Romans 10 (BOHCB)

1 ’Yan’uwa, abin da zuciyata take so da kuma addu’ata ga Allah saboda Isra’ilawa shi ne su sami ceto. 2 Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba. 3 Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah. 4 Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya. 5 Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.” 6 Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa, “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’ ” (wato, don yă sauko da Kiristi), 7 “ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu). 8 Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela. 9 Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto. 10 Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka. 11 Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.” 12 Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi, 13 gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.” 14 To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba? 15 Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!” 16 Amma ba dukan Isra’ilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?” 17 Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi. 18 Amma ina tambaya, “Ba su ji ba ne? Tabbatacce sun ji.“Muryarsu ta tafi ko’ina a cikin duniya,kalmominsu kuma har iyakar duniya.” 19 Har wa yau, ina da tambaya. Shin, Isra’ila ba su fahimta ba ne? Da farko, Musa ya ce,“Zan sa ku yi kishin waɗanda ba al’umma ba;zan sa ku yi fushin al’ummar da ba ta da fahimta.” 20 Ishaya kuma ya fito gabagadi ya ce,“Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni;Na bayyana kaina ga waɗanda ba su ma taɓa neman sanina ba.” 21 Amma game da Isra’ila ya ce,“Dukan yini na miƙa hannuwanaga mutane marasa biyayya da masu taurinkai.”

In Other Versions

Romans 10 in the ANGEFD

Romans 10 in the ANTPNG2D

Romans 10 in the AS21

Romans 10 in the BAGH

Romans 10 in the BBPNG

Romans 10 in the BBT1E

Romans 10 in the BDS

Romans 10 in the BEV

Romans 10 in the BHAD

Romans 10 in the BIB

Romans 10 in the BLPT

Romans 10 in the BNT

Romans 10 in the BNTABOOT

Romans 10 in the BNTLV

Romans 10 in the BOATCB

Romans 10 in the BOATCB2

Romans 10 in the BOBCV

Romans 10 in the BOCNT

Romans 10 in the BOECS

Romans 10 in the BOGWICC

Romans 10 in the BOHCV

Romans 10 in the BOHLNT

Romans 10 in the BOHNTLTAL

Romans 10 in the BOICB

Romans 10 in the BOILNTAP

Romans 10 in the BOITCV

Romans 10 in the BOKCV

Romans 10 in the BOKCV2

Romans 10 in the BOKHWOG

Romans 10 in the BOKSSV

Romans 10 in the BOLCB

Romans 10 in the BOLCB2

Romans 10 in the BOMCV

Romans 10 in the BONAV

Romans 10 in the BONCB

Romans 10 in the BONLT

Romans 10 in the BONUT2

Romans 10 in the BOPLNT

Romans 10 in the BOSCB

Romans 10 in the BOSNC

Romans 10 in the BOTLNT

Romans 10 in the BOVCB

Romans 10 in the BOYCB

Romans 10 in the BPBB

Romans 10 in the BPH

Romans 10 in the BSB

Romans 10 in the CCB

Romans 10 in the CUV

Romans 10 in the CUVS

Romans 10 in the DBT

Romans 10 in the DGDNT

Romans 10 in the DHNT

Romans 10 in the DNT

Romans 10 in the ELBE

Romans 10 in the EMTV

Romans 10 in the ESV

Romans 10 in the FBV

Romans 10 in the FEB

Romans 10 in the GGMNT

Romans 10 in the GNT

Romans 10 in the HARY

Romans 10 in the HNT

Romans 10 in the IRVA

Romans 10 in the IRVB

Romans 10 in the IRVG

Romans 10 in the IRVH

Romans 10 in the IRVK

Romans 10 in the IRVM

Romans 10 in the IRVM2

Romans 10 in the IRVO

Romans 10 in the IRVP

Romans 10 in the IRVT

Romans 10 in the IRVT2

Romans 10 in the IRVU

Romans 10 in the ISVN

Romans 10 in the JSNT

Romans 10 in the KAPI

Romans 10 in the KBT1ETNIK

Romans 10 in the KBV

Romans 10 in the KJV

Romans 10 in the KNFD

Romans 10 in the LBA

Romans 10 in the LBLA

Romans 10 in the LNT

Romans 10 in the LSV

Romans 10 in the MAAL

Romans 10 in the MBV

Romans 10 in the MBV2

Romans 10 in the MHNT

Romans 10 in the MKNFD

Romans 10 in the MNG

Romans 10 in the MNT

Romans 10 in the MNT2

Romans 10 in the MRS1T

Romans 10 in the NAA

Romans 10 in the NASB

Romans 10 in the NBLA

Romans 10 in the NBS

Romans 10 in the NBVTP

Romans 10 in the NET2

Romans 10 in the NIV11

Romans 10 in the NNT

Romans 10 in the NNT2

Romans 10 in the NNT3

Romans 10 in the PDDPT

Romans 10 in the PFNT

Romans 10 in the RMNT

Romans 10 in the SBIAS

Romans 10 in the SBIBS

Romans 10 in the SBIBS2

Romans 10 in the SBICS

Romans 10 in the SBIDS

Romans 10 in the SBIGS

Romans 10 in the SBIHS

Romans 10 in the SBIIS

Romans 10 in the SBIIS2

Romans 10 in the SBIIS3

Romans 10 in the SBIKS

Romans 10 in the SBIKS2

Romans 10 in the SBIMS

Romans 10 in the SBIOS

Romans 10 in the SBIPS

Romans 10 in the SBISS

Romans 10 in the SBITS

Romans 10 in the SBITS2

Romans 10 in the SBITS3

Romans 10 in the SBITS4

Romans 10 in the SBIUS

Romans 10 in the SBIVS

Romans 10 in the SBT

Romans 10 in the SBT1E

Romans 10 in the SCHL

Romans 10 in the SNT

Romans 10 in the SUSU

Romans 10 in the SUSU2

Romans 10 in the SYNO

Romans 10 in the TBIAOTANT

Romans 10 in the TBT1E

Romans 10 in the TBT1E2

Romans 10 in the TFTIP

Romans 10 in the TFTU

Romans 10 in the TGNTATF3T

Romans 10 in the THAI

Romans 10 in the TNFD

Romans 10 in the TNT

Romans 10 in the TNTIK

Romans 10 in the TNTIL

Romans 10 in the TNTIN

Romans 10 in the TNTIP

Romans 10 in the TNTIZ

Romans 10 in the TOMA

Romans 10 in the TTENT

Romans 10 in the UBG

Romans 10 in the UGV

Romans 10 in the UGV2

Romans 10 in the UGV3

Romans 10 in the VBL

Romans 10 in the VDCC

Romans 10 in the YALU

Romans 10 in the YAPE

Romans 10 in the YBVTP

Romans 10 in the ZBP