4 in the SBIIS2
Matthew 4 in the SBIIS3
Matthew 4 in the SBIKS
Matthew 4 in the SBIKS2
Matthew 4 in the SBIMS
Matthew 4 in the SBIOS
Matthew 4 in the SBIPS
Matthew 4 in the SBISS
Matthew 4 in the SBITS
Matthew 4 in the SBITS2
Matthew 4 in the SBITS3
Matthew 4 in the SBITS4
Matthew 4 in the SBIUS
Matthew 4 in the SBIVS
Matthew 4 in the SBT
Matthew 4 in the SBT1E
Matthew 4 in the SCHL
Matthew 4 in the SNT
Matthew 4 in the SUSU
Matthew 4 in the SUSU2
Matthew 4 in the SYNO
Matthew 4 in the TBIAOTANT
Matthew 4 in the TBT1E
Matthew 4 in the TBT1E2
Matthew 4 in the TFTIP
Matthew 4 in the TFTU
Matthew 4 in the TGNTATF3T
Matthew 4 in the THAI
Matthew 4 in the TNFD
Matthew 4 in the TNT
Matthew 4 in the TNTIK
Matthew 4 in the TNTIL
Matthew 4 in the TNTIN
Matthew 4 in the TNTIP
Matthew 4 in the TNTIZ
Matthew 4 in the TOMA
Matthew 4 in the TTENT
Matthew 4 in the UBG
Matthew 4 in the UGV
Matthew 4 in the UGV2
Matthew 4 in the UGV3
Matthew 4 in the VBL
Matthew 4 in the VDCC
Matthew 4 in the YALU
Matthew 4 in the YAPE
Matthew 4 in the YBVTP
Matthew 4 in the ZBP