Philemon 1 (BOHCB)
1 Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu, 2 zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka. 3 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. 4 Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina, 5 domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka. 6 Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi. 7 Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka. 8 Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata, 9 duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu. 10 Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus, wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi. 11 Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni. 12 Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata. 13 Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara. 14 Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba. 15 Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani 16 ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji. 17 Saboda haka in ka ɗauke ni a kan ni abokin tarayya ne, sai ka marabce shi kamar yadda za ka marabce ni. 18 In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina. 19 Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi. 20 Ina fata, ɗan’uwa, zan sami amfani daga gare ka cikin Ubangiji; ka wartsake zuciyata cikin Kiristi. 21 Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce. 22 Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku. 23 Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka. 24 Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina. 25 Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku.
In Other Versions
Philemon 1 in the ANGEFD
Philemon 1 in the ANTPNG2D
Philemon 1 in the AS21
Philemon 1 in the BAGH
Philemon 1 in the BBPNG
Philemon 1 in the BBT1E
Philemon 1 in the BDS
Philemon 1 in the BEV
Philemon 1 in the BHAD
Philemon 1 in the BIB
Philemon 1 in the BLPT
Philemon 1 in the BNT
Philemon 1 in the BNTABOOT
Philemon 1 in the BNTLV
Philemon 1 in the BOATCB
Philemon 1 in the BOATCB2
Philemon 1 in the BOBCV
Philemon 1 in the BOCNT
Philemon 1 in the BOECS
Philemon 1 in the BOGWICC
Philemon 1 in the BOHCV
Philemon 1 in the BOHLNT
Philemon 1 in the BOHNTLTAL
Philemon 1 in the BOICB
Philemon 1 in the BOILNTAP
Philemon 1 in the BOITCV
Philemon 1 in the BOKCV
Philemon 1 in the BOKCV2
Philemon 1 in the BOKHWOG
Philemon 1 in the BOKSSV
Philemon 1 in the BOLCB
Philemon 1 in the BOLCB2
Philemon 1 in the BOMCV
Philemon 1 in the BONAV
Philemon 1 in the BONCB
Philemon 1 in the BONLT
Philemon 1 in the BONUT2
Philemon 1 in the BOPLNT
Philemon 1 in the BOSCB
Philemon 1 in the BOSNC
Philemon 1 in the BOTLNT
Philemon 1 in the BOVCB
Philemon 1 in the BOYCB
Philemon 1 in the BPBB
Philemon 1 in the BPH
Philemon 1 in the BSB
Philemon 1 in the CCB
Philemon 1 in the CUV
Philemon 1 in the CUVS
Philemon 1 in the DBT
Philemon 1 in the DGDNT
Philemon 1 in the DHNT
Philemon 1 in the DNT
Philemon 1 in the ELBE
Philemon 1 in the EMTV
Philemon 1 in the ESV
Philemon 1 in the FBV
Philemon 1 in the FEB
Philemon 1 in the GGMNT
Philemon 1 in the GNT
Philemon 1 in the HARY
Philemon 1 in the HNT
Philemon 1 in the IRVA
Philemon 1 in the IRVB
Philemon 1 in the IRVG
Philemon 1 in the IRVH
Philemon 1 in the IRVK
Philemon 1 in the IRVM
Philemon 1 in the IRVM2
Philemon 1 in the IRVO
Philemon 1 in the IRVP
Philemon 1 in the IRVT
Philemon 1 in the IRVT2
Philemon 1 in the IRVU
Philemon 1 in the ISVN
Philemon 1 in the JSNT
Philemon 1 in the KAPI
Philemon 1 in the KBT1ETNIK
Philemon 1 in the KBV
Philemon 1 in the KJV
Philemon 1 in the KNFD
Philemon 1 in the LBA
Philemon 1 in the LBLA
Philemon 1 in the LNT
Philemon 1 in the LSV
Philemon 1 in the MAAL
Philemon 1 in the MBV
Philemon 1 in the MBV2
Philemon 1 in the MHNT
Philemon 1 in the MKNFD
Philemon 1 in the MNG
Philemon 1 in the MNT
Philemon 1 in the MNT2
Philemon 1 in the MRS1T
Philemon 1 in the NAA
Philemon 1 in the NASB
Philemon 1 in the NBLA
Philemon 1 in the NBS
Philemon 1 in the NBVTP
Philemon 1 in the NET2
Philemon 1 in the NIV11
Philemon 1 in the NNT
Philemon 1 in the NNT2
Philemon 1 in the NNT3
Philemon 1 in the PDDPT
Philemon 1 in the PFNT
Philemon 1 in the RMNT
Philemon 1 in the SBIAS
Philemon 1 in the SBIBS
Philemon 1 in the SBIBS2
Philemon 1 in the SBICS
Philemon 1 in the SBIDS
Philemon 1 in the SBIGS
Philemon 1 in the SBIHS
Philemon 1 in the SBIIS
Philemon 1 in the SBIIS2
Philemon 1 in the SBIIS3
Philemon 1 in the SBIKS
Philemon 1 in the SBIKS2
Philemon 1 in the SBIMS
Philemon 1 in the SBIOS
Philemon 1 in the SBIPS
Philemon 1 in the SBISS
Philemon 1 in the SBITS
Philemon 1 in the SBITS2
Philemon 1 in the SBITS3
Philemon 1 in the SBITS4
Philemon 1 in the SBIUS
Philemon 1 in the SBIVS
Philemon 1 in the SBT
Philemon 1 in the SBT1E
Philemon 1 in the SCHL
Philemon 1 in the SNT
Philemon 1 in the SUSU
Philemon 1 in the SUSU2
Philemon 1 in the SYNO
Philemon 1 in the TBIAOTANT
Philemon 1 in the TBT1E
Philemon 1 in the TBT1E2
Philemon 1 in the TFTIP
Philemon 1 in the TFTU
Philemon 1 in the TGNTATF3T
Philemon 1 in the THAI
Philemon 1 in the TNFD
Philemon 1 in the TNT
Philemon 1 in the TNTIK
Philemon 1 in the TNTIL
Philemon 1 in the TNTIN
Philemon 1 in the TNTIP
Philemon 1 in the TNTIZ
Philemon 1 in the TOMA
Philemon 1 in the TTENT
Philemon 1 in the UBG
Philemon 1 in the UGV
Philemon 1 in the UGV2
Philemon 1 in the UGV3
Philemon 1 in the VBL
Philemon 1 in the VDCC
Philemon 1 in the YALU
Philemon 1 in the YAPE
Philemon 1 in the YBVTP
Philemon 1 in the ZBP