Revelation 14 (BOHCB)
1 Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu. 2 Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu. 3 Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya. 4 Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon. 5 Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne. 6 Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. 7 Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.” 8 Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.” 9 Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, 10 shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. 11 Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.” 12 Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu. 13 Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.”“I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu. 14 Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa. 15 Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.” 16 Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya. 17 Wani mala’ika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi. 18 Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin ’ya’yan inabin sun nuna.” 19 Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah. 20 Aka tattake su a wurin matsin inabi a bayan gari, jini kuwa ya yi ta gudana daga wurin matsin inabi tsayinsa ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300.
In Other Versions
Revelation 14 in the ANGEFD
Revelation 14 in the ANTPNG2D
Revelation 14 in the AS21
Revelation 14 in the BAGH
Revelation 14 in the BBPNG
Revelation 14 in the BBT1E
Revelation 14 in the BDS
Revelation 14 in the BEV
Revelation 14 in the BHAD
Revelation 14 in the BIB
Revelation 14 in the BLPT
Revelation 14 in the BNT
Revelation 14 in the BNTABOOT
Revelation 14 in the BNTLV
Revelation 14 in the BOATCB
Revelation 14 in the BOATCB2
Revelation 14 in the BOBCV
Revelation 14 in the BOCNT
Revelation 14 in the BOECS
Revelation 14 in the BOGWICC
Revelation 14 in the BOHCV
Revelation 14 in the BOHLNT
Revelation 14 in the BOHNTLTAL
Revelation 14 in the BOICB
Revelation 14 in the BOILNTAP
Revelation 14 in the BOITCV
Revelation 14 in the BOKCV
Revelation 14 in the BOKCV2
Revelation 14 in the BOKHWOG
Revelation 14 in the BOKSSV
Revelation 14 in the BOLCB
Revelation 14 in the BOLCB2
Revelation 14 in the BOMCV
Revelation 14 in the BONAV
Revelation 14 in the BONCB
Revelation 14 in the BONLT
Revelation 14 in the BONUT2
Revelation 14 in the BOPLNT
Revelation 14 in the BOSCB
Revelation 14 in the BOSNC
Revelation 14 in the BOTLNT
Revelation 14 in the BOVCB
Revelation 14 in the BOYCB
Revelation 14 in the BPBB
Revelation 14 in the BPH
Revelation 14 in the BSB
Revelation 14 in the CCB
Revelation 14 in the CUV
Revelation 14 in the CUVS
Revelation 14 in the DBT
Revelation 14 in the DGDNT
Revelation 14 in the DHNT
Revelation 14 in the DNT
Revelation 14 in the ELBE
Revelation 14 in the EMTV
Revelation 14 in the ESV
Revelation 14 in the FBV
Revelation 14 in the FEB
Revelation 14 in the GGMNT
Revelation 14 in the GNT
Revelation 14 in the HARY
Revelation 14 in the HNT
Revelation 14 in the IRVA
Revelation 14 in the IRVB
Revelation 14 in the IRVG
Revelation 14 in the IRVH
Revelation 14 in the IRVK
Revelation 14 in the IRVM
Revelation 14 in the IRVM2
Revelation 14 in the IRVO
Revelation 14 in the IRVP
Revelation 14 in the IRVT
Revelation 14 in the IRVT2
Revelation 14 in the IRVU
Revelation 14 in the ISVN
Revelation 14 in the JSNT
Revelation 14 in the KAPI
Revelation 14 in the KBT1ETNIK
Revelation 14 in the KBV
Revelation 14 in the KJV
Revelation 14 in the KNFD
Revelation 14 in the LBA
Revelation 14 in the LBLA
Revelation 14 in the LNT
Revelation 14 in the LSV
Revelation 14 in the MAAL
Revelation 14 in the MBV
Revelation 14 in the MBV2
Revelation 14 in the MHNT
Revelation 14 in the MKNFD
Revelation 14 in the MNG
Revelation 14 in the MNT
Revelation 14 in the MNT2
Revelation 14 in the MRS1T
Revelation 14 in the NAA
Revelation 14 in the NASB
Revelation 14 in the NBLA
Revelation 14 in the NBS
Revelation 14 in the NBVTP
Revelation 14 in the NET2
Revelation 14 in the NIV11
Revelation 14 in the NNT
Revelation 14 in the NNT2
Revelation 14 in the NNT3
Revelation 14 in the PDDPT
Revelation 14 in the PFNT
Revelation 14 in the RMNT
Revelation 14 in the SBIAS
Revelation 14 in the SBIBS
Revelation 14 in the SBIBS2
Revelation 14 in the SBICS
Revelation 14 in the SBIDS
Revelation 14 in the SBIGS
Revelation 14 in the SBIHS
Revelation 14 in the SBIIS
Revelation 14 in the SBIIS2
Revelation 14 in the SBIIS3
Revelation 14 in the SBIKS
Revelation 14 in the SBIKS2
Revelation 14 in the SBIMS
Revelation 14 in the SBIOS
Revelation 14 in the SBIPS
Revelation 14 in the SBISS
Revelation 14 in the SBITS
Revelation 14 in the SBITS2
Revelation 14 in the SBITS3
Revelation 14 in the SBITS4
Revelation 14 in the SBIUS
Revelation 14 in the SBIVS
Revelation 14 in the SBT
Revelation 14 in the SBT1E
Revelation 14 in the SCHL
Revelation 14 in the SNT
Revelation 14 in the SUSU
Revelation 14 in the SUSU2
Revelation 14 in the SYNO
Revelation 14 in the TBIAOTANT
Revelation 14 in the TBT1E
Revelation 14 in the TBT1E2
Revelation 14 in the TFTIP
Revelation 14 in the TFTU
Revelation 14 in the TGNTATF3T
Revelation 14 in the THAI
Revelation 14 in the TNFD
Revelation 14 in the TNT
Revelation 14 in the TNTIK
Revelation 14 in the TNTIL
Revelation 14 in the TNTIN
Revelation 14 in the TNTIP
Revelation 14 in the TNTIZ
Revelation 14 in the TOMA
Revelation 14 in the TTENT
Revelation 14 in the UBG
Revelation 14 in the UGV
Revelation 14 in the UGV2
Revelation 14 in the UGV3
Revelation 14 in the VBL
Revelation 14 in the VDCC
Revelation 14 in the YALU
Revelation 14 in the YAPE
Revelation 14 in the YBVTP
Revelation 14 in the ZBP